Sunday, December 29, 2019

KASUWANCI NA

61-65

AsmaBaffa

      Page nakine Zainabsanusi78 Allah ya bar kauna.


    Godiya da jinjina me tarin yawa TASKAR SURAYYARHMS na gode da Sharhi kuna kokari, haka ake son gp.

        Bata zarce ko ina ba sai wani kungurmin kauye wanda mota bata shiga sai dai ka sauka ka hau machine a karasa da kai wata hanyar ma sai dai ka karasa a kafa,wata yar bukkar kara ce kamar ta Fulani, daga kofa Hajja ta tsaya tare da cewa Gafara dai Malam,yace Allah ee Mana Hajiya kece tafe yau? Hajja tace ae Wlh Malam ta furta tare da shiga dan karamin dakin,gefe ta zauna suka gaisa yana ta faman washe baki,tsoho gashi wani mugun kazami bakinsa duk goro yana yauki,hakora Yellow dasu shar in banda wari ba abinda yakeyi, farcensa zako zako kamar na kanti duk dirty a ciki,suma duguzum da wani lalatattun kayansa,yace Hajiya da Alama wata rigima ta taso ko,Hajja tace kwarai kuwa abinda ya kawoni kenan da waya zan maka Amma zuwa da kai yafi Sako, ko ina a dakin wasu litattafan ne na  sunayen taurari da Alama taurari yake bautawa dasu yake aikin shirkarsa.

    Hajja tace Malam kasan idan aiki babba ne bana bukatar a duba min,bana bukatar a hango min meke akwai dan kar ma naji wata matsala,kawai aiki na kawo cikin Uku ayi daya,wannan takadarin jikan nawa Aayan,kasan yayi aure to matarsa naga tafi karfina irinsa ce bata da kirki,nan take yace ba sai kin karasa ba na san komai, tace to aikin da nake so shine ko Ya saketa har abada kar ta dawo hannunsa,idan bai yuwu ba ya kara aure ta koma baiwa,idan bai yuwu ba ya tsaneta inda take kar ya raba ko ita ta tsaneshi da kanta,Malam ya dago yace me sauki kenan Amma bari muji abinda su zasu ce ayi wato aljanun da yake aiki dasu kenan,littafin taurarinsa ya bude da carbi sai wata kwalabar turare yayi shuru yana kallon littafin sai daí kaga bakinsa na motsi yana magana shi kadai yana to..to...ae...yawwa...ae...uhum...uhum..suna bashi Umarni kenan.

  Sai da ya gama sannan ya dago yace Hajiya baki taba kawo aiki me wahalar wannan ba,da farko dai sunce jikanki kullum cikin addua yake baza su iya shiga jikinsa ba ko sun shiga wahala zasu sha,na biyu kafin ma su shiga jikin nasa zasu kwashe shekaru suna fakonsa sai ranar da ya shagala da duniya sannan su shiga,ko sun shiga din dole fita zasuyi da kansu, aikin kuma bazai yuwu ba sai dole an shiga jikinsa,sannan ita yarinyar idan an Sa ta bar gidan Jikanku shi zai sha wahala ta dalilinta zai iya rasa ransa ita kanta yarinyar ba a zaune take ba kullum Azkhar take ba fashi,kuma kin san asiri ma yana tadda hali wannan taurin zuciya ce dasu gaba daya idan ma anyi suna da karfin zuciya,amma abu daya za ayi shine a hanasu kwanciyar hankali da zaman lfy idan kin yarda idan kuma kina ganin bai miki ba to fa a wannan lokaci sai daí kije wajen wasu duk rashin Imani na wannan yaron yasha kaina,dama kuma nasha fada miki,Hajja ta nisa tace ita yarinyar a batar da ita ko a haukatata mana gaba daya in yaso Shi ya kashe kansa dan ubansa,Malam yayi dariya yace Hajiya har yau kina nan da Halin nan naki na mugunta Amma kije zamuyi iya kokarinmu,ni kuma har India zan kira manyana dole ko ta yaya ne sai an miki abinda kika ce kina so,tunda kin yarda ko mutuwa ma jikan naki yayi baki da damuwa, Nan Hajja tace da dai yafi a dage sosai ta zube masa makudan kudi ta bar wajen,tayi waya da malamai da dama duk akan aikin sannan taje wajen wasu ma sunfi biyar Sabo da a hada karfi da karfe kuma sun bata tabbacin ba matsala.

     Makara mukayi don har rana ta fito bamu sani ba muna manne da juna muna bacci,lokacin Meenat har ta hada Breakfast da komai,Maeesha kuwa gyaran gidan ta fara kasancewar yau Ba schl,ni na fara bude ido na da kyar na iya zare jikina cikin nasa sabo da gaba daya ya makalkaleni ta ko ina ko juyi bazan iya ba,wannan ne ya tashe shi daga bacci,muna hada Ido na runtse ido, kawai sabo da kunya,Murmushi ya saki har ina jin sautinsa da sauri na sauka daga Bed din na shige hadaddiyar toilet dinsa nayi Brush da wanka kana na dauro Alwala na fito dan guntun Towel dinsa na daura na fito ina goge gashina,yana Saman Bed ya tsaya sai kallo na yake sannan ya mike shima ya shiga wanka,kafin ya fito na idar da Sallah na shafa Lotion dinsa tare da turarukansa har gashina na gyara shi sosai ina haka naji muryarsa yace kawo min Towel dina ko ki bude Wardrop ki miko min new, wai dan kar a bata kaya da yawa nayi Sauri na dauko Jallabiyarsa fara nasa dan tight short dinsa na Sa Jallabiya ba karamin kyau nayi ba duk da tayi min yawa kowa ya kalleni yasan nayi kyau.

   Toilet din na nufa na manta kawai na murda Handle na shige gaba daya da Sauri ya juya min baya yana ta masifa ban kalleshi ko daya ba na fito da gudu nace kayi hakuri mantawa nayi wlh na kara dan tura kofar na dan tura hannu na tare da  mika masa ya karba ya zuba su a washing machine sannan yace miko min wasu ki bude part din karshe,da Sauri na bude na dauko tare da kara miko masa ya amsa ya daura sannan ya fito ina dariya nace na gani dai abin tsoro ma, murmushi yayi yace ke kika sani kuma,Wajensa na karasa kawo na tayaka Allah na iya ni nake shirya su Meenat ma fa, na zuba Lotion a hannuna nace to juyo mana ni ko dama wayo zan masa dan na taba masa jiki ne Sabo da yana birgeni,shafa to kiyi kuma Sauri sallah zanyi na fara murza masa Lotion ina ta murmushi dan fatarsa sai laushi kawai,nazo waist dinsa na tsokaneshi Sabo da naga baya so a kalle masa tsaraici nace kwance towel din nayi Sauri mana dariya yayi yace a'a ki kwance da kanki kai.

   Ina gamawa yace saura kaya to ya dauko wani Yadi shara shara fari me shegen kyau karamin dinki fitted na Maza yan gayu,da Singlet sai short ya miko min karasa aikinki, na karba kuwa ya dauka zan wani kasa sai ya karbe yasa Boxers dinsa,nasa masa singlet yasa wandon kayan na Sa masa rigar, da Sauri ya gyara sumarsa tare da fesa turaruka ya tayar da Sallah,ni kuma na fita tare da sauka kasa na duba na ga me su Meenat suka dafa idan basuyi ba nayi,tea suka sha da Doya da kwai kawai,sai farfesun kaji,na dinga masifa kun san dai bazan fito da wuri ba dan Iskanci sai kuyi wani Doya kawai da tea mijina yana ci ne? Ba sosai yake ci ba,Meenat tace au bamu birgeki ba a hakan? Ke da kika ce hira zaki je kuyi kawai ki dawo sai yanzu zaki fito duk hirar ce tun jiya? Shike nan bacci bazai kwasheni ba nama kwana din ina ruwanki ke zaki tsara min abinda ya dace nayi kece gaba dani ko nice gaba dake? Daga yau ma acan zan dinga kwana sai me kuma? Dariya Meenat tayi kawai tace ah mun gane, to gyaran gidan fa? Ya kika gani ya miki ko shima mijinki bazai masa kyau ba? Dubawa nayi nace wannan ai nasan kun iya dama kuma na gani kunyi kokari,bari to zo ki tayani muyi masa Kunun Gyada,da su muka shiga kitchen din suka taimaka min Dan danan muka shirya lafiyayyen kunun gyada,na fara soya dankali suka ce sun gaji su nace to kuje ku huta,suna fita sai ga Aayan ya shugo kitchen din a bayana ya tsaya kamar zai shige jikina ina jin kamshinsa a saitin kunne na yayi magana a hankali yunwa nake ji fa ki danyi Sauri,yana fadan haka ya fita ya barni nan ina jin jikina wani iri.

    Tunowa nayi da zan fara yanga ta na daina cin abinci a gabansa da yawa Sabo da kar ya rainani gashi kuma bana koshi da wuri sai na shirya dabarata yanzu duk girki sai na samu na zuba a kitchen din in ci abina na koshi sai na rage space kadan idan anzo ci a dining sai aga ina ta yanga naki cin abincin da yawa sai dai na dan ci kadan,
    Cikin rashin Sa'a yau nace zan fara tunda tare zamu ci a dining,na zauna na ebi chips din na zuba kunun gyada ta,farfesun kajin dasu Meenat sukayi nan ma na zuba Naja gefe ina cin abina a nutse,Kawai Aayan yazo zai shigo kitchen yaganni kicif ina cin abina,nan take ya gane me zanyi don Allah ya zuba masa basirar gane abu,dariyace ta kamashi me karfi ya danneta,ya juya palo dan kar na ganshi naji kunya.
   Saida na koshi sannan na sha ruwa na gyara lips dina na fito na shirya Dining na gyara kitchen din na fito,Aayan yana Dining yana jirana nazo na zuba masa ni kuma na zuba komai dan kadan kamar dan yaro ne zaici irin yar gayun nan, yaga ina ta wani juya cokali a ciki ina tsakura,shiko yana ta cin abinsa har farfesun,ya kalleni yace kici mana wannan dan abincin nufinki zaki ci? So kike ace bana baki abinci ko so kike ki rame? Baki na tabe ina yatsina fuska na ce ya isheni haka,ya kalleni tare da danne dariyarsa yace me yasa kika daina cin abinci ko baki da lfy? Na shagwabe fuska nace ni...yanzu bana son wani ciye ciye da yawa,yace to kiyi hakuri kici kinji yanda ya zage yana ta lallabani sai naci abinci ni kuma ina botsewa haba sai naji wani dadi nace lallai Aayan ya fara sona sosai ji yanda yake ta kula dani yana damuwa sai naci abinci,ni kuwa sai yanga nake wai ni a dole na masa wayo ban san shike min wayon ba.
  
   Kusa dani ya dawo yace Dole sai ya bani da kansa nafi ci na koshi yaga wasa nake da cikina so nake cuta ta kamani,nan take na Tsorata Sabo da na koshi taf cikina ya cika,ina ji ina gani ya zauna ya dinga dura min abinci da kansa,kamar zanyi amai Amma yaki saurara min,Dankali da Kunun gyada ya dinga danna min,ya dawo kan farfesu,tun ina dannewa nace dan Allah na koshi Amma dama Sabo da mugunta ya shirya min yace sai na cinye ya san ina da ci,Idona ya kawo Hawaye na fara kuka ina bashi hakuri Amma yaki yarda sai cusa min yake,sai da naci me uban yawa wanda kwakwaran motsi nayi sai nayi Amai,ya miko min yatsun Sa da ya bani farfesu dasu yace tsotse abinki,haka na tsotse yatsun tas shi kuma yanda nake tsotsar yatsun ne ya tayar masa da hankali nan take ya birkice,Sha'awarsa ta motsa da kyar ya dan danne yace ku shirya da yamma zamu fita zan dawo na daukeku,hararsa nayi nace to ina turo baki akan dura da yayi min.

    Ameer dasu Mujaheed ne zaune a katafaren Palonsu suna game suna hira,Mujaheed yace ni fa guys wlh ina son beb din nan kanwar matar Aayan Meenat take ko wa? Khaleel yace ai yarinyar tayi ne  ina fada ma gaba dayansu Allah ya zuba baiwa Barin ma matar Aayan gaskiya Ameer Banga laifinka ba,Ameer yayi dariya irin ta yan duniya sannan yace baza ma ku gane ba sai nan gaba,ni na hango abinda na hango,kullum da ita nake kwana nake tashi,Sajeeda dake gefensu taji haushi dan ita Ameer take so yanzu, rai bace tace haba Ya Ameer mene haka wannan cin fuska ne ina wajen fa wlh zan fadawa Abbi kasan dai yace Aure zai mana,Ameer ya kalleta shekeke ke dalla rufe min baki me zaki kaimin gidan nawa? Har daki kike bina muna aikata abubuwa zaki zo kice wani na aureki,Amma kasan dai ai kaine kace ba komai zaka aureni tunda kaine ka lalata ni,Mujaheed yace ko kunya bakwa ji ku rufe mana baki Hajja in ta dawo ku fada mata mana a fasa can da matsalarku,Cousins kenan dama haka akeyi ko mai ace cousin dina ne Kaza Kaza kullum kayi tunanin yan uwan ashe ana nan ana aikata masha'a tare,Mata har gidan kani ko wan babansu zaka ga sun tafi hutu an samu Cousin mace ko namiji ana ta shekewa,su kuma iyaye tunaninsu zumunci akeyi sai suyi ta jin dadi Allah kyauta.

    Hajja ce sanye da glass dinta na ido ta zauna a Cikin jikokinta nan Fa Sajeeda tana kuka tace Hajja kinji wai Ameer bazai aureni ba, Hajja ta gyara zama fatarta duk tayi yaushi tace shi din banza,ya Isa ma,shi waye shi wlh wlh Allah daya sai anyi wannan aure kwanan nan ma kuwa ko sama da kasa zata hade,waye kai? Ka Isa nayi magana nasa doka da hukunci ka tsallake ko Ubanka Mustapha bai Isa ba bare kai karamin shege,nan Hajja tayi masa tatas yayi shuru yana ji Amma ya rantse indai Sajeeda ta shiga gidansa sai ya kusa hallakata da muguntarsa ita kuwa Sajeeda murna takeyi don tun da ta taso a duniya take son Ameer sosai Sabo da ya hadu shima ba laifi.

     5:30 muka gama shirinmu tsaf mun hadu karshe yau kamar wata Sallah haka muka dau wanka,Aayan kuwa bamu san a inda ya shirya ba haka muka ganshi ya shigo cikin dakakkiyar shadda sea blue yanda yayi kyau ya zarta hankali ma,Maeesha ya kalla yana zuba kamshi yace kinfi kowa kyau yau,nan take naji haushi ni bai yabeni ba ai ni ya dace yace nayi kyau ba su ba,Meenat kuwa yace Yau kamar Queen haka kika koma nan take Meenat ta fara dariya tana tnx Yaya,Ma'eesha kuwa ta makale a jikinsa,ni da yau nafi kowa haduwa yanda nayi kyau har ya wuce misali Amma bai ce nayi kyau ba sai su Meenat,kasa danne fushina nayi sai kumbura nakeyi haka na karasa Sa sarka ta na dauki mayafi na da jaka nace muje Meenat da Ma'eesha suka yi waje ni kuma zan fito yana Bedroom din namu ya jawo hannuna na fisge abina,ya kara jawoni na fado jikinsa gaba daya,na sadda kaina kasa a saitin kirjinsa,hannaye biyu yasa ya dago da fuskata yana kallon lips dina tare da cewa wa kika sawa jambaki kuma? Nace masu sona na cikin gari idan mun fita nake Sa ran zasu kalla suji dadi, bakin ciki ne ya ziyarce shi me tsanani Amma sai ya danne ya hade bakina da nashi ya dinga sha,sai da ya shanye jambakin tas sannan ya dauki wipes a saman mudubi na dinga tsalle ina son guduwa amma ya rikeni tam da kansa ya goge min fuska tas ba abinda ya bari na kwalliya ta,hakan ma yaga baiyi ba sai ya jani toilet fuska ba walwala ya danna kaina a saman sink yasa soap ya wanke min fuskar tas ya goge min da towel nayi wani mugun Fresh jajayan lips dina suka fito natural sai na kara wani kyau kowa yasan Natural kyau na gaske nayi,ga kayan sun hau jikina,dankwalin dana kafa kamar gogoro ya zame ya jefa shi saman Bed ya dauki Hijab ya sa min duk da haka nayi kyau sosai sai ya cire Hijab din ma tare da cewa baki da kyau sam sam Bazan iya fita dake ba bari muje da kyawawana su Meenat,dama haushinshi nakeji ya bata min kwalliya kuma baice ina da kyau ba yanzu kuma wai ya fasa zuwa dani,ban san sanda na fashe da kuka ba me karfi, ba shiri yace taso taso mene haka wannan uban kuka zaki fasa min kunne,gyalena na dauka ina share Hawaye yace Sa Hijab na kara sakin kuka yace to yafa gyalen haka muje wannan masifa haka,ina dariya na yafa haka nabi bayansa,sai da na kara tsayawa a bayansa na zaro Powder a jakata muna tafiya bai San ina ta shafawa ba,na gama nasa jambakina red,kafin mu karasa mota har na gyara ribbom din gashina nayi acuci sosai na gyara mayafin aiko na dau kyau kowa ya ganni yaga yar gayu,nasa glass dina dan Brown nayi kyau ba a magana,yana juyowa sai da ya firgita kamar aljana kafin aje mota har na sake kwalliya yace zanyi maganinki a ransa tunda bakya jin magana dai dai  nake dake.

     Gaba na shiga Meenat da Ma'eesha suna baya  shike Driving yau,katafaren store muka tsaya Meenat sai jin dadi muke muma mun Zama yan gayu,sabo da neman suna sai da na karasa tare da rike Hannunsa muka jera sabo da naga Yan mata sai shige da fice suke a wajen ko wacce ta Sha wanka, hannuna ya rike yana murzasu muna tafiya duk inda muka keta sai an kallemu,Kayan sawa iri iri yace mu zaba,dana tashi sabo da tausayin kudi abinka da ba a saba ba kawai sai na zabo atamfofi dasu laces materials dasu Ready made duk ba na sama da Dubu biyar daka biyar sai kasa,gani nake na gama kure karyar kudi, yana duba kudin yace a maida su wannan ai wanke kudinka ne Hajiya,da kansa ya dinga jidar mana kaya masu matukar tsadar gaske komai latest,haka takalma  ma,bags ma ba a magana,har su cosmetics yana zabo me tsada muma muna daukan wanda muke so,har jewelries, muka je bangaren Inner wears yace su Meenat su zabi nasu aiko suka jida masu kyau iri iri,ya jani wani bangaren can daban na inner wears yace zabi size naki naga ko Bra kuwa kina sawa? kullum daga an dage miki riga direct ake tafiya can,Kunya naji na rufe ido nace Ina sawa mana amma a boye nake sawa na wanke a boye bana so ace kamata ina sa Bra,to mene a ciki dan kinsa yaja tsaki tare da cewa anya kuwa jinin birni ce ke? Nace a'a daga garinku nazo murmushi ya saki sannan yace mu bamu da dangi a Rimin Gado mu gaba da baya dan birni ne ni,muna ta Zaba iri iri masu kyau ya dauko min wata yar karama yace ga wata me kyau,Hararar wasa na masa nace kaima kasan sunfi haka wuce nan sai kace yarinya,muna dariya sai ga wata yar gayu tana kwas kwas da takalmi ga kamshi tana zubawa muryarta muka ji tace Aayan  kaine a nan we finally meet here ohh,Dagowa yayi tare da zuba mata idonsa me matukar kyau ya danyi murmushi kadan sannan yace Sameera kece How u?longest time,tace am great ina ta so mu hadu wlh amma ba dama tun aurenka na farko fa gaskiya mun dade.

     Wani kishi da bacin rai ya taso min na bata rai nayi kicin kicin na tashi hankalina gaba daya ina Harare harare,itace second wife din naka? Ina Yarima yana dariya yace yana lfy yar duniya kin buya amma dai kin sake aure yanzu ko? a'a aure ai sai na huta ina aiki ina samun kudina matsalar maza ta isheni baku da kirki Sam ni sai na huta zan yi Insha'allah,Jin bata da aure yasa na kara fusata na daure fuska na dawo gaban Aayan na juya bayana tare da kwantar da jikina a jikinsa muna facing juna da Sameera sai kallon Banza nake mata,Hannunsa na jawo guda biyun na sakalosu ta kafaduna ina wasa da yatsunsa,Murmushi Sameera tayi tare da cewa am sorry to say Aayan kasan bana boye abinda ke raina amma wannan tayi maka yarinya da yawa Aayan kamarka da auren kamar wannan da gani ma baza ta wuce 15yrs ba,ga mata a gari zunduma zunduma da ka fada mana ai da mun zabo maka manyan yara amma irin wannan ai kuruciya zaka sha baza kaji dadinsu ba.

   Dariya sukayi gaba daya tare da wani tafawa abinda ya bani haushi kenan ya kara kuleni mene nasa na tafawa da mace,nan take naga fa ta fada min baka zata barni da takaici  ban san sanda nace uhm Allah sarki kuma a hakan bashi da kamata dan ina masa abinda Babba bata isa tayi masa ba,tunda tsab nake daukeshi wanda nasan ko uwarki yafi karfin.....kafin na karasa yasa tafin hannunsa ya rufe min baki da karfi dan yasan sai na karasa ko za a mutu sai na rama,ina so na kwace baki na amma yaki Sakina ya toshe min da tafin hannunsa yana fada min a kunne kina magana wlh yau na lahira sai ya fiki jin dadi bakya jin magana ko ke ba a isa an miki abu kin hakura ba sai kice sai kin rama wannan wacce magana ce ta marasa kunya uwarta fa kika ce,Sameera ta kalleni sosai tace da Sameera kike zance yarinya zaki san kin zagi uwata,wlh sai kin San wa kika cewa haka,Allah ya taimakeki yanzu Kinci darajar Mijinki amma a sannu zan goge miki abinda ke kanki,Bakina na kwace nace Ba Sameera ba Allah yasa kece Sameeran Gaya🤣 wlh nafi karfinki kina magana kina cijewa ke ga yar daba karewar Daba munga Amana ta Alim ma😍 Sameera dama irin Masu takama da yan daba ne har yara ne da ita yan daba,bata da kunya duk abinda taga dama haka zata fadawa mutum shi yasa ko zaman aure bata iya yi,sabo da ko yaushe a shirin daba take kana mata zata sa yara yan daba suyi ma kaca kaca tana takama da kudi sabo da ubanta ita kadai ya haifa ya rasu ya bar mata dukiya me tarin yawa,Tun kafin ya mutu ya raba gado yaba yan uwansa ya barwa yarsa komai,shi yasa take abinda taga dama,kuma bata San mutunci ba duk inda take da kai zata iya ci ma mutunci ta ko wanne hanya,Aayan kuwa Business ne ya hadasu tsakanin Company nata da nasa tun da dadewa.

    Ni kuwa nace komai dabancinki baza ki bude min ido ba kiyi duk abinda zakiyi nima baki San ko ni wace ba shi yasa har kike magana dani haka ina kyaleki,ki Bari watarana Business ya hadamu anan zaki gane true color dina,Tsaki taja ta bar wajen a fusace,Aayan yana ta kallon yanda nake tsiwa yar ficika dani gaban sangamemiya irin Sameera ko tsoro bana ji,na kalleshi nace girma ya fadi wlh ka ba dani ina ma kallon Ustaz har wani hannu kake hadawa da yan tasha,da gani wannan yar tasha ce gaka da fyallelliyar budurwa me zaka ji a hannun wannan me suffar mazan, kayi dacen mata amma baka godewa Allah kana wani rikewa wata hannu bayan ga hannun da zaka samu lada Allah kyauta ka daina irin wannan a gabana dan wlh ni bazan dauki a wulakantani ba dan baka darajani ba Sam,ka zubar min da mutunci ace Namiji yana da kamata yana rike hannun wata banza,wannan babban matsalace dole na tuntubi kaina Ashe ma ban kai mace ba.

    Yana jina ina ta masifa kamar uwarsa yana dariya a ransa,yace to yi hakuri masifaffiya tunda bakya so na daina,wai nice budurwa shi baya daukana a budurwa Sam,yace wai ke nan budurwa ce? Bacin rai ya kamani sai na danne a fili  nace a'a kwaila ce,a na dinga masa masifa ina zan rama zaka San ba budurwa bace ni daga yau na Canja salo again na fasa wannan Business din da mukace za muyi wani zanyi daban sai na sa kayi nadama har ni za a wulakanta dan anga ina biyayya ina cusa kaina ina kokari naga an zauna lfy shike nan za a gani,dariya yayi yace a'a dan Allah tsokanarki nakeyi fa muyi Business dinmu zan biya kudin,nace anki din sai na rama nima.

    Mun gama siyayyar komai yasa aka kai boot din mota ya biya muka fito kenan sai ga Ameer da Khaleel tare da wasu yan mata masu suffar karuwai sai chewgum suke taunawa su a dole manyan yara,na kalli Aayan na bata rai nace kalli Meenat a gabanmu tsaya kaga abinda sukeyi kalli,ya kuwa kalla sosai ni kuwa wai dan kar ya kalli yan mata nayi masa wayo,Muna zuwa Ameer sai kallona yakeyi zasu shiga mu kuma zamu fito na bi ta tsakiyar yan matan nan a hankali yanda zasu ji nace yan iska sun dauko yan iska su a dole yan mata ana yaye baki a titi na wuce fit na koma kusa da Aayan,Khaleel ya fusata kwarai da maganata haka yan matan ma,Ameer kuwa so yasa baya ganin laifina sai dai ma birgeshi da nakeyi aransa ma cewa yayi wannan gaskiya kika fada Mufeedata tabbas yan iska ne suka dauko yan iska Allah ya baki basira tare da saurin ganewa🤣

    Yan matan zasu zageni Ameer yace wlh duk wacce ta fadi ko bakar magana a kaina sai ya mata illa har fada suka so yi da Khaleel..
   Muna shiga mota na tuna zanyi girki kuma kayan miyarmu ya kare nace Aayan kayan miya na manta,Yace to mu koma store din nace a'a danyi gaba wajen yar kasuwar can zamu samu.
    Muna zuwa yayi parking nace sai ya fito munje tare,yace a'a nifa ban taba siyan abu a kasuwa ko gefen hanya ba a store nake siya,Na fara rokonsa dole haka ya fito muka karasa wajensu,sabo da tattalina da son kudi nace Malam kwano nawa nawa? Aayan yace nidai a zuba kawai mu tafi,nace a'a so kake ayi mana tsada bazai yuwu ba yo ni akan barkono kwano daya idan nazo sarowa Basai na yini a wajen ba ana ciniki ba kuma karshe kaga na siya arahar banza,Dariya Aayan yayi yace yini guda fa? Nace Cass ma kuwa, Agogon Dubu biyu ina siyoshi a Dari biyu da hamsim ni highest Dari biyar zan siyi shege,ka dinga zuwa dani siyayya kaga araha,Aayan kallona kawai yake yana dariya,Nace kai me kayan miya kwanon tattasan ne dari biyar a garin gaba gaba muke da zan siya haka,yace gaskiyar magana Dari hudu da hamsim baya tsada bana nawa kike so a siyar miki,Nace to ka rage,nafa San kan kasuwar nan,Aayan yace Haba Ke kuwa har kwano guda Dari hudu da hamsim kacal a kasa siya mene na tsada a nan? Harara na watsa masa tare da dan zungurinsa nayi masa magana a hankali bana son haka ba a yiwa yan kasuwa haka,zaka kashe min ciniki idan kasan haka zaka min ka koma mota yanzu duk ragi ai ragi ne,Aayan yace Malam zuba mana kwano biyar ga kudin ya zaro kudi ya mika,na fara rigima na cumimiye a jikinsa baza a biya ba kwano har Dari biyar gwara Ku tafi gida ni Ku barni a nan nayi cinikin ko Dari hudu na siya sai na samu Dari Dari ta Zama tawa,na dawo a taxi, ko kulani baiyi ba yace to tumatir fa,nace a tsaya ni zan Zaba da kaina,me kayan miya yana ta dariya yace kudi kudi ne ga gwalagwaje wanda ya gama lugwiguwicewa daf yake da rubewa kudinsa daban,ga masu kyau manya da kanana,nayi layin  marar kyau gwalagwajen nace duk tumatir tumatir ne tunda dafashi za ayi mu sharbe miya Malam ga me sauki ba sai anyi asarar kudin ba a bamu wannan,Aayan dariya ta kamashi ta gaske ya dinga yi yace wlh baki isa ba gwara da Allah ya kawoni na gani dama abinda kike sawa muna ci kenan? Nace to sau nawa ka shanye miyar sa kana Santi ai ni in kaga lafiyayyan tumatir a fridge to na cin salat ne,ai ko harda kwalla Aayan yake dariya ni kuwa ko a jikina,yace Allah na gode ma da na gani da Ido na shi yasa Ashe ba kya yarda a bawa kowa yayi cefane sai ke Ashe Guba kike bamu muna ci.

    Aayan yace Malam me kyau wanda yafi kowanne tsada zaka zuba, na hangame baki ina jimami shike nan za a ci kudinmu a banza,akan dan tumatir har yan Dubu Dubu na fitowa naji kamar na fisge kudin,na bata rai ina ta fushi nace ai gwara ni ka bani na dinga tara ma kudin watarana sai mu dakko a siyi abu me amfani dasu amma wlh wannan Almubazzaranci ne, mukaje layin Albasa nan ma dan yaga yanda zanyi yace zabi da hannunki one by one ki dinga zubawa a ledar mu gani,me Albasa yace ai kwano kwano muke saida wa,Aayan yace bari ta Zaba sai a auna zan biya ko nawa ne,aiko na fara Zaba sai na duba wacce ta tsage ko ta kusa lalacewa ko marar kyau sai na dauka na nunawa me kayan miya nace kaga dai wannan araha zata yi ehe,wannan ma ba me tsada bace,Aayan yana murmushi yace pick the nice one mana,na kai hannuna kan me kyau sai na koma na faki idonsa na jefa marar kyan a leda yana kallona yana dariya har na gama sannan yace to Malam juye wacce ta bari bata Zaba ba su zamu siya,haka aka auna ina gani kamar na fashe sabo da ni kudin da aka kashe kawai nake jin haushi da an tattala su ai sai a moresu watarana Rayuwar Manage na iya a haka na taso da ita na saba.

   Na dauko shima ya dauki wasu muka zuba a mota ina ta harararsa yana kallona ta gefen Ido yace daga yau tsinke baza ki kara siyowa da kanki ba da kaina zan siyo ko na bayar a siyo,nace girkin ma ba sai kayi abinka ba,wlh ya kamata ka koyi adani sabo da rayuwa ni gaskiya nake fada ma.Maeesha dama suna gani sun San halina sun San yanda nakeyi a kasuwa dariya suma sukeyi Meenat tace Yaya Aayan ya kaga mutuniyar taka ta iya Zabe ko?

   Dama kadan yake jira ya dinga dariya yace ai naga Zahiri yau Meenat,haka takeyi ko a gida Ammah ta dinga ta mata fada amma baza ta ji ba cewar Ma'eesha.
   Meenat tace ai baka San abin haushi bama shi yasa bama Rakata kasuwa watarana akan egusi da zamu siya wlh sai da muka yini a table din me egusi har fada sukayi ya koremu gaba daya,kai ai kadan ka sani, turmi ma ba a cin arziki a gidanmu ko daka wasu sukayi a ciki sai ka biya ashirin, haka gugan Rijiya ma ko kurar Ciro guga duk na haya ne hhhhh Aayan ya dinga dariya Meenat suna ta bashi labari suna min dariya,sai da na saki Kuka sannan sukayi shuru.
    Haka ma Ya Aayan watarana ta siyo min jakar makaranta me kyau ina ta murna wata kawarta Nawwara tace gaskiya jakar tayi kyau nima zan siyo aiko Mufee na jin haka tace Dari uku na siyo ta bani Uku da hamsim na siyar miki,ina kuka haka ta siyar da jakar nan taci ribar Hamsim,Aayan yana driving yana dariya.

     Malamin Hajja ya hado mata muggunan da za a sa min tare da Aayan a abinci,da sauran wasu iri iri na wajen Malamai shi yasa yanzu ta saka rigima wai Daddy ya fadawa Aayan a dawo damu ai muma jikokinta ne taga abinda tayi bai dace ba bata kyauta ba
   Daddy yasan ba gaskiya bane amma yasan Allah na nan ba matsala ya Sanarwa Aayan.









AsmaBaffa
[1/16, 5:51 PM] Asmabaffa: 🌖🌖🌖🌖
🌖🌖🌖🌖

     KASUWANCI NA







            66-70

By
AsmaBaffa


                JANNAT wannan page naki ne.


    Godiya gareku House of Hausa Noveld kun iya Sharhi.

 Bayan yayi parking a cikin gidan fitowa mukayi tare da jidar kayan muna kaiwa muna dawowa har muka kwashe komai ya rufe motar  take away na abinci da ya siya mana na karba ina ta masa godiya da addua ya wuce abinsa nima na shiga Bedroom dinmu, Bayan munci mun koshi wanka nayi na shirya cikin sabuwar Nighty dina iya cinya me siririn hannu peach color na fito fes ina kamshi Meent ce ta shigo Sis kije inji Ya Aayan amma fa yana compound jikin motarsa da alama fita zaiyi,Hijab nasa har kasa kamar zai ja kasa na fita lokacin tuni munyi sallar Isha,saman Motar na ganshi a zaune cikin kana nan kaya ba karamin kyau yayi ba,wani abu ya tsirga min na tsinci kaina cikin wani yanayi na shauki wanda bazai misaltu ba wani dadi yana ratsani, kallona yake cike da tsantsan nishadi kwance a fuskarsa zuciyarsa cike take da farin ciki wani Sanyi na ratsashi.

     Ina murmushi na karasa tare da cewa au akace fita zakayi kuma naga ka zauna saman bayan mota,yana murmushi yace zance fa nazo kinyi sabon saurayi kuma kina wani cewa fita dariya nayi nace kaima dai baka rabo da tsokana a haka zubin mugaye gareka, am serious ni fa zance nazo dama gori kike min kece kullum kike zuwa zance,Dariya nayi nace to nan gaba idan zaka zo ka dinga bugo waya sabo da ai banyi kwalliyar zuwa wajen saurayi ba na fada kamar gaske, muryarsa naji yace duk fa cikin business ne ki daina tunanin da gaske ne kudi za a biya ki wannan fitowar ma da kikayi kin ci kudade masu yawa,dadi ya kamani nace an gama ko kalma daya ce duk kudi ne? Yace of course, murmushi nayi tare da gyara tsaiwata yana sama na matsa jikin kafafunsa, yace yan mata suna na Aayan duk da cewa baki tambaya ba,ban san lokacin dana fara dariya ba ni abin ma kunya ya bani amma na daure nace ai yanzu gashi ka fada, yaci gaba da tunda na ganki kika shiga raina naji bazan iya bari ki wuce ba batare da na miko Kokon Barata ba gareki, uhmm nace tare da tunani sannan nace kasan me ni ban iya so farar daya ba dole sai mun zauna da mutum idan naga halayensa sun min sai na yarda amma yanzu bazan amince ba, sama naji yayi dani ya daudarani saman motar nima kusa dashi jikinmu na gugan juna,baki na bude tare da cewa wannan saurayine ko dan Shan minti ne kawai,dariya yayi ai an daura mana aure da Budurwar kawai bata sona ne shine nake zuwa zance sabo da na lallabata.
   Murmushi nayi nace to naji game din tayi kyau back to our business nawa na samu? Yace ai Dari biyar kika samu sabo da kin kasa magana baki fadi kalamai masu sanyi ba taya zaki samu kudi.

   Masu Zafi zan fada yanzu ma kuwa na irin fuske ba wasa nace look in to my eye aiko ya kalla da mayun idonsa I was kidding u  but u I knew I love u,i wish I can show u how much I love u,i care for u,my heart is full wth ur love my Prince, yana murmushi yace proof what u have just said, nan take da gaske nakeyin kalamai na ni, bana karya bane amma a boye a raina nace na samu Damar jin dadi na sai na fake da kudin,a fili kuwa sai na ce ka tabbata  zan samu kudin nan da yawa,kai ya daga min tare da kara matsowa jikina sosai yatsunsa ya sarke da nawa tare da jawo ni jikinsa, hannayena na sakalo ta wuyansa a hankali na rungumeshi a jikina sannan na dago kaina tare da shigar da bakina cikin nasa ya fara tsotsa kamar ba gobe, tunawa nayi ko yan aiki na zirga zirga a wurin nace yan aiki fa?yace ai basa kwana a nan gidan da safe suke zuwa nemi kudinki na Business yarinya,dariya nayi a raina nace Ina ta masa wayo ya kasa ganewa,nace ni dai mu koma bedroom,lallai kudi zaki nemo da yawa karfa ki karar min da dukiyata,ina dariya nace hau dani baya wannan ni zan baka kudin cikin nawa ka cire Dubu guda,baki isa ba sai dai na daukeki,nace ni dai baya nake son hawa,ko baka da karfi ne? Hannu yasa ya daga ni sama sosai kamar ya dauki tsinke ya dauri a kafadarsa naga ya mai Dani bayansa kamar yar jaririya,nace kai karfinka yayi yawa amma a haka dan Lange Lange da kai, murmushi yake har bedroom dinsa karki cire Hijab din, why? Zaki gani ya furta yana dorani saman bed sannan yazo ya daga hijab din tare da shigewa ciki,dariya nayi yanda yake min abubuwa a ciki don tuni ya zare min rigata tare da kashe light, gaba daya ya gama haukatani ni kaina abinda nake masa ba a cikin hankalina nakeyi ba, ba komai a jikinmu haka muke murzar juna, kalamai yake sabo da sucking na fara masa ko gidan ubanwa na koya oho wannan abu kamar da Aljanu sai kaji ka iya kaima🤣
    Kukan dadi yakeyi yana zazzagar da kalamai amma ni bana yarda kawai dama na karya ne tunda nasan Business yace ayi,nice nakeyi da gaske a raina, boobs dina yake murzawa har shidewa nakeyi,kiss kuwa yau ina jin sai lips da tongue dina sun kumbura maybe dan sun tsotse a wajensa,yau wani abin mamaki sai ga Aayan yayi releasing sosai abinda Bai taba yi ba tunda yayi aure sai dai a mafarki, bai taba tunanin zaiyi ba Sam shi yasa ma bai yi tunanin sexing dina ba Sam, ya dinga bakin ciki yana jin haushi yace ya zubar da yaransa a banza,za a wankesu a ruwa,na dinga dariya nace yanzu haka ma yan biyu ne ko yan uku ma,ya kara Jin haushi yana kwance gefe,na ce yanzu haka akwai me Sunan Mommynka a ciki ko me Sunan Daddy, dariya yayi tare da cewa wlh ba a wanke Daddyna ba ai Me sunan Daddy yana nan zuwa nan gaba bakiyi abinda zai fito ba,sai Abbansa yaji dadi da yawan gaske sannan me Sunan Daddy zai yo waje,haka kace ko? Ya jawoni jikinsa tare da cewa tnx Baby kinci kudi me yawa yau mota sabuwa dal da dalleliyar waya me tsada kika samu,ni haushi ma ya bani maimakon murna bai San dadin dana ke ji ba na faranta masa burina na ganshi cikin Jin dadi amma shi tunani yake ma dan kudi nayi ni Sam yanzu ba kudin bane a gaba na ba so nake ya so ni kawai.
   Shuru yaga nayi bana murna kamar baya can,ko sunyi kadan a kara miki? Nace a'a na gode hakanma sun isa,murmushi yayi yana kallon yanayi na,nayi miki kema kiji dadi? Jin dadine yasa nayi murmushi nace ae,ya fara gwangwajeni da salonsa nima saida na ji zam zam,garin kuma sani naji dadi shima ya sake dawowa ruwa nan na kara masa abubuwan da kawai ya kara kawowa,kamar yayi kuka sabo da takaici yace next time kawai Sex zaiyi shi kam,ina ta tsokanarsa har bacci ya kwashe mu,tun daga Ranar kuma ko me zamu yi bai kara kawowa ba,dama kuma baice ma zaiyi xxx din ba.

    Ameer kullum shi yana wajen Hajja sabo da sun shaku sosai duk wani plan din ta ya sani,duk bai damu ba dadi ma yakeji shi za a sa Aayan ya sakeni,kawai sai yaji Hajja tana cewa za a sa min ciwon hauka ko kuma wata cuta ko wacce za a rabani da gidan su Aayan gaba daya,nan hankalin Ameer ya tashi ya za ayi a haukata masa Mufeedansa,shi da yake so ya Aureni yana kauna ta baya kaunar abinda zai cutar dani ko ya ganni cikin wani Hali,nan take yace dole na dau mataki kan Hajja na hanata aikata abinda take niyya,nan ya dinga sawa Hajja ido har ya gano magungun nan data ajiye tana jira na dawo ta aikata abinda bokayen suka ce mata,Ameer murna ta kamashi ya kwashesu gaba daya harda wata yar tukunya da wani ruwa a ciki,ya zubar da ruwan a tsorace,ya fasa tukunyar,garin maganin da ruwan rubutu duk ya samu jikin katangar gidan ya haka rami me zurfi jikin flowers yanda baza a gane ba ya zuba rubutun ciki garin maganin ya juye su daga ledar a cikin rami sannan ya maida kasar ya binne su sosai yanda ba za a gane ba ya kwashe ledojin ya zuba cikin Dustbin.

    Bayan kwana biyu Hajja ta duba taga ba komai,kamar me ciwon hauka haka ta fito tana ihu da masifa,ta tambayi kowa amma ba wanda yace ya gani,Ameer kuwa dama tasan na wajenta ne bazai ma dauka ba sai dai ya goya mata baya shi yasa dashi ake tambayar yan gidan yana masifa kamar gaske,Hajja ana sa masa albarka ga wanda ya gajeta,haka a gaban Ameer ta kara buga waya wasu malaman sunce baza su sake samun irinsa ba bare su bata,wasu kuma sunce ta koma ta karba,Ameer ya makale mata tace ai shi zai kaita ma su karbo,kafin su tafi ya tara yan iska ya biya su kudi kan a tare motarsu su kwace jakar Hajja kudin dake ciki nasu ne masu aiki sauran maganin da suka samu kuma su bashi a hannunsa zai nemesu,haka suka tafi gari gari har wanda a jirgi sukaje daga nan suka je na kauyukan kano duk suna jakar Hajja tana murna,Ameer yana Driving tana gaban mota suna ta hira tana fada masa tsare tsarenta wanda zata shiryawa Mufeeda,suna tafiya hanyar daji daji ba kowa sai ga yaran Ameer sun tare motarsu kamar gaske suka kwantar da Ameer a kasa Hajja kuma suka kwace jakarta tana rokonsu suna ganin makudan kudin da suke ciki suka dinga murna suna godewa Ameer a Ransu,suka kwashe kudin tas,magungunan kuma sukace wato gidan bokaye kuke zuwa ko? Kune masu hana mutane Zama lfy a duniya Allah ya tonaki tsohuwar banza ke da jikanki yau karshenku yazo,Hajja ta fara magiya tana rokon kar a taba mata jika sabo da tana son Ameer sosai ita tun asali tafi kaunar Ameer da kowa,Ameer ya kifta musu ido su kyaleta haka su kwashe komai su tafi,ai kuwa suka kwashe komai suka jefawa Hajja jakarta,Ameer ya tuna da rubutu jarka har biyu a gaban mota yana sani yace Hajja maganin sun kwashe Allah yasa muna da biyu a gaban mota,kamar gaske suka take mishi wuya sukace au harda wasu a mota kuka boye Allah ya Toni asirinka dauko mana su ko mu fedeka,Ameer ya tashi yana kunshe dariyarsa ya ebo yana kuyi hakuri gashi kuje dan Allah,sai dai suka kaiwa Hajja masga daya sannan suka kara gaba.

    Hajja jiki na rawa tana kyarma a firgice tace Allah ya isanmu kaga shegun yara wannan turosu akayi,Ameer yace sannu Sannu Hajja ta Allah ya saka mana muje muyi mu bar nan kar su dawo ko wasu kalar suzo su harbemu,Hajja tace iceko baka ji rauni ba Ameer dina naga sun take ma wuya,ai munyi arziki da basu taba min kai ba,yana Driving Hajja tace yanzu me zan cewa malaman nan? da wanne baki zance an kara sacewa? Ameer a ransa yace kai Allah yayi muguwa a nan wajen sai son kai amma bata son Mufeedata,a fili yace shawara ta ki Bari sai an kwashe kamar wata daya ko biyu ki koma muce mun aikata baiyi aiki ba Sam bamu ga canjin komai ba sai su bamu wasu kalar kinga me zafin ma zasuyi mana tunda sunji wannan baiyi ba,Hajja taji dadi tana dariya ta balli goronta tace hakane Jikana shi yasa nake sonka akwai dabara amma idan suka ce sun San karya ne fa?,kasan fa duba sukeyi sun San komai,Murmushi Ameer yayi yace karya ne Hajja ba wanda yasan gaibu duk raina muku hankali sukeyi idan kina so ki san karya ne kije da jakarki ba komai a ciki kice ya duba miki mene a ciki idan ya fada ki bude wlh bazai San mene ciki ba wani abin ma da zaki ji sun fada Aljanu ke fada musu wani karya wani gaskiya amma sai ku dinga yarda,ai kamar Hajja zata daki Ameer ya karyata malamanta tace Wannan sabo kakeyi Ameer malamai magada Annabawa kake fadawa suna karya,Ameer ya dinga dariyar Jahilci n Hajja dan sunyi Islamiyya sun San komai,amma ganin baza ta gane ba kawai ya canja zancen ya kyaleta,ita ko sai masifa take masa,har ya gaji yace Hajja ke dai baza ki gane karyar mutanen ba a hadisi  aka rawaitosu ko a Alqurani?, Salati Hajja ta saki tace yau naji dan iskan yaro to yi min Wa'azi Allah ya taimakeka kaine da Mujaheed ne ko Khaleel wlh yau da basu kwana a gidan mu ba,ka kiyayeni rakani kayi ba Wa'azi nace kazo ka min ba,kai din abin arziki kake aikatawa? Wanne iskanci ne baka yi,ai ni nasan wlh ba dan iska bane tunda ni bana bin mata duk a baki kike ji ina surutuna ko kin ganni da mata wlh ni ba zina nake ba,ban taba yi ba,ko kinji nace Ina son mace wlh da aure nake sonta ni bada iskanci ba,bana fata na ajiye mace don kawai naji dadi da ita sai dan na aureta gaba daya har karshen rayuwata,Hajja tace Sajeeda fa ai tace ba abinda bakayi da ita ba? Wlh sharri ta min don na aureta amma ni ban lalata mata rayuwa ba kuje asibiti a dubata,idan ma an ganta a lalace to wlh Allah wani ne ba ni ba,ke kin San ni ba irin Khaleel bane ko Mujaheed wanda basa fada sai dai aga sun aikata sune masu son ayi fasikanci da mata, Hajja tace uhm naga Alama ai nasan halinka Ameer kai dai a barka da masifa ga kawo shawara wajen iya hada tuggu,to amma mene hadinka da mata tunda gashi duk inda za a ganku da mata kuma Sajeeda nima ai ina ganinta a dakinka,Hajja kenan kina son Gulma,zan ci ubanka wlh karka kawo min raini,ayi hakuri Hajja mata da kika gani Allah daya dan rage Zafi nake dasu ina dan tabe tabe a jikinsu idan na danji sai na kyalesu,Sajeeda kuwa har room take Bina na kwanta da ita naki yarda,tace na aureta naki shine take talla da kanta ganinta hakan ne zai sa na sota ni kuwa kara tsanarta ma nayi wlh ba wacce na tsana sama da ita,kuma ban aikata komai da ita ba sharri take min,Hajja dan Allah kar a aura min ita wlh zan iya mutuwa,banza Hajja tayi dashi sai daga baya tace amma kasan tana sonka,ae amma ai badan Allah take so na ba cewa fa tayi don duk gidan nan ni kadai nake kama da Yaya Aayan daga Aayan sai ni a kyau na yan gidan nan shine fa dalilinta dama nasan Aayan take so ba ni ba,ba sai ku aurawa Aayan ya kara ta biyu da ita ba,Hajja tace halina da kai basira haka za ayi aure za a kara masa ta nan zamu samu Damar wulakanta Mufeeda,Ameer najin haka yace ai kuwa bazan bari a aura masa Sajeedar ba tunda za a taba min lafiyar Mufeedansa ta nan za a dinga kai maganin bokaye,wa ya sani ma ko Sajeeda ta dinga dukan Mufee dinsa kullum ina Sam da sake bazai yuwu ba dole ya canjawa Hajja shawara amma sai ya nutsu ya samo dabara.

    Washe gari naje schl na dawo wanka nayi na shirya cikin wando pencil brown  riga Maroon na gyara gashina kamar wata Baturiya ba karamin kyau nayi ba, zaune nake a kujerar dake kitchen ina yanka cabbage, kamshin Aayan naji kafin na juyo naji ya tsaya a bayana tare da dafa kafaduna da hannu biyu a hankali yayi Sallama na amsa tare da mikewa tsaye nace sannu da zuwa, na kwanta a jikinsa ba tare da na tallabeshi da hannayena ba sabo da akwai cabbage a jiki,kallona yakeyi sosai yanda nayi kyau amma Bai ce nayi kyau ba,lemon Fruits dana hada  yayi Sanyi na tsiyaya masa a glass cup na mika masa ya karba ya shanye na karbi Cup din shi kuma ya bar kitchen din ya haura samansa,na dan Dade a tsaye ina tunanin ko lfy? Dan naga kamar yana cikin bacin rai amma ya zan masa tunda baya iya fada min matsalarsa sabo da ba sona yake ba nice dai nake wahalar da kaina a raina nace wlh bazan iya ba kaje kayi ta fushinka da kaina kuma nayi wa kaina fada ni da nake so ya soni back kuma in Zama jigon rayuwarsa na tsaya wasa gwara idan na sace masa zuciya sai na shareshi yanda zaita wahala a kaina yessss na fada da karfi wlh haka za ayi yanzu bari na kwantar da kaina first yanda Meenat tace nan ma da karfi nace shegiya Meenat yarinya da fusaha,da sauri na ajiye aikin da nake na wanke hannuna na bishi samansa sabo da irin su Aayan son girma garesu suna bukatar biyayya sosai.

    Ina shiga na iske wanka yake sabo da na sanshi ya sanni don ba kaya ma muna romancing juna me yayi Saura kuma kawai Toilet din na Murda handle din sannan nace na shigo,shigo mana kinga na huta ma,Shiga nayi da towel a jikinsa ya shafa shaving cream a kirjinsa zai fara aski, na karbi a bar askin na jawo masa wata doguwar kujera ya zauna nace aske gashin kirjin zakayi harda shi gaba daya? yana kallon shiga ta wacce tayi matukar yi masa kyau yace kinyi kyau idonsa har ya canja nace tnx amma yanzu har kirjin zan aske? Kina so ne? Hmm in ina so ma ai baza ka barshi ba tunda baya cikin Business dinmu, murmushi ya saki yace sai a zame wasu kudin cikin naki tunda ke kike so kece zaki biyani kudin ajiye miki shi,kuma yana da tsada kin sani,nace a'a karka taba min kudi aske abinka na hakura,in kina so zan bar miki kyauta,to ina so a bar min,hanci ya lakace min Hajiyar kudi kenan,dariya nayi nace to an fasa askin ai sai kazo ayi wankan,jansa nayi yace ai baki isa ba yarinya sai dai ki tube muyi tare amma baza ki min wanka ki kalleni ba bazan yarda ba sai dai ayi 50-50,Dariya nayi nace a'a to mene na jin kunyata abinda nasan komai na kai hannu zan janye Towel din ya ja gefe da sauri tare da Jana ya tura ni bedroom ya kulle kofar yace je ki kawo min abinci kafin na fito,lallai Aayan yana da kunya wasu mazan kuwa ba ruwansu amma shi ya sanni na sanshi amma kunyar na kalleshi yake.

   Kafin ya fito na shirya masa komai a dakinsa ina zaman jiransa dama wankan sa dadewa yakeyi sosai yafi mata ma,yana fitowa nace nazo? Yana dariya yace a'a dan Allah zauna abinki zan yi da kaina nasan halinki kice zaki cire min towel,ina zaune ya gama shirinsa tsab cikin kaya marasa nauyi,nace Ohh kayi kyau shi kuma ya dawo inda nake zaune a kasan Carpet dake dan gefen bed na sa abinci gaba,ya wara kafafuna tare da Zama a gabana ya jingina bayansa a fuskata,kayi kato ai Sai kace wani yaro zaka zauna min a gabana kalli fa ta ya zan baka abincin kato da kai a gaban  karama haka ka fiye son jiki,ni a Sanina mace tafi Namiji son jiki sai gashi kai kafi macen ma,sauri ki bani abincin wajen Daddy zan je yanzu,nace da dare nan haka? Ae mana dan Allah kaje Dani pls kaji,Su Meenat fa? sai mu tafi dasu ko a barsu a gida,hmm ina tunanin ma fa Family House zamu koma again tunda naji abinda Daddy ke nufi kenan,Nan take hankalina ya tashi,raina ya baci,muna jin dadinmu shike nan amma ya za muyi ko dan sabo da Daddy sai mu koma,a fili kuwa ban nuna damuwata ba sai ma nace ah kace mu shirya kayanmu amma an gyara mana part ko tunda har almost 1wk bama ciki,yace an gyara komai neat amma ban san me yasa ba ban son komawa amma Kin San Hajja zata takurawa Daddy ne ta fara fushi dashi a kaina,abincin na fara bashi me shegen dadi fried rice tasha hadi da kaji sai fruits da sauran kayan ciye ciye,nace ba matsala karka damu zamu koma ko dan Daddy ba abinda zai faru,kin san ma mene? Nace sai ka fada yace Ameer shike zuga Hajja akan komai na tabbata ma yanzu shine yace sai an dawo daku gidan,nan take na kara Jin tsanar Ameer a raina,Aayan yace Ameer shi ya gaji Hajja a mugunta komai shike tsara mata da Alama ya tsaneki kamar haka nake gani,baki na tabe ta Allah ba tasa ba,ya zaiyi dani ai ni Duwawu ce dole a zauna dani,shegen dan iska,jaraba annamimi da fuska kamar yalo, dariya Aayan dinga yi yanda yaga sai zagin Ameer nakeyi ba ji ba gani yace zagin ma harda Raps Baby ba a tsayawa a huta,dariya nayi nima nace Allah dan iskan yaro sai iyayin jaraba yana gadara da takama sai kace shine Aayan,to ko shine Aayan ma ya isa ya min na kyaleshi,Dariya Aayan yake au nine ma me gadara da iyayi? Nace a'a misali nayi hhh,Allah mutuncinsa daya da yasa nake dan raga masa yanda kuke dan kama dashi kadai kuke kama a gidan nan ni ban san ma ya akayi yayi kyau ba matsiyaci,Nan take naga Aayan ya hade girar sama data kasa kamar zai dakeni,lfy? Allah Baka hakuri in dai akan na zagi dan uwanka ne,Allah dan kuna kama....Tsawa ya buga min rabon da naji irinta har na manta tun farkon haduwarmu dashi,masifa ya fara ni bama kama zaki ce yana da wani kyau baki da hankali idan sonshi kike ba sai kin fada min haka ba ya ja tsaki ya haura saman Bed abinsa.

   Firgita nayi kaina ya daure daga ana labari sai fushi kuma ni mene hadina da wani Ameer kuma,mikewa nayi nace kayi hakuri ba haka nake nufi ba ni,da sauri ya Zabura ya Mike hado kayanku a kaiku can sai ki dinga ganin Ameer me kyau,Ka fahimceni bafa nufina kenan ba wlh,mene abin fushi a nan ana lbr to kayi hakuri na furta cikin sanyi na,shekeke ya kalleni yace na rantse yau sai kun koma Family House Hajja bata isa tasa na Canja muku gida ba ra'ayina ne ganin damata ne dan kawai hankalinku ya kwanta muje kawai na rigada na rantse,gani nayi ina lallabashi yana wani kara hawa nace fine mu koma mana mene to, na fice na bar masa Bedroom din naga cikin fushi yake gaba daya yau. 

    Su Meenat suna shigowa na sanar musu su Kansu basu ji dadi ba,nace su hada mana kaf kayanmu,Meenat tace sis dazu naga wani wlh kamar Abbanmu a mota wani me kama dashi tsaki Naja tare da cewa sai me to dan kin ganshi tunda bai neme mu ba me zamuyi masa,Sis kamar fushi kikeyi lfy? Ko fada kukayi da mijinki? Nan take na fara hawaye ina sanarwa Meenat,Meenat tayi dariya tace Sonki yakeyi kishinki ne,ke komai kiyi fushi ai ba haka akeyi ba,ki daina cewa zaki rama abu ko dole sai kin maida martani kinji mene abin Kuka ai zaku shirya ne,idona na goge muka shirya,Sai ga Aayan ya leko fuska a tamke yace let's go,muka bishi har mota da kayanmu,Driver ne yaja mu har gidan sai da ya tsaya a inda ake siyar da wayoyi ya siyo guda biyu masu kyau da shegiyar tsada ya bani daya ya bawa Meenat daya,sai Meenat ce kadai tayi masa godia ni shuru nayi masa muka je har gidan,Ameer yana so zai fita da mota kawai ya hangoni wani farin ciki ya kamashi Bai San sanda ya tsaya ba ya fake da gaisawa da Aayan,Bro ya kk? Aayan yana fushi kamar zai tsage yace am ok,ya kalleni kawai yace Sis barka da zuwa ko kulashi banyi ba Meenat ce ta amsa,sai da ya kara yi min magana sannan na amsa da kyar ina fitowa da kayanmu,yace Bari na tayaku kaiwa ciki,Aayan yace no need jeka abinka,murmushi ya saki a ransa yana ko banza zan dinga kallonta ina jin dadi na.

   Hajja tana sama tana kallonmu sai murna takeyi burinta zai cika,Abbi bakin mugu yana kusa da ita yana tsara mata muggun nufi,matarsa ma haka tare da sauran  kannen Abbi,Ameer kuwa ganin na dawo sai ya fasa fita kawai ya koma part dinsu.

    Aayan sai fushi yakeyi nima haka aka shigar mana da kayanmu, komai Neat a gidan yasha gyara sai kamshi,muna Hutawa muka wuce bangaren Daddy har Meenat muka kwashi gaisuwa sai murna yake yana jin dadi tare da sa mana albarka,bamu zauna ba muka dawo part dinmu tare dasu muka fada kitchen kamshi ya fara tashi a bargarenmu,sai ga jaraba sun fara shigowa,Sajeeda da Haneefa sunzo harda lekowa kitchen suna tabe baki Sajeeda tace yara ana ta jagwalgwalon ne? kamshi na tashi kamar gaske a baki ba dadi bari yau zamu dan dana muji,Aayan yana jinsu basu San yazo sakkowa kasa ba,yace kafin nazo nan waje Ku tabbatar kun bace min a part Nonsense ya furta yana Jan tsaki,da sauri suka fice Sumi Sumi sai suka tafi wajen Hajja,tana ganinsu tace to fa Allah kawo mu jaraba ta dawo na shiga uku da kawo kara me tayi muku,nan suka shirya karya wai nice nasa Aayan ya zagesu kuma nace ya koresu,Hajja da kanta tace muje wajen nata na daina saurara mata.
    Suka taho Aayan ne ya bude musu kofa Hajja ta fara ta kansa kamar zata cire bakinta tana zagin Aayan,Haneefa tace daga munce idan ta gama girki ta sanmana sai zagi,Hajja da karfi tace ina makirar take tana shigowa kitchen tace gidan ubanki ne ko kayan abincin uwarki ce ta zuba mana,to dole suci idan naga dama ma part dinsu zaki je ki dafa musu abinda suke so,Aayan yace wlh basu isa ba ai ba baiwarsu bace ni na biya sadaki na aureta ba wanda zai sata ko ya hanata sai ni,Hajja ta fashe da kuka Wlh sai na fadawa ubanka yiiiiiiii,muna jinsu a kitchen tace ke dan uwarki wlh sai jikokina sunyi abinda suke so baza ki raba min kan zuria ba,matsiyatan bayi a gama a zuba musu suci,Meenat tace ga danye nan shine naku shi kuka siyo da kudinku wannan kuwa mun rigada mun dafa,kuma hakki ne a kan miji ya ci da matarsa muma tunda ba mutunci baza mu basu ba basu kai matsayin da zamu dafa musu abinci suci ba,Hajja tace iyeeeeee kana ji da girma na suke fada min haka? Yace ai Hajja kin dade da zubar da girmanki shi yasa suka take amma matata me tarbiya ce,Haneefa Hajja ta kiftawa ido tare da cewa Ku zubar da abincin uban kowa ya rasa,Aayan yace wlh duk wacce ta zubar sai gaba daya kun bar gidan nan yau ba gobe ba ai ba gidan ubanku bane,akan Mufee ba abinda bazan iya ba dama darajar Daddy kuke ci gaba daya zaku bar min gida wlh kunji na rantse,haba wani dadi ya kamani a kitchen mijina ya tare min fada ya nuna yana sona a gaban kowa,Muna haka sai ga Ameer da zureriyar wayar wuta,yace ke Sajeeda dan uwarku abin naku har ya kai kuzo kuna zagin matar Aayan,a ransa kuma matarsa yake nufi tunda sona yasa baya so ko sauro ya cijeni,Sajeeda zata masa rashin kunya ya fara tafkarsu son ransa sai da ya Zane musu jiki Hajja na tsine masa tana kuka.

   Gaba daya fadan ya koma kan Ameer Hajja ta sanarwa Abbi,nan fa Ameer aka hadu a kansa suka masa tatas,a ransa kuwa yace babu wanda zai taba Mufee na kyaleshi,ta nan bangaren soyayyar Ameer a gareni rahma ce sabo da shi ke Tsarawa Hajja komai baya bata me kyau a kanmu yanda zata ci mana mutunci,shi kadai ya samu Hajja ya lallasheta ta hakura yace Hajja Ku baku iya mugunta ba ai ba a nunawa mutum a fili ba a sonsa ta kasa zamu bullo musu ki daina bari ana musu a gabansu sai su dauki mataki suma fa suna zuwa gidan malamai nan Ameer yasa Hajja farin ciki ya gama tsarata tsab,yace Asiri muka yiwa Aayan yanzu abinda zasuyi a karya asirin dake jikinsa sai a dora sabon aiki,Hajja ta fara kiran malamai tana so a karya asirin dake jikin Aayan ko wanne iri ne,maganin tsari take so ayiwa Aayan sannan ta sake sabon kalar nata.
   Hajja ta manta Sam anyiwa Aayan asirin da bazai Haihu ba bazai iya komai ba,Kuma tace a karya komai dake jikin sa ko zai karye din oho?

  Abbi Kansu suna mamakin Ameer bai fiye shiga harkar su ta makircin da suke aikatawa ba sai jefi jefi amma kuma yanzu yafi kowa bawa Hajja shawara a kanmu,sai sukayi tunanin Ameer ya tsane mu ne da yawa shi yasa,suma murna sukayi za ayi maganinmu sunga muna nema mu canjawa Aayan zuciya kamarma ya fara sona tunda sunga yana bin umarnina sabanin wancan matan nasa na baya,amma Abbi yace shima dole ya shiga harkar nan dan ganin ya raba ni da Aayan.


          71-75
By
AsmaBaffa

   Ina matukar Godiya ga masu Sharhi Allah ya bar Kauna,kuma Insha'allah daya bayan daya sai kunga sunanku a Novel din nan na Kasuwanci na,sai dai ko Halin mantuwa,ina ganin sharhin ko wacce kuma kuna cikin list dina,sai dai duk wacce taga kamar na manta da ita ta tuna min pls love u all❤❤

   Sai masu Sharhi wanda zasuyi watarana ban kula ba suga banyi musu reply ba kuma nayiwa wasu to ayi min Afwa ban kula bane, wacce taji ban kyauta mata ba kar tayi shuru tazo taci kwalata sannan ta tsige min dankwali ta wankeni tasssss🤣🤣🤣na baku dama.


   Ga page dinki ta gidana,Al albarka, masoyiya ta gaske me Sharhi kamar ruwa,kina birgeni KHADIJA A HAMZA



  Gaisuwa ta zuwa ga babbar me kaunata HANAN ta Gp na gata nan na Cillo ta ki cafketa.😍









    Abbi cikin takaici ya ja Hajja bedroom dinta yana cewa Hajja munyi sake,wlh munyi sakaki,taya zamu bari mu rasa dukiya muna ji muna gani,kin san yaron nan ya fara son yarinyar nan shike nan wlh sai abinda tace dashi talaucewa zamuyi dan naga Alama yarinyar nan bata da imani ko kadan, nan Hajja ta fada masa tsarinsu da suka shirya ita da Ameer,Nan take Abbi ya Dafe kai,yace shike nan kun kashemu iceko baku aikata ba? Ya zaki biye wani Ameer ai Rusa mana aiki ne wannan kin San mene a jikin yaron?dama da kyar muka samu wannan ya zauna a jikinsa,Hajja tace mene abin yi? Abbi da yan uwansa sukace ki bar komai a hannunmu,Ameer yazo shigowa wajen Hajja ya dau wanka so yake yazo part dinmu na ga kwalliyarsa.

   Yana jin me su Hajja suke yi hankalinsa ya tashi tabbas yasan sai sunga bayan Mufee amma yace ina Sam ba a isa ba baza a Rusa masa farin ciki ba,Shiga Bedroom din yayi tare da Zama gefe yana jinsu suna ta tsare tsare dan kar su gano shi sai ya dinga kiftawa Hajja ido yana mata signa da ido,ko idan Abbi yace ga abinda za ayi sai Ameer ya makewa Hajja kafada wai kar ta yarda,Hajja kadai ke gane me yake nufi,su kuwa su Abbi basu sani ba,sai ji sukayi Hajja tace me kuka sani,me kuka iya,har nawa kuke a duniyar,ni na tsuguna na haifeku zaku zo kuce ni zaku canjawa tunani,to baku isa ba iyyeee wato Ku ga wayayu wayonku yafi nawa?Ni wato bani da tunani ban san me nake ba ko? Abbi cike da ladabi ya Dafe kai yana Oh Hajja ki saurara kiji,Ameer ya kara makale mata kafada yana mata signa,Sani Kanin Abbi yace kai dan ubanka me ya sameka ne ko kafadarka ke ciwo ko tabin hankali ka hadu dashi,Abbi yace Lfy? Yace gashi nan Ameer sai wani makale kafada yake yana wani farfari da Ido ko dan daudu ka dawo bamu sani ba,kaga dan iskan yaro to uban me kake yi, pink lips dinsa ya turo yace to ni me nayi daga abu ya cijeni sai ace bazan sosa ba,Abbi yace to zaka bar dakin nan dan uwarka,Hajja tayi gazal tace kar Ku Zagar min shi ba ruwanku yaron kirki irin Ameeru dan albarka,Abbi ya tabe baki yaci gaba Hajja ki Bari muyi tsarinmu,Hajja tace sam bazai yuwu ba ni zanyi haka kawai na zauna jiranku wankin hula ya kaimu dare komai naku na yan boko sai anyi lissafi an tace an rairaye sannan a aikata,mu kuwa sha yanzu magani yanzu,Abbi suna matukar yin biyayya ga Hajja basa tsallake maganarta haka suka kyaleta cewa tayi nata suma za suyi nasu,Ameer ya kara kallon Hajja ya makale mata kafada Hajja tace a'a  ban yarda ba Ku bari idan na gama kalar nawa Bai yi aiki ba sai na baku dama kuyi naku mu gani,a haka suka tsaya amma Abbi yace karta je a karya asirin jikin Aayan pls sabo da akwai shirinsu a jikinsa,A nan kawai Hajja ta yarda cewar ta fasa karyawa kawai zasu ci gaba da nasu,a nan Ameer bai hana ba tunda ya hana abubuwa da dama kar Hajja ta ganeshi ne kawai ya hakura.

    Direct part dinmu Ameer ya zarce irin dole fa naga wankansa wanda ni ban san me yake nufi ba, ya kuwa yi dace muna zaune tare da Aayan a Palo yana fushi dani tun kan maganar Ameer dan nace yana da kyau,yaki cin abinci yau fushi yakeyi,har yamma 5pm yazo ya zauna a Palo,kuma nasan yunwa yake ji sai chat yake a waya,har sabon girki na masa kala biyu yaki ci,Yanzu haka ma Kunun gyada na masa na Dade banyi masa ba sai kosai naga yana sonsa,wanka na fesa Malam kamar a London cikin Wando tight iya rabin cinya Maroon,sai rigata fara me arnen kyau gashi yasha gyara na sakeshi na danyi masa style a gaban goshi kadan,Allah tsine wanda zai ce ban hadu ba yau ko mutum dutse ne yau ya kalleni sai jini ya fara gudana a jikinsa.

    Sabo da haka ma na kalli Meenat da suka dawo daga Islamiyya nace to ku zauna a Bedroom kar naga yar iskar da fito palo Dariya Sukayi Meenat tace to kin manta zamuje birthday party din kawata yau ni da Ma'eesha zamu wuce ta palon, wanne which kind party ba inda zakuje kun San dai ko Ammah na da rai bata bari muje wani party,bafa wani party bane na kirki sis,Driver baya nan kun sani schl ma yau banje ba kun  sani dai wa zai kaiku,zamuje a napep,fine amma kafin Ku fita kuje Ku fadawa Aayan shine ke rike mu yanzu kamar yayanku ne ko ma uba idan ya yarda kuje idan yace no shike nan.
   Meenat tace uhm lallai Sis yanzu mun koma hannun mijinki ma? To kici da kanki kiwa kanki Sutura sannan ki zauna a gidanki Meenat,duk wannan shike mana ai ko dole baza muyi gaban kanmu ba,ni macece Allah ya rufa mana asiri mun samu me Kula damu shike nan kuma komai sai muyi ba saninsa?

    To fa wasu idan ana rikesu a gida ganin wanda ke rikesu ba shine ya haifesu ba,kuma suna tunanin in ya tsine musu ko ya musu baki baza ta kamasu ba,kana gani zaka ciyar da mutum,ka shayar dashi,tufatarwa ka bashi ilmi da sauran abubuwa wasu ma ko yayansu basa yiwa rikon da sukewa dan riko sabo da su kyautata sai kaga kuma wanda ake rikewa yafi ma dan gidan iko,gadara,da rashin mutunci a gida,ayi ta ganin laifin masu rikon da ka zauna a gidan zaka ga yaron Ashe kwallon shege ne,ba wanda ya isa ya fada masa yaji,abinda yaga dama shi yakeyi baka isa dashi ba,da ka takura ace ka zaluncesu,kana gani zaita abinda yaga dama karshe ma wasu kaji a gari suna zaginka suna kala ma sharri cewar baka musu kaza kaza gari ayi ta tsine ma,karshe ma wasu su dinga cewa marikan nasu iyayen banza,ko a gidan suyi ta shirya ma mugunta iri iri suna zalintarka baka sani ba,more especially ace matar me gidan ce ta dauko wani ko wata take rikewa,suna ganin kamar itace da gidan ma ko saurarar mijin nata basa yi bayan komai shike yi a gidan suna cin arziki,kawai matar zasu fadawa itace take rikesu itace yar uwarsu mijin nata ko gaisuwa sai sunga dama,itama kuma tana kallo gani take ma ita ke musu komai ba mijin ba,bayan da dama zaka ga komai shi za a fadawa yayi musu amma Bai isa dasu ba,wani ko aikene sai dai ya aiki nasa ko na waje,da yawa ana magana kan azzalumai masu rikon yara ko yayan kishiya ko na yan Uwa ba a fadar laifin yaran,duk da cewa akwai masu zalincin Amma ya kamata mata masu dauko rikon Yara ko mijin ya kawo miki a daure a nuna musu muhimmancin me rikon nasu.ba kawai ayi ta yin abinda aka dama ba ana ganin ba iyayen da suka Haifa bane me zasuyi ya bika.

    Fita nayi ina sheka uban Kamshi Aayan zaune a palo yana danna waya na karasa dauke da hadadden tire jere da abinci iri iri,gaba daya bana jin dadin fushinsa yau,duk sai naji duniyar tayi min zafi,tun kafin na karaso ya zuba min ido yana kallona kamar ya hadiyeni naji dadi a raina ko bai fada ba nasan ya yaba kuma nayi kyau,kafin na gama tunanina ya juya min baya a saman 3seater tafkekiya,ni dariya ma ya bani kamar yaro na fushi,
  Ranka ya dade ga abinci ka daure kaci kaji,dama ni na saba da lallashin mutum kan dole yaci abinci ji nakeyi kamar nice banci komai ba shi yasa nake nacin sai anci abinci,Muna haka muka ji bugun kofar Ameer,na manta shigar dake jikina nayi hanyar Door zan bude, muryar Aayan naji a hankali yace kuma a haka zaki fita again? Da sauri na koma daki na saka Katon Hijab sannan na fito na bude kofar,Ameer yasha wanka gaskiya ba karya yayi kyau cikin kana nan kaya,Murmushi yayi min na bashi hanya ya shugo,Aayan tunda yaga shine ya kara hade rai da kyar ya amsa masa gaisuwar tasa,Yau Ameer harda ce min Aunty ya gida,ganin da mutunci yazo da fara'a na amsa masa nima sannan na koma kusa da kafafun Aayan inda yake kwance na fara masa tafiyar tsutsa a kafafu ina wasa da yatsunsa,Ameer yana satar kallonmu ransa ya baci sai kishi yake taso masa Amma ya danne, Aayan yana kallon yanayin Ameer shi bai yarda dashi ba sam yayi kicin kicin.

    Cike da shagwaba nace Yanlabai Abincin pls,wani shock yaji a jikinsa yanda nayi maganar shi kanshi Ameer sai da yasha mamakina a haka yar yarinya dani sai iya shege fal ciki,Ameer a ransa cewa yake ina ma nine Aayan gaskiya ya dace wlh irin wannan kulawa haka ga shagwaba kai da sake,a fili kuwa kamar baya jinmu danna wayarsa yake ya hakimce a kujera,Damun Aayan nayi da pls kajiii har sai da ya gaji ya mike zaune tare da ajiye wayar gefe can yace Bani zanci,da murna na zuba masa tare da mika masa,kin karba yayi yace hannunki aikin me yake? Da Sauri na gyara zama kusa dashi,yace ba fa a dining bane bazanji dadin ci ba,Nace ya zanyi to? Ke kika damu naci ai sai kiyi yanda kika ga dama ya fada cike da gadara, cinyarsa kawai na zauna samanta sosai bai ce komai ba sai lumshe ido da yayi ma,

na fara bashi a baki da hannuna idan na bashi bazai ko hadiye ko taunawa ba sai nace to ka ci mana sannan zai fara taunawa yana yanga yana kumbura wai fushi yakeyi shi fa,Ameer Kamar Tv yake kallonmu ya wuce gaban a share abin,yanzu ma waya Aayan yake dannawa yaki dago kansa bare na bashi abinci nayi nayi lallashin ya dago yakiya,sai ma ya kara yin can gefe da kansa ina binsa da kyar na rike kan da hannu na biyu na saitashi nan kuma ya tsaya Kikam a haka yaki bude bakin,Sai da nasa daya hannuna na bude masa lips sai ya datse hakoran nasa kuma suma,Yatsu nasa na ware su da kyar ya hangame dan mitsilin bakin nasa ya barshi haka,Ai Ameer tagumi ya rafka tare da Sa mu gaba kamar Tv yana ta dariya, na Sa masa abincin yaki kulle bakin bare ya hadiye nan ma Hannu nasa na rufe na matse bakin sannan ya cinye, haka yake ta bani wahala idan nayi wannan sai nayi wancan duk ya gajiyar dani ni kuma kamar dole sai yaci.
   Ameer ganin gatan Aayan yayi yawa ma haushi da kishi ya dameshi gashi wani abin yana sashi dariya ma watarana Amma kishi ji yake kamar ya mutu ko Ya batar da Aayan ace yau shine ake masa haka ai da yafi.

    Muna zaune na zubawa Ameer nace gashi Ameer kana shan kunun Gyada na sani ko? Ga abinci ma ka zuba ai ko ba ya sha sai ya sha yau tunda ni nayi girkin kuma daga hannuna ya fito, ya karba yana sha ko kallon Aayan baya yi Sabo da haushinsa yake ji ya aure masa Mufee Amma ta wani fannin yana godewa Aayan dan ta silarsa ya sanni kuma zai kwace ni nan gaba.

       Muna zaune sai ga Meenat da Ma'eesha sun dau wankan Material dinsu na ankon Birthday da zasu je yanda suka sha kyau ba a magana,Kamar yanda nace haka suka zo gaban Aayan tare da durkusawa suka gaisheshi cike da Ladabi sannan sukace Yaya Zamuje Birthday din kawarmu ta schl a gidansu akeyi idan ka Amince,mamaki yayi sannan kuma yaji dadi ga Sis dinsu basu nemi izininta ba sai shi gaskiya suna da tarbiya sun san me sukeyi,da murmushi dauke a fuskarsa yace shine kuka sha kyau haka salon a dinga kalkemin matana gaskiya am gealous dariya mukayi gaba daya har Ameer,Ameer yace Wannan Ma'eesha ai tafi kyau ma wannan Meenat ta fiye iyayin tsiya wai ita me kwalliya shi yasa bana kulata ni,Dariya nayi nace Wannan ai tsokanace Ameer kana ganin Yan mata an hadu,Ameer ya tabe baki tare da cewa masifaffiya dai ta fasawa Khaleel kai rannan wannan ai Dukan mijinta zata yi watarana, shi yasa ma bata da saurayin kirki sai irin su Kwaja da Nasuru Opera,Aayan ya sheke da dariya Kai Ameer wanne Nasuru Ópera din kake nufi? Ameer yana dariya yace Opera daka sani wanda su Haneefa suke aikensa Sa ido wajen wanda suke fada ai Camera suke bawa Opera Sabo da shige shigensa ake ce masa Opera kaga ko ina ka shiga ta Opera kayi Searching,Dariya muka dinga yi banda Meenat da take son yin Kuka.

   Ma'eesha tace wlh mantawa nayi Sis ban fada muku ba rannan ma a hanyar schl wani ya dinga bin Meenat yace sunansa FELA me GALA wai shi dan rawar gala ne  a kasuwannin kauye baku ganshi ba kafafunsa kamar na sauro yasha wandonsa Fela kato sai uwar Kafada kamar ansa riga a hanger ,Ameer yana dariya yace baki da sa'a Meenat Allah yayi a cikinsu zaki samu miji wai ya akayi ke duk wankan naki da iyayinki kike karewa a yaran su Sajeeda,Nima nace dama Yaran su Haneefa ne? Ameer yace sosai ma ai Fela Gala shike sanar musu duk wani wajen chasu idan za ayi show Saturday sunday irin su Haneefa ai duk basa muamula da manyan Yara,ki kula ki gani duk wata yar duniya me ji da kanta zaki ga mace har mace ga kudi ga kyau Amma indai lalatacciya ce bata taba kula mazan kirki sai daí ki gansu da maza kazamai,garori,munana, tabbas zancen Ameer hakane na fada a raina duk haka yan bariki suke kuma mace na ji da kanta Amma in kaga wanda take kulawa suna harka sai ka kusa kuka.

   Aayan yana dariya ya kalli Meenat da ta hade kamar yar Minister ya kasa rike dariyarsa duk ya san yaran nasu Sajeeda,karku damar min mata Kunji na fada muku kai Ameer tashi ka kai min su Driver dinsu dama baya nan kaga kaima kaci wanka kuje ko zaka samu wata Operiya a can kaima, wannan yarinyar da bata da kunya zaka ce na kaisu,Magana nayi nace haba Ameer ka kaisu mana kuje ku dawo yanzu ko dan ni ka taimaka,Ameer yace  a ransa dole na kai tunda Umarninki ne Queen Mufee ta,Tunda zan faranta miki ai zan kaisu dole,A fili yace Sunci darajar Ya Aayan da ke  kuzo mu tafi kuma ku tabbatar takalminku fes yake kar a bata min mota,Meenat sai Harara take zuba masa har suka fita tare gaba daya,da Sauri ya wuce wajen Hajja yace ku je jikin mota ina zuwa,

yana Zuwa wajen Hajja tana ta faman kurbar kunu yace Hajja Albishirinki na samo babbar hanyar maganin matsiyatan nan,Hajja tace mene abinda ka samo fada min Dan Albarka, yace yanzu zan shiga jikinsu sosai zaku ga muna mutunci dasu sosai,zan kwantar da kaina a wajensu yanda zasu yarda dani kinga kafin mu karbo maganin da zamu Sa musu na kulla alaka dasu me karfi ni sai na shige na aikata komai da Komai ko Ya kika ce,amma in ba haka ba za a samu matsala wajen aikata abinda malamai suke so a kansu tunda basu yarda damu ba,don haka yanzu zan fara kullum zaki dinga ganina a part dinsu zamu dinga mu'amula har su yarda dani cikin kankanin lokaci sai kawai mu gama dasu,Wani farin ciki ya kama Hajja,tace haka za ayi yanzu ka kawo magana me kyau,amma da ubanka yazo min da maganar banza ba basira ba wayo a ciki,to Amma kana ganin zasu yarda ka shige musu jiki har su yarda dakai? Ameer yace har nayi nisa ma yanzu ma sun yarda dani gashi nan sunce na kai mata kannenta wani party na dawo dasu,Hajja ta mike tsaye da murna dan Manzon Allah fa? Ko wasa kake?Yace da gaske leka ta window zaki gansu shi yasa nazo na sanar miki kar a kawo miki gulmata ki yarda kin san muna tare ke nakewa aiki,Hajja tace yo wa Isa ya kawo min gulmarka dan Albarka ai kasan bana yarda da maganar su a kanka,dariya Ameer yayi a ransa yace tsohuwa kenan nima kaina nake gyarawa hanyar samun Mufeeda na aureta ina ruwana da wani kudirinku ke dasu Abbi can da yawarku,a fili yace Hajja me zan siyo miki? Hajja tace abinda ka saba siyo min kullum dan Albarka,Ameer yace ai yau ba Hantar Rago kadai zaki ci ba harda yan shila idan ma dawisu kike so shi zan kawo,Dariya Hajja ta saki tace Ko mene ma duk ina so tunda kaine dan Aljanna.Ameer ya fito ransa fes ya tsara Hajja Sabo da yasan ana ganinsa tare da Su Meenat za a kai gulmarsa wajen Hajja ta daina yarda dashi,yanzu kuwa ya kashe bakin tsanya.

    Yana fitowa ya harari Meenat ke zaki shiga baya Ma'eesha ta ce zata shiga gaba tafi kyau baza a ganni da mummana a gaban mota ba,Meenat tayi banza dashi ta shiga bayan felleliyar motar Ameer, Ma'eesha a gaba,Ameer shi irin yan Tsabtar nan ne da shegen iyayi shi a dole Saurayi wankan ma da yake irin na mawakan turai matasa irin su Justin Bieber etc kowa yaga Ameer zaiyi tunanin kwallon dan iska ne ko ta askinsa kawai ba sai an tambaya ba,wandunansa kansu na zamani samari masu ji da kansu,Duk da cewa duk matasan yan wanka ne a gidan su Ameer Amma Ameer shi mata ma rubibinsa suke gashi da wanka Tsabta ga kamshi kuma yana da kyau wanda ke jan yan mata Uwa Uba ga diri me kyau.

    Aayan ne kadai bazai já dashi ba dan Aayan shi halittarsa ce ba kakalowa yayi ba haka yake komai in yayi me kyau ne,shiga kuwa dama shi a turai yake kana gani komai a jikinsa yake ba wasu yan dabaru akayi ba zallar baiwa ce,Shi kuwa Ameer tsabar kakale kakale ne da jarabar son iyayi ace Babban yaro sai da ya tsatso kyansa ya fito fili,Su Mujaheed ma haka suke shegun duniya ne wajen gayu,Suna Tafiya a hanya Ameer ya daga waya wata cikin yan matansa ta kirashi yanda ya kanannade murya kamar Sardaunan Ramlat yana Rapping English kamar wani Dj khaleed,Baki Meenat ta tabe tana jin iyayin da yake faman Digawa,aranta tace wannan wlh irin mijin Sis ne har kusan Halinsu ma sai daí Aayan karshe ne a komai,bayan ya gama wayar ya wani rare kidan Nija kawai tashi yake kamar zai fasa mana kunne,Maeesha ce mayyar rawa har ta fara yi a motar tana ihu uhhhh tare da dage hannaye sama,Shi kuwa idan kida yayi kida sai daí kaga ya bugu sitiyarin yana juya kan mota komar ma motar yakewa rawar,yanayi da kansa gashi duk Baiti ya iya abinda suke cewa kamar shi ya rerata, dama ga motar tasha tint ta samarin zamani,Maeesha yin abinta take wata tana shigowa me dadi tace ohhh yeee taci gaba da yi tana bi itama shi kanshi Ameer ta bashi dariya,ya kalleta yace ashe dai ke yar gari ce kin waye,duk kin san wakokin nan haka Amma kin iya rawa? Ma'eesha tace sosai ma ai  wayar Sis Mufee nake sacewa naje schl da ita na turo latest a wayoyin classmate dina,duk wacce ta shigo bata wuceni har rawar,Ameer ya mika mata hannu suka tafa yace kin birgeni ta gidana,ai kawai a Shana,tace tunin ma ai Baza a barmu a baya ba ina jss3 fa going to ss1 ai dole aje damu,Ameer yace yessooooo Baby,

Meenat tana jinsu suna tayi sun cika motar ga kida ga surutu suna ta yi da baki gashi ana jin wakar ana bi kuma da baki ga rawa anayi a zaune gaba daya sun gigita motar.
     Meenat kuwa wayarta take latsawa wacce Aayan ya siya mana tare katuwar gaske.
    a wani karamin hole akeyi Amma ya tsaru sosai wajen sabo da yarinyar dangin masu kudi ne shi yasa aka tsara abin,ashe yarinyar Cousin din Sameera me yan daba ce,itama Sameera tana wajen itace ma ta hada mata Birthday party din,Yan mata irin su Meenat duk sune a wajen ansha wanka da samari na schl Yara tare da wasu kuma manya sai yan Uwa,Yarinyar  Husna tasha wanka ana ta pics wasu na rawa,su Meenat ma suka Parker a wajen,Ameer yace ki bari yarinya na kankaro miki girma yanzu,Harara Meenat ta watsa masa,yace ni da zan taimaka miki nayi featuring dinki a wajen,Maeesha tace muje tare Yaya Ameer ni kayi ft dina ko a pics din da za muyi,kina ja Baby kanki na kawo light muje,ya rikewa Ma'eeshah hannu Meenat na gabansu duk inda suka wuce sai an kallesu,abinda Meenat bata sani ba an san Ameer sosai shima yanda yake nuna kudi da kalar Naira yana karyar arziki,kusan dama Daddy na Aayan ya makalewa lokacin Aayan bai dawo Nigeria ba,Ameer yake likewa Daddy sai da yayi suna sosai,ko a Tv za a nuna Daddy zai bude Abu sai kaga Ameer a wajen tun yana karami yake son ace shi wani ne yayi suna duniya ta sanshi shi yasa da farko bashi da Kamar Daddy shi yake masa labadi,ganin haka su Abbi suka juyawa Ameer hankali da ya girma sosai sai ya daina Saurarar Daddy gaba daya yake bin iyayensa.

     Ai kuwa Meenat tasha mamaki yanda taga ana ta kallon Ameer ana girmamashi ,mata na rubibinsa,Har uwar gayya Sameera tazo wajensa suka gaisa tace Ina Aayan?Yace yana gida,ka gaisa min shi,wannan yaran fa?ta furta tana mana wani kallon Banza,tana ta kallonmu tace Amma wannan sunyi min kama da wata sosai,yawwa yarinyar da Aayan ke aure,Ameer yace kannenta ne,Sameera tace kai Amma yarinyar bata da kunya ko kadan ina nan zan gyarata soon,nan take Ameer ya canja fuska yace ban gane ba? Tace kwarai tayi min laifi wanda ni kuma sai na nuna mata duniya ba kowa ake tabawa a kwana lfy ba,Ameer ya fusata yace lallai kema kuwa da kin tabbata wani in ya tabaka ya taba banza kuma ba kowa ake tabawa ace za a iya ramawa ba,wani in ya taba har abada ba a iya daukan fansa a kansa,Sameera tayi murmushi tace ba irinmu ba wlh,Meenat ma tace to ke har wace da baza a miki ki hakura ba wata tsohuwa ma dake,Sameera tace duk sai kun maimaita abinda kuka ce,Ameer yace Sameera kin san Halina ke a yan daban naki kanana ne kawai kallonki ake ana tunanin kin wuce haka Amma baki kai ba,wlh wlh kika sake wani abu ya samu Mufeeda ki fara irga kanki cikin wanda suka sheka lahira kin san mu kin san Halina try me.Dariya Sameera tayi tace Ameer kenan ko Aayan da take matarsa bai ce min komai ba sai kai? Husna ce tazo ta janye su gaba daya tana kuzo muyi pics nan fa suka dinga daukan hotuna Har Ameer dan shishigi cewar Meenat,yan mata kuwa jikin Ameer suke faman mannewa ana daukansu,anyiwa Ameer  ma haka inaga Aayan uban kyawawa da daukan wanka Meenat ta fada a ranta.

    Tunda su Meenat suka tafi naci gaba da bawa Aayan abinci yana min yanga,Yana karba da kyar har na gaji na mike na barshi a nan yana fushinsa,Kwashe komai nayi na gyara ko ina aiki yana kallona har Magrib tayi na shiga kitchen zan mana Dinner,Ban san sanda yaje masallaci ba kuma bai dawo ba har bayan Isha sosai,

     Su Meenat Suna gamawa Ameer ya dawo dasu gida sai da ya tsaya ya siyo musu ice cream sai yace banda Meenat bata da biyayya nawa dana Ma'eesha ne,Meenat tace sanda zansha ma ka sani ne,kuma sai na sha sai dai ka mutu.
    Ina gama girkin na gyara komai na gidan nayi wanka nasa rigar bacci ta da turare na kaiwa Aayan abincinsa yana dakinsa ya dawo ina ajiyewa na juya na bar dakin,Bedroom naje tare muka ci abincin  mu dasu Meenat muka koshi bayan ina dafawa naci wani kitchen Sabo da tsaro ko Aayan zai ce muci tare sai yaga ina cin kadan irin yar gayu ni.
    Muna gamawa mukayi Brush muka kwanta tare dasu kamar yanda mukeyi da,Meenat tace to yau kuma baza aje hirar ba?Nace ina ruwanki Sa ido,Meenat tana dariya tace a'a maida wukar bani na kar zomon ba,Sis yau ba jin dadi?Dan Allah da zafi ko dadi ne dashi nasan yanzu an gama kwashe ki,Dukan wasa na kai mata ina dariya nace zan ci uwarki wlh uban kwasheni akayi ki bari idan kinyi auren kyaji naki kalar, kwana nan zan fara zuwa gyaran jiki idan munyi hutun schl zan karbi kudi wajen Aayan Amma bazance gyaran jiki zanyi ba kar ma yayi tunanin shi zanwa ko sonsa nake,Meenat ta dinga dariya tace Sis wa zakiwa gyaran jikin to? Kyaji dashi can sai kizo nan ki tamana zancen da bashi kenan Ba can kuma da kinje ki zage ku sha love,oh karya nake miki kenan? Meenat tace to mu dai kiyi bacci dan Allah mun gaji da labarinki ke Sis sai za ayi bacci kice zaki bamu labari,ko tsakar dare ki tashe mu,

Nace Meenat kinfa rainani wlh tam,ai kuwa sunyi Baccinsu wurin 12 na kasa bacci sabo da tunanin Aayan Yamin yawa sai juyi nake ina tunano yanda muke murza juna ina murmushi ni kadai, na tuna da abinda nake so muyi shawara da Meenat Aiko ba bata lokaci na juya jikin Meenat dake shakar bacci nace Meenat ina girgizata tsaki ta ja  tana sosa gefen kunne,nace Meenat ki tashi mana na daka mata duka ta mike a firgice, nace mantawa nayi ban fada miki ba wai don Allah rannan kika ce kinga alamar Aayan kamar yana so na?

    Wani takaici ya kashe Meenat tace yanzu akan wannan zaki tasheni kusan karfe dayan dare?Nace ae gwara na kara jin gaskiya,cikin magagin bacci Meenat tace baya Sonki ko kadan,yaaaa tsaneki ne Sis kin kasa ganewa bakya birgeshi ko kadan ta koma ta kwanta sai baccinta takeyi,ni kuwa gaba daya naji duniyar ta kife min.

    Nan danan zazzabi ya fara kamani me zafi ga bakin ciki Meenat ta gano Aayan baya sona bana birgeshi,nan nayi tunanin yes gaskiya ne tunda ko yabo na ba yayi bai cewa ina da kyau na hadu,wannan ya nuna ya tsaneni sosai ne kawai sai na fashe da kuka na dinga yi da karfi a saman Bed cikin bargo,duk na hana Ma'eesha da Meenat bacci da Kukana sai ma kara karfinsa da nayi,sai tsaki sukeyi suna juyi su fa sam basa kaunar bacci tare dani dama tun Asali tun Ammah na da rai Sabo da tashinsu nake na hanasu bacci,lokacin ina Sana'a a gida tare da da Ammah cikin dare zan tashe su nace sai munyi lissafin kudi ko na fara basu labarin ya za ayi a tara kudi,ko tattali,idan kuwa nayi Sana'a banci riba ba ko jarin ya karye to fa sunga ta kansu kwana zanyi ina kuka a kan gadon mu,Ammah watarana sai ta jawo sandarta ta kwandala min sannan nake shuru dan ni bacci bai dameni da yawa ba,na riga na saba da jarabar neman kudi ban fiye bacci me yawan gaske ba.

   Suna jina kalar Kukan da nake harda me jiniyar motar yan kwana kwana,Meenat tasa Hijab ta fice har saman Aayan dan ita ta manta ma tace Aayan bai sona,cikin magagi ta fada min,knocking tayiwa Aayan ya zata nice sai yaji muryar Meenat,a firgice ya bude tunaninsa wani abu ne ya sameni tace wlh Yaya mudai kazo ka tafi da ita ta damemu wlh sai kuka take ta hana mu bacci,ko ka canja mata dakinta ita kadai mu takura mana takeyi,me ya sameta? Ba komai mu bamu sani ba dama haka takeyi ko a gida idan ta fadi a Business ko jarinta ya karye to sai ta kwana tana uban kuka har sai tayi Zazzabi,Aayan yace akan kudin? Meenat tace sosai ma watarana akan Naira darinta ta fadi a kasuwa sai da ta kwana tana kuka karshe sai da aka mata Allurar zazzabi Sabo da kuka,Duk daren nan sai da Aayan ya dinga dariya,Meenat tace ranar da jarin Awarar ta ya karye aka rasa dubu daya mun zata wlh ta samu tabin kwakwalwa,ni dai kaje dan Allah ka daukota a can ta damemu mu,maeesha ma tana zaune ba bacci kuma gobe muna da Test a schl.

   Meenat na gaba Aayan yana bayanta suka je har Bedroom din yanda nake haka nake ta barka kuka na,muryar Aayan dana ji ce tasa na kara ci gaba da kuka na yafi na da karfi ma,na cukwikwiye kaina a bargo ga uban gumi na hada,yace ke mene haka? Amma anyi girman banza babba dake to wa zai wa wani fada kenan? Na dauka ma lallashina yazo ya lallabani mu tafi dakinsa sai kawai naji ya rufe ni da bala'i, Kamar me Aljanu na dinga shure shure a Cikin bargon na kara ci gaba da kuka na,ina wayyo Marainiya ni,Zan mutu, Meenat tace baza fa tayi shuru ba wlh sai a kwana a haka da ita gwara ka dauketa kuje can in yaso ko zaneta ma kayi mu muyi baccin mu,Maeesha tace wai me akayi mata ne tana dariya tace wlh sis Mufee baza ta girma ba ko ni na fita wannan kuka dama ta saba abinta,Aayan yace Dan kune kawai zata hanaku bacci Amma da Bazan kalleta ba ta shekara tanayi,Meenat tace dan Allah ka rufa mana asiri ka dauketa muyi bacci,Aayan ya fara kokarin janye bargon dana ke ciki yana tsaki nace wlh tunda yayi tsaki Bazan je ba a barni nayi Kuka na,da karfi ya fisge bargon ya hau saman Bed din yanda nake kwacewa ina burburwa hannayena ya rike biyu na kasa motsi sai Kukana nake harda hawaye kwara kwara,ya samu bakina yasa yatsun hannunsa dan mugunta ya dinga dalla masa yatsansa kamar Harbin kunama ba shiri nayi shuru,tashi mu tafi yace, nace Bazan je ba,ai kuwa ya make min baki naji zafi ba shiri nace zanje wlh kayi hakuri,meenat sai dariya suke ya figeni yana jana fii yace kusha baccinku yau zata gane kurenta,Meenat ta rufe kofa tace wanne zata gane kurenta wai mu za awa wayo kuje dai ku sha iskancinku kuyi luf abinda shi kanshi kasa bacci yayi dama hakan yake so na ganeku.

   Ai kuwa kamar Meenat ta sani yana kaini Bedroom ya fara masifa yana min fada ke baki san kina shiga hakkinsu ba? Ba kyau takura rayuwar wani Yara suna so suyi bacci kuma a gabansu kannenki kike musu kuka,ai ba su akewa ba matan aure me gida sukewa kuka ba wani ba,idan shagwabarki kikeji kizo kiyi min ni zan dauketa ba su ba,nace to ni me nayi abinda fushi kake dani, yace ba dole nayi fushi ba muna Business dinmu kinzo kince Ameer yana da kyau ke yanzu zaki ji dadi nace Meenat ce me kyau ba ke ba,to ai nima sau nawa kace Meenat ta fini,wannan ai cin fuska ne,to ki kiyaye yanzu duk kinsa ma na fasa baki kudin Business sai an sake sabo,nima dadi naji zan masa wayo naji dadina nace to a sake sabon mana wa yake jin tsoro tunda kudi zan samu sai na samu wanda yafi na da ma.

   A ransa yace lallai Mufeeda yarinya ce yanzu ta yarda,nima a raina nace dadi a banza kuma a bani kudi nice da riba ka hadu da ni,Muryarsa naji yace to yanzu duk kukanki da shagwabarki Maza sauketa a kaina ki samu kudi kuwa da yawa yarinya,Nace ai ba sai kace ba yanzu zan nemo hanyar arzikina mota,gida da kasar waje ko da kafar katako,jikinsa ya jawoni muka fada saman Bed ba kunya na fara kuka na irin na dazu,shi kuwa lallabani ya farayi yana mene ne Pretty na? Na koma shagwaba kala kala yana biye min tare da fara sarrafani,a raina nace da haka kawai ina can zanyi kwanan kunci tunda hakane Meenat na gano yanda zan dinga baki aiki idan ta baci,Aayan kuwa a ransa dadi yake ji marar misaltuwa yana godewa Meenat dama ya kasa bacci ko kadan ni kawai yake bukata.










AsmaBaffa
[1/19, 12:07 PM] Asmabaffa: 🌖🌖🌖🌖
🌖🌖🌖🌖

  KASUWANCI NA






         76-80






Official






By
AsmaBaffa




Ina mika dubun godiya ta gereku
MAMAN 2 KIDS
AUNTY SUMEE
MEENAL SIDI
MRS HAMZA
ADABIYA ISAH
SAMEERA AHMAD
JAMILA SULE
MAMAN MEENAT

    Sai manya manyana ina jinjina muku
MAMAN MEENAT
MUM SUHAIL
MAMAN HAIDAR
QUEENMERMU
MAMAN WALEEDA
JIDDER ZARIA
MARCYCOOL
PHERTIMARH
AUTA
FLOWER ina kike kwana biyu Allah yasa lfy?
BIBA
HEENDU
HUMAIRAH





Page naki ne AYSHATABDULLAHI Me hadarin Sharhi na gode.👍😍






        Kwance nake a jikinsa na lafe luf muna huce gajiyar harkoki da muka kwasa,kin taba soyayya Ne Mufeeda? Naji muryarsa yana tambayata,wow yanda ya furta Mufeeda kamar wasu Aljanu ne suka fada Sabo da dadin sunan ba a cewa komai, kamar gaske nace ae na taba yi,gabansa ya fadi sosai ya shiga damuwa har kishi ya cika shi ya daure yace da wa? KUDI nace ina na san wani so ni ban san komai ba ai ni imani na kudi,ni kudi ne masoyina,Dariya yayi a ransa yasan ban san ma kudin ba ban san dadinsu ba Amma ina kirarin nasan kudi,a fili kuwa yace yanzu idan na baki million daya a hannunki me zakiyi da ita? Yanzu duk kuna ci kuna sha da Sutura ga schl baku da matsala da ita,ta ya zaki kashe million daya fada min naji? Kwanciya ta na gyara a jikinsa tare da fadawa tunanin ta yanda zan kashe kudin da ya fada,na gama tunani na nace na dinga cin kayan dadi,na fantama na Sa kaya irin na matan shugaban kasa,na dinga zuwa wajen da ake gasa kaji ina ci,na siyi fili kato,da mota,dariya yayi yace to kuna da motar hawa duk wacce kuke so akwai,me kike so kici wanda babu a gidan nan?Sannan kuna cin na wajen ma ai ko? Ae to ni dai ina so ace nima ina da nawa na kaina ba na wani ba,sabo dame?kayan mijinki ai naki ne, a'a ba nawa bane kafin a baka ma sai kayi yar murya,ko kuma a dinga bata rai ko kasa mutum ke ebowa ya baka watarana sai ya gaji,sannan Maza dan suna ma abu sai suyi ta juya ka ana ma kallon wata shatara, matan Hausawa kenan kike nufi duk abinda yasa suke karatu da aikin Gomnati don kawai su samu kudi ba sai sun saurari na mijinsu ba,kuma most of them badan Allah suke so su samu kudin ba kawai biyayya ce basa so suyiwa mijinsu shi yasa suke neman kudin, ya fita kin fita,bai Isa ya saki kiyi ba,wani ma in kudinta yafi na namiji zai sha wulakanci dole shi zai kwantar da kai yana mata biyayya.

    Nace hakane ko Ilmi macen tafi namiji sai kaga ko kudin albashi ya dauka ita zai kawowa sai yanda tayi dashi,shi yasa Maza suke tsoron auren macen da ta fisu Ilmi ko ta fisu albashi,sabo da matan Hausawa basu iya samu ba,mace daga tana daukan dan Salary sai kuga ta fara wulakanci kowa taka shi takeyi ita me kudi,dan Allah mata mu gyara halayen mu,wasu gidansu kaje da kyar suke kallonka ma bare mutunci ya hadaku Sabo da tana daukan Salary,mazan sam basa jin dadinsu,ga jarabar son kudi da neman kudi aje nan aje nan ba hutu ba lokacin me gida kuma bai Isa yace komai ba tafi karfinsa sai abinda taga dama,idan ma kishiya zaiyi cewa zatayi ya kara me ya dameni suje can su karata da kudina me nake nema a wajensa ko Sakina yayi zan iya rike kaina da Yara na,abin haushin kuma da zasu rabu sai aga ta koma bin Maza kanana tana kashe musu kudin da ta kasa taimakon mijinta dasu.

    Mun dade muna hirarmu dashi yana wasa da dukiyar fulanina wani dadi na shigata na juyo ina facing dinsa tare da kara shigewa jikinsa,yace ya dai? Wani sonsa nakeji yana ratsani ta ko wacce gaba dake jikina,baki nasa ina lashe lips dinsa kamar mayya nan ma haka muka kara birkita kanmu mun dade muna farantawa juna rai,ni kam yanzu son Aayan ya gama ragargaza min zuciya,kwakwaran numfashi banayi sai da tunaninsa,komai nasa birgeni yakeyi,ji nake kamar a hademu na zauna cikin jikinsa har abada abin fa ya wuce gona da iri yanda nake jin son Aayan ya zarta hankali har mamaki nakeyi,bani da burin da ya wuce na ganni tare dashi ina jikinsa,kallon Aayan kadai idan ina yi a Cikin gidan gaba daya sai naji dadi da sanyi marar misaltuwa,nayiwa zuciyata fada abin yaci tura,ko schl naje ba komai nake ganewa ba kawai tunanin Aayan yafiye min komai a duniya.
     Kwanaki sun dan ja,Ameer ko yaushe yana part dinmu kusan kullum sai yazo,a nan yake cin lunch da Dinner haka kullum suke fada da Meenat,Ma'eesha ce kawarsa kullum suna tare suna danna waya da jin wakoki aikinsu kenan, Meenat bata da time yanzu karatun waec da Neco sukeyi,Ma'eesha kuwa za a shiga Ss1 kwana nan,ni kuma ina ss1 going to 2 Sabo da ya tsallakemin jss3 ban karasa ba aka sani a ss1 shi yasa Amma da Ma'eesha ma ta fini class.
   Ma'eesha ta zama yan mata Sabo da kansu daya da Meenat kusan ma tafi Meenat girma ta kamoni Sabo da dama tana da saurin girma tsayin kafa tayi sai ka rantse ma ba Meenat ce yayarta ba,Sabo da zama da suke yawan yi da Ameer Ma'eesha har ta fara son Ameer sosai Amma boyewa takeyi dan kar mu gane sai dai kullum bata da zance sai Na Ameer.
    Kudi masu yawa Aayan ya bamu muje mu sake uniform tare da schl bags da takalma amma sai yace yasan idan nice me araha zan siyo mu tafi tare da su Meenat Driver ya kaimu.

     Muna mota Driver zai kaimu store nace canja hanya Baba ka kaimu Kasuwar kofar Wambai yafi araha,Meenat tace wlh mu store za a kaimu masu tsada yace a siya mana,Baki na make mata tayi shuru,ya kaimu Kofar Wambai muna gaban table din masu takalma ina ta zabga cikiniki yaki daidaita,na daga wani baki nace nawa wannan Malam? Dubu uku yace,a garin ina za a siyi wannan dubu uku Malam Dubu daya da Dari biyar idan ka siyar, Ma'eesha ce ta matsa gefe tare da kiran Aayan a waya Hello Yaya taki kaimu store wlh muna kasuwar Kofar Wambai kuma a kasuwar ma table din masu araha wai dan Dubu daya da Dari biyar kuma suna ta Surutu da masu saida kayan dan Allah da aurenta fa Yaya.
    Mata masu zuwa kasuwa a zauna ayi ta Surutu da masu saida kaya,da aurenki zaka ga wasu har canja murya suke suna lankwasheta abinda basa yiwa mazajensu sai siyiwa yan kasuwa sabo da suna neman a rage musu ayi musu araha su siya a banza.

   Aayan kuwa kishi ne ya sokeshi da bacin rai wai yacewa yarinyar nan  suje Mall amma ta kaisu kasuwa cikin maza ana ta cakudewa yanzu haka ma wani ya gogar masa jikin matarsa nan take bai San sanda ya shiga mota ba ya bar Office driver ya ja suka tafi,a hanya ya kira Ma'eesha ta fada masa inda suke minti kadan sai ga Aayan ya danna musu Horn tare da sauke glass.
    Ina ganinsa hankalina ya tashi na rude ko ta kan me kaya banbi ba nayi sauri na isa motar mu na fada ciki,Meenat da Ma'eesha suka shiga bayan mota kusa da Aayan da Kansa ya kaisu Shopping ya siya musu wanda suke so masu tsadar gaske komai har ni ma suka siya min nawa,ni kuwa tuni nasa Baba Driver ya maidani gida.
     Da suka dawo da kyar na fito palo,Ranar da dare nasha warning wajen Aayan sai da ya min ba dadi ina bashi hakuri.

    Anyi mana hutun schl Meenat tana zana waec da Neco dinta,yau Sunday muna zaune a palo ina yankewa Aayan Farce,Ma'eesha na karatu a wayarta da Ameer ya siya mata me kyau,Meenat kuwa abinci take ci dawowarta daga schl kenan yamma lisss,wayar Aayan ce ta fara ruri,da hannuna na daga kiran naga ansa Bobo nasan Yarima ne na kara masa a kunne yace Hey frnd  ya kk,Yarima yace gani a gidanku fa bude min kofa, Ma'eesha yayiwa magana yace budewa Yarima kofa Angel dama haka yake cewa Ma'eesha,Meenat kuma yace mata Preety, ni kuma daga ke shike nan sai ta mugun baci zai ce Mufeeda ina takaicin wannan abun da yake min Amma ya na iya tunda ni ba a sona.

     Ma'eesha na bude kofa Yarima yayi arba da ita wow ya furta a ransa da gani ba sai an fada ba yasan ma kanwar matar Aayan ce Sabo da kama da muke kawai haske zan fisu kadan shima idan baka sanni sosai ba baza kace na fisu haske ba,ba wani me yawa bane,Maeesha akwai fara'a ta gaisheshi tana murmushi sai kallonta yake ta gama Tafiya da Imaninsa gaba daya, bashi da burin auren yarinya karama Amma akan wannan kuwa sai dai a mutu, da sallama dauke a bakinsa ya shigo,Gaskiya Yarima ya hadu Chocolate ne me haske karshen kyau yana da shi dan fulanin Asali ne,ga wanka iya wanka dama duk irin abokan su Aayan ai haka suke basa muamula da garori, Ma'eesha kuwa kunya ma taji irin yanda ya mata Kwarjini gashi ya hadu sai kuma irin kallon da yake mata.
    Yana zuwa ya mikawa Aayan hannu suka tafa shegen gari kwana biyu Aayan ko Saudiyya banga kaje Umrah ba last wk ina can ina ta jiranka kace zaka je har na dawo bamu hadu ba,Tabe baki Aayan yayi tare da cewa gwauro shike yawo lokacin da yaga dama,dariya Yarima yayi lallai Aayan ka canja,juyawa nayi muka gaisa dashi a mutunce yana tsokanata da Abokinsa yayi kiba ya kara kyau me nake bashi ne,Meenat kawo masa ruwa,Kallon wacce aka kira da Meenat yayi tana can Dining tana cin abincinta da alama bata San anyi bako ba,Yarima a ransa yace su wannan gaba daya kama sukeyi da juna amma Ma'eesha irin muryata ce da ita sak,Meenat ce muryarta tafi tamu siranta sabo da iyayinta ta maidata siririya,kayan sanyi ta kawo masa iri iri kana ta gaisheshi a ladafce ya amsa tare da cewa Mufeeda wannan duk kannenki ne? Ae mana wannan Ma'eesha wannan Meenat,yace ke kuma Mufeeda triple M kenan yeah Ma'eesha ta amsa muna dariya,Meenat yan mata uwar iyayi tana ji da yan matan ci sai girman kan tsiya watarana kamar wata yar sarki aka take komawa magana ma sai taga dama,watarana kuma ta zage ayi da ita,Muna zaune ana hira sai ga Ameer ya shugo an ci wanka yazo dan ya birgeni ni Mufeeda wacce ban san me yake bama,Maeesha har taji sanyi data ganshi kusa da ita ya zauna ta gaisar dashi,Yarima ya fara kishin Ameer ya zauna kusa da Ma'eesha kuma yaga Ma'eesha sai wani Fara'a take masa sun fara surutunsu da alama sun saba da juna,s hi kuwa Ameer gaba daya Hankalinsa na kaina yanda na hade cikin Lace riga da skert ba karamin kyau nayi ba,abinda ya bashi haushi ganin ina yankewa Aayan farce gashi kuma kafafun Aayan gaba daya saman cinyata ya dorasu yana kwance dan naji dadin yanke masa farcen.

    Muna zaune daf da Magrib wata yar aiki ta shigo wai Meenat tazo tayi bako,Meenat tace ita bata da bako baza taje ba,tun kafin ta fara magana Ameer ya fara dariya,haka Aayan ma,nima na gane me suke nufi ko irin su Kwaja ne suka zo,Yarima yace mene haka daga ana kiran yarinya zaku fara mata dariya bai dace ba,Yar aikin tace a wata fyallelliyar mota yazo Hajiya da gani dan wanine,Nace mu ai bamu damu da wani me mota ba ko talakane indai yana da aikin yi,halaye masu kyau to alhmdllh zamu bashi ba wani sai me mota ko kudi etc,Aayan yace Pretty jeki kiji idan Bai miki ba ki dawo,kawai sabo da Aayan ne yace shi yasa ta figi Hijab tana fushi zata fita,nace ba kwalliya haka za a je? Kallona tayi kamar zatayi kuka ta fita abinta haka, taga mota iya mota tana jira taga wani Handsome ya fito sai taga Fela Gala da gani ba motarsa bace arota yayi, fitowa yayi tare da tsayawa yasa Hannu a aljihu harda Harde kafafu ya basar a jikin mota sai yanzu ma ta gane Ashe Motar tana ganin su Haneefa a cikinta,wato sune suka bashi aro azo a raina mata hankali.

   Ko saurarar Fela batayi ba tayi gaba abinta sai gata ta shugo kamar zata fashe tana wa Aayan magana dan Allah Yaya ka ganshi can ya biyo ni har gida wlh dan Allah ka koreshi sune suka kara turoshi, Ma'eesha tace Fela Gala ne wlh tun daga sunan Yarima shima ya fara dariya bai Sha dariya ba sai da ya leka ya ganewa idonsa harda rike ciki sabo da dariya,Ameer kuwa ba a magana,Aayan ne ya fita ba shiri yayiwa Nasuru fata fata da gudu ya fice daga gidan ya bar motar dama ta gidan ce.
   Meenat ta kalli Ameer tare da zuba masa Harara ta wuce Bedroom ta barsu suna bawa Yarima labari duk kwalliya da iyayin Meenat irin su Nasuru Fela ke zuwa wajenta,Yarima ya kalli Ma'eesha tare da cewa to ke yar ficika wanne kala ne naki? Dariya sukayi Sabo da Fela Gala ne yace mata Yar ficika,Maeesha tace ni yarinya ce ba yanzu ba,wani dadi Yarima yaji a ransa,Maeesha kuwa a ranta cewa take insha'allah Ameer ne ma,Shi ko Ameer tunani ma yake yaushene zai mallaki Mufeedansa,Ni kuwa ina nan zuciyata dankare take da son Mijina Aayan wanda naga Sam bai damu dani ba.
    Sallah sukaje masallaci har Isha basu dawo ba,lokacin na tattara su Meenat muna kitchen muna karasa abincin da muke,suna dawowa na fito da ludayi a hannuna ni ga uwar girki na manta ma da Ludayin juya miyar na fito,Ameer yace ina zaki abun miya kuma? Nace na manta sauri nake nasan Babyna yanzu wanka zaiyi,Ameer nan take mood dinsa ya canja amma ni ban gane ba nace bari ka gani na koma kitchen na ajiye ludayin na fito naji muryar Ameer yace mu dai ki koma ki karasa mana abincinmu yaran nan jagwalgwalo zasuyi mana,murmushi nayi nace sun iya sosai ba matsala,ya kara magana pls Aunty kije ki karasa da kanki,nufin Ameer dan kar naje wajen Aayan shine ya hada min wayo wanda ban sani ba ni kuma sai na koma kitchen din,n a tayasu muka karasa komai na barsu su gyara kitchen tare da shirya Dining,dana fito nace Ameer ina Aayan fa? Baki ya tabe yace suna wancen palon shi da Yarima,palon da ya fada min na nufa

    Direct naje shiga palon naki muryar Aayan yana cewa kyaleta ai wahalar da kanta takeyi bari nayi ta gama shiga hannu zata ga wulakanci,sai suka tafa da Yarima,nan take naji jikina ya dauki rawar sanyi,tsoro da fargaba tare da bakin ciki ya dirar min,ban san wa suke nufi ba,ban san akan me suke maganar ba sai na fassara maganar da naji kawai ba bincike ban tsaya naji dalili ba ko da wa yake nufi kawai sai na yanke hukunci cewar ni suke nufi dani suke,wato ni ya gano ina sonsa wahalar da kaina nakeyi,ya bari na shugo hannu ya wulakantani,ni zai wulakanta ma tab lallai dan Adam,duk abinda nakeyi Ashe baya gani a banza sai ma mugunta da yake hada min,nan take na fara tunano tun farkon haduwarmu irin tsanar da ya nuna min,Ammah ta da suka kashe min tunda sune suka jawo duk so yasa na manta,har aurenmu irin abinda ya dinga min a farko na wulakanci ina ta binsa,so yasa na manne masa nake kai kaina har dakinsa na sakar masa jiki,nasa yaji dadi,na godewa Allah da yasa ba ayi sex ba.
    Mata da dama suna irin wannan daga jin magana bata kai ta kawo ba,basu san ma akan me akeyin ta ba,amma da yake kullum a zargin mazajensu suke irin ko sun daina sonsu,ko suna kula wata,musamman ace suna da kishiya ko zai kara aure,ko wani dalili yasa dai taga mijin ya dan canja to zargi zata kasance a ciki iri iri,komai yayi laifi ne a wajenta,magana idan ta ji ko da abokinsa sai ta fassarata ta koma tashin hankali Babba,wata ma har abokin zata daina kulawa,ko ta masa rashin mutunci,miji na neman aure abokin dole shine a gaba wai dan me zaiyi nan fa zata kulla masa wata ma sai ta rabasu sun bata sun daina abotar,wata kuma duk abokansa ta daina kulawa ko ta ci musu mutunci wai sune suke zuga mijinta,duk da cewa ana samun masu hakan amma mata mu daure mu daina zargi tare da saurin yanke hukunci,ko magana akayi sai a dinga fassara ta bai bai sabo da ba a son zaman lfy.

     Ni dai ina tsaye naji kamar ma zazzabi zan fara sabo da yanda nake son Aayan ko kaina ban so haka,bani da burin da ya wuce naga ya soni back amma sai gashi abinda naji ma daga bakinsa,Hawaye na share na daure na shiga palon fuskata ba walwala nayi Sallama suka amsa,Nan take Aayan ya kafeni da idonsa yana ganin yanda lokaci kadan na fita daga hayyacina,dazu lfy lfy muke,kamar ma kuka nayi,ganin yana kallona nayi kasa da kaina,tunaninsa ko yan gidansu ne suka yi min rashin mutunci ya tabbatar idan kuwa sune suka sa na dawo haka yau sai anyi yaki a gidan nan,baya son a taba masa ni yanzu ko kadan, kasa jurewa yayi yace ina zuwa Yarima yaja hannuna mukayi waje dashi muna fitowa a jikin kofar yasa yatsansa tare da dago da fuskata yana kallona sannan a hankali yace lfy? Me akayi miki? Nayi shuru,Hajja ce? Su Haneefa nan ma shuru sai Hawaye dake biyo min a kumatuna a raina ina kara cewa yanzu wannan zankadeden rabuwa zaiyi dani,shike nan baya sona? Yace am asking u me suka miki ya fada da tsawa,duk ya shiga damuwa lokaci guda ya rude Allah sarki So,so banza ne kawai sai ya bani tausayi kuma na batawa wanda nake so rai,har bana ganin laifinsa sai nawa sabo da Aayan baya laifi a wajena so hana ganin laifi,tunowa da maganarsu dana jine yasa na kara birkicewa,kawai nace ni ba wanda ya min komai kawai ji nayi bana son auren Kasuwancin nan ko nawa zan samu,ko yanke talauci ne wlh bana sonsa dan Allah ka sakeni na tafi, wani dum yaji maganar a bazata to ko dai itama sun mata wani asirin ne ko kuma sun sa mata wani abu taci ai ko wlh bazai iya sakinta ba har abada sai dai duk inda zata je da aurensa,jikin Bango ya Dafe kawai yayi shuru yana Innalillahi kawai yake maimaitawa duk zarginsa tunaninsa Su Hajja ne ko asiri ko kuma wani abu suka mata wanda baza ta iya zama ba, da kyar ya dago muka hada Ido sai da na rumtse Idona yanda bazan iya kallonsa ba ya Zama wani iri idonsa yayi jajir,Hannu na ya figa kamar zai tashi sama ya jani muka Haura samansa har Bedroom ni dai kawai binsa nakeyi,a ciki ya tsaya tare da rike kugunsa da hannu biyu kansa ya daga sama yana danne lips dinsa na kasa da Hakoransa yama rasa ta ina zai fara, maganarsa naji a hankali yace Mufeeda! na kalleshi tare da sadda kaina kasa,yace ki fada min me ya faru dake me kike ji me yake damunki ko kuma a gidan ne wasu suka ce miki wani abu ni dai nasan ban miki komai ba,ko kema sabo da bamuyi Xxx ba zaki tafi? Da sauri nace a'a wlh ba haka bane,yana kallona yace to ko bana Haihuwa kike nufi? Nan ma kafin ya rufe baki nace wlh ba wannan bane,to mene tell me,karki rufeni ko ki cuci kanki just tell me what's is going on? Ina Hawayena nace ni kawai na gaji da auren ne Bana son kudin yanzu,Wait bafa Business muke ba wannan wasa ne kema kin san aure ne na sunna aka yishi ba wai akan kudi ba,nace ae na sani kawai bana son auren ne nace ma ni bazan zauna ba kawai,ok yace ko gidan nan ne bakya so? Fada min sai na Canja muku gida,kai na girgiza a'a, yace ko Wacce kasa kike so fada min wlh zamu koma can indai kina so,a raina nace jibeshi kamar gaske salon ya kara mallake min zuciya yaji dadin wulakantani da kyau to bazan je ba,nace bazanje ba ni a fili,Abuja fa?nace ko villa ne banso,to kiyi Hakuri idan wani abu aka yi miki addua akeyi akan komai ba fushi ba haba yan mata nan ya dinga lallashina,sai nayi kamar zan Yarda naji tausayinsa sai kuma na fasa nace nifa bazan zauna ba.

   Yana gajiya ya tamke fuska ba mutunci yanda na sanshi tun farko,nan take naji tsoronsa jikina ya fara rawa, tahowa yayi kamar zai makeni na fara ja da baya yana Huci yace bari kiji bude kannenki wallah kinji na rantse har uku bazan sakeki ba kuma ba inda zakije idan kika fita ma ko gate ne bada izinina ba sai munyi Shari'a dake a gaban Allah ban yafe miki ba,kiji ni da kyau ba wani Business auren za ayi as from today ni kuma duk Hakkin ki daga yau zan fara baki,yana gama fadin haka ya kwanta a saman Bed yana Dafe kansa dake Sarawa, tausayi kuma ya bani sosai yanda ya nuna ya damu a kaina gaba daya sai na tsani kaina me yasa nayi haka,amma dai zuciyata ta hanani na hakura,ido ya rufe sosai still yana Dafe da kansa ya rike sosai da alama ciwo yake masa da yawa,Hankalina ya tashi nima,mikewa yayi tsaye kamar wanda yasha giya yana maye da tangadi,haba ban san sanda tausayinsa ya gama rufeni ba gaba daya naga ya fini shiga damuwa yazo ya ratsa ta gefen zai wuce ya fita tuni na damko hannunsa ya tsaya cak tare da juyo da fuskarsa ya kalleni gabansa na koma tare da fadawa jikinsa na rungumeshi kam kam sosai da sosai kamar za a kwace min shi, baiyi hugging dina back ba,da kaina cikin kunnensa na rada masa Rug me back am so sorry, bai kulani ba babu zato naji bakinsa cikin nawa ya fara tsotsa ya rabani da kasa dan dagani yayi sama yanda tsayinmu zaizo dai dai ba sai yasha wahalar sunkuyoba,haka muke tsotse bakin juna kamar mun samu wani kayan dadi na tsotsa,wannan kiss din yafi na kullum dadi,gardi,tare da nishadi,yanda nakeji  ya zarce na fada muku,muna ta yi ba ji ba gani kamar zamu cinye kanmu ko nayi kamar zan kwace bakina sai ya kara rikeni kam ya hanani sai da muka dauki dogon zango a haka sannan da kyar na zare jikina daga nasa,amma duk da haka kara jawoni yayi jikinsa tare da fara lashe min wuya,tsigar jikina tashi take kawai gaba daya ya gama kara min sonsa a zuciyata, da kyar nake iya tsaiwa da kafaguna shima haka,ya fara kokarin cire min kaya na tuna yayi maganar hakki dazu da sauri na rike masa hannu tare da cewa abinci still dai ban saki raina ba bana wani nishadi kamar dazu,kyaleni shima yayi fuska ba walwala yace let's go,sai da muka saita kanmu sannan muka sauka kasa,Gaba dayansu Har Yarima da Ameer suna Dining suna ta cin abincinsu muka sakko duk kayanmu ya nuna da gani anyi yamutse yamutse,ga T-shirt din Aayan Fara kar ce duk jambakina red da Powder a jiki duk na shafa masa ba tare da mun sani ba sabo da murzar juna,Yarima da Ameer duk sun gane me akayi,Meenat ma ta gane gani ba jambaki a bakina sannan duk ga wani nan a bata gefen bakina,Aayan harda digon jambakin a hancinsa duk sai yanzu ma muka kula da hakan,Yarima sai dariya yake kunshewa yana kallon Aayan, dan Iska wlh zaka bar gidan nan banza munafiki Cewar Aayan,Yarima yace to me nayi kuma? Bayan ka shanyani,Ameer kishi ya hanashi kallon kowa kawai tura abincinsa yakeyi,Aayan har yau yana cikin damuwa ya kasa cin abincin kuma yunwa yake ji,ni kuwa bakin ciki baya hanani cin abinci ko cuta nake sai naci na koshi haka nake bare kuma kafin naji Maganar da su Aayan sukeyi tun a kitchen muna girkin na cika tumbina, ganin ya kasa ci na Mike tare da Zama kujerar dake kusa da tashi zan bashi da kaina,kafin na fara Ameer ya ajiye spoon yace ina zuwa bari nayi waya ya fice da sauri zuwa part dinsu,Yarima yace nima tafiya zanyi Ma'eesha zo ki rakani mota nan yayi mana Sallama suka fita,Aayan yace sai nazo zanyi maganinka ya furta da alama kawai danne bacin ransa yakeyi,Meenat ma tuni tayi Bedroom zata fara karatu,daga ni sai shi ya Dafe kai tare da rafka tagumi da gani yana cikin damuwa me yawa.

     Hannun da yayi tagumi na janye a hankali ba tare da nace komai ba na ebo abincin a spoon na fara bashi da kaina yanda yake ci zaka San baya jin dadinsa ko kadan,kamar kurame haka muke har yace ya koshi nace ko spoon biyar baka ci ba fa? Zan fara masa magiya ya Mike kawai ya haura sama ya barni a nan,ban damu ba na tattara komai na kai kitchen tare da gyara komai na shiga Bedroom dinmu nayi wanka da duk wani abu da zanyi nayi nasa Night gown dina da kawata Sayyah ta bani wai inji mamanta kala Uku hadaddu amma basu fiye tsaraici ba nasa light blue din masha Allah nayi gaskiya karshe na daura ta samanta na fita lokacin Ma'eesha ta dawo daga wajen Yarima tana nuna min chocolate masu Uban yawa da kudi masu yawa wai a bani inji shi,na karba nayi godiya nace bari na nunawa Aayan kafin Ku fara sha nayi waje zuwa Bedroom dinsa,gefen Bed na hangoshi a zaune yayi shuru kawai yana kallon sama da alama tunani yakeyi yaji Sallama ta,amsamin yayi kawai tare da kwanciyarsa saman Bed ya barni a tsaye,banji dadi ba ni kaina muna zamanmu lfy na jawo bacin rai kuma shi dama kafin a lallasheshi aikine.

    Haneefa ce Zaune tare da Mommynsu suna hira,Mommy tace Ameer naga fa kamar kwanan nan ya Mannewa wajen yan iskan can a part dinsu ban san ko Hajja tasan labarin ba,Haneefa tace Mommy ki barshi ai da alama bata sani ba gwara ma da kika tuna min bari naje na fesa mata tayi maganinsa ya daina zuwa na tsani Su Mufeedan nan Shegu wai su masu kyau,Mommy baki ta tabe tare da cewa je ki sanarwa Hajja ni ma yau zan fadawa Abbi abin na Ameer yayi yawa, da sauri Haneefa ta tafi part din Hajja,ta samu Hajja sai Mulki take zubawa tana wani takama da isa tare da bawa yan aiki umarni.

     Haneefa ta zauna gefenta tare da cewa Hajja wani labari na kawo miki marar dadi so sad wlh abin kunya ma,Ina jinki Hajja ta furta tana gadara,Haneefa ta gyara Zama tare da sanarwa Hajja yanda Ameer ya koma bangarensu Mufeeda.
   Hajja da masifa tace to azukwi uwar munafunci me yasa kuke takurawa Ameeru ne,ina ruwanki Algunguma to nasan da zuwansa aikina yake ni na turashi,kinzo da guntun munafuncinki ai zai shigo ne zan fada masa me kika ce ya farfasa miki jiki,Haneefa ta fara bata hakuri daga fadar gaskiya sai a lullubeni da fada to daga yau bazan kara fada ba ko mene zai faru ya faru,Hajja ta dakko yar sandarta ta karfe tayi kan Haneefa da gudu ta fice ta bar Hajja na Masifa ta gaji da Gulmar Ameeru da akeyi a gidan nan.








AsmaBaffa
    Loves u all 😍
[1/20, 11:23 PM] Asmabaffa: 🌖🌖🌖🌖
🌖🌖🌖🌖

   KASUWANCI NA






           81-85







Official







By
AsmaBaffa






   


Page din yan TASKAR SURAYYARMS ne wannan ina jinjina.


   Gidiyata bazata irgu ba gareku Yan HOUSE OF HAUSA NOVELS
ASMABAFFA FANS CLUB
TASKAR FIRDAUSI SODANGI
UWARGIDA


Na gaisheku masu Sharhi a ci gaba.






        Hajja tana nan tayi gaho da baki tana sauraren Ameer yazo suyi maganar komawa wajen Malamai tunda yanzu taga ya shiga jikinmu sosai zai iya aikata komai,Abbi sai Haushin Hajja yake ji ta hanasu aikata nasu ita kuma ta kasa komai ta biyewa wani Ameer.

    Na dan Dade a tsaye ina tunanin me zance masa sai da na gaji nace gashi Yarima ya bamu,juyowa yayi yana daga kwancen,kudin na mika masa tare da bude masa ledar kayan zakin iri iri,a hankali yace ki basu kuje ya kyauta,To ka kirashi ka mishi godiya,Ba musu ya jawo faskekiyar wayarsa ya dannawa Yarima kira bugu biyu ya dauka suka fara suruntunsu na abokai naji Yarima yace to ya zamu shirya mata Plan din,Aayan yayi dariya tare da cewa ka bari sai mun hadu zanzo gobe ko jibi idan na samu time,ok anyway shaa cewar Yarima,Aayan yace dazu Ashe har wani wahala kayi na kudi da Sweets tnx, ban son Godiya Malam Good night I forget to tell u gobe Umma na zasu dawo tare da Abba, good to hear that sai nazo nayi missing girkin Umma tun muna London,Yarima yana dariyar Jin dadi yace ga matarka nan tafi ma Umma iyawa,Uhm gaskiya ne Night nan suka yi Sallama,ni kuwa na kuma jin ance ya plan dinmu a kanta nasan ma nice kawai na kara Jin haushi,Na kumbura kamar zan fashe da kuka,Kallo na yayi yaga yanda nayi a ransa yace to fa wannan na kasa gane meke kanta,ni kuwa Harda Haushin yace yayi missing girkin Babar Yarima wato nawa ni ba dadi bai dameshi ba har girkin wata yake tunawa yafi nawa ma wani haushi ya turnuke zuciyata naci gaba da tsaiwa a kansa rike da kudin tare da ledar kayan da Yarima ya bamu.

   Kallo na ya karayi yaga kamar zance na shiga uku na lalace na hada girar sama data kasa na cokalo lips gaba kadan nake jira kuma na tsaya masa a kai, light ya kashe ba tare da yace min komai ba nima ban motsa ba kamar me gadinsa haka nake tsaye gefen bed din, mun dauki lokaci a haka yaga dai ko matsawa naki yi nan ya kara kunna light haske ya mamaye dakin,inda nake haka nake, kallona ya sake kare min ni kuma tunani nakeyi ba a sona ni ban san tsakin da Naja ya fito fili ba,a fusace ya Mike tare da dirowa daga saman bed sai da na firgita,ban kara tsurewa ba sai da naga ya zaro wata wayar wuta doguwa ya nufo inda nake da gudu na watsar da kayan na fice da shegen gudun da rabon nayi irinsa tun ranar dana je guess house Hon Chairman neman tallafi.
   Dariya ma abin ya bashi dama gwadawa yayi yaga karshen rashin kunya, ban tsaya ba sai dai Su Meenat suka ji na banko musu kofa tare da fadawa Kansu,da gudu suka Mike daga baccinsu suka yi waje can Palo da gudu basuyi tunanin nice ba sabo da tunaninsu ai can nake kwana,Dariya suka bani na fito ina ce musu kai nice fa,Meenat ta manta ni yayarta ce sai da ta dura min ashar daga baya tace yi hakuri wlh na tsorata kin bani haushi muka dinga dariya Ma'eesha harda bige kafa da jikin Bed, ganinsu da kayan bacci nace ku koma Bedroom kar Aayan ya fito ya ganku a haka,Ko kunya kishinki yayi yawa cewar Ma'eesha,nace ae naji dai,suna shiga kafin na shiga suka banke kofarsu tare da Sa key wai sai daí na nemi wajen kwana.
    Ni kuma tsoro nakeji na kwana ni kadai ban saba ba,lallabawa nayi na koma dakin Aayan kamar munafuka ko wacce taje yin sata haka nake sanda kamar Soja ana kwanton yaki,a hankali na tura kofar dakin Allah ya taimakeni ya kashe light ya kwanta saman Bed Amma ba bacci yake ba tunani na yakeyi gaba daya ya kasa bacci yanzu na gama sangartashi tare muke bacci idan bana kusa matsala ce a gareshi kasa bacci yake.
    Lallabawa nayi yana tunaninsa baiji motsina ba har na hau saman Bed din gefe daya can na kwanta a hankali ina dauke numfashi na, nayi shuru kamar ansa wata na'ura me jawo ruhin mutum zuwa na dayan haka nakeji,gashi a kusa dani Na kasa sukuni burina na rungumeshi mu kwanta yanda muka saba,idan na taba shi kuma ina tsoro kar ya mike da fushi ya zaneni,Shi kuwa ya lula tunanina kamar yaje ya dakko ni,ji yake ma me yasa ya koreni gwara ai ina dakin ko banza ya dinga jin motsina.

    A hankali nake matsawa kamar ana jana ban san sanda zuciyata ta Gaza hakura ba,idan na matsa sau daya sai na huta dan kar yaji,ji yayi kamar abu na motsi a bayansa ya firgita shima,ya kara ji ana matsowa,Sandarewa yayi gaskiya aljanune suke shafar mutum a gidan nan,shima gashi sunzo masa,na kara zakudawa kamar tsutsa,a bin yaji yayi yawa kawai ya kunna Haske dal ya haske dakin,ni kuwa Sabo da tsoro har Hawaye ne ya zubo min nasan zanji jiki yau dukana zaiyi,waje daya na dunkule a saman Bed din,wani farin ciki ne ya mamaye masa zuciya Amma bai nuna ko Alama ba, ba tare da yace komai ba ya sauke ajiyar zuciya sannan ya kashe light again ya matsa can karshen Bed ya kwanta wai kar ma na taba masa jiki bayan yana so.
    Juye juye na farayi ina wash cikina wayyo,bai kulani ba har na gaji nace bani da lfy fa,ya min banza,nace da gaske nake fa,shuru nan ma,nace ba karya kasan bana karya fa,nan bai ce min komai ba,nace ita dai Duniya da ake ganinta ba matabbata bace,wa ya sani ma ko Bazan kai gobe ba,ko jibi ma ba lallai na rayu ba wa ya sani ma,yau in kaine gobe ba kaine ba,duk wannan abin watakila ma Baza mu kara yi ba a duniya,mene abin fushi da juna,ni ba cewa nayi sai an soni ba,ni bance ace ana sona ba,ai ba a so dole,maybe ma idan an fada din ba lallai ayi soyayyar ba mutuwa tazo ta riski mutum,ni dan anmin shuru ina ruwana bana gaba da mutum,kuma bana rike mutum a raina kamar zuciyar Fir'auna ni ba haka nake ba ana yi min abu nake mantawa na mai da komai ba komai ba Sabo da Duniya ai ba kanwata bace Meenat ko Ma'eesha bare ta daga min kafa,Ina maganata yana jina yana dariya a boye, muryarsa naji yace ina ruwana to sai me kuma,a raina nace iyye lallai ta tabbata baya so na na gama wannan tunatarwa ta mutuwa Amma ko a jikinsa nama mutu kenan,nace to in Allah ya yarda Bazan mutu ba sai naga Yayan jikokina da tattaba kunne idan an tsaneni a harbe ni,shuru ya min kamar bacci yakeyi,nace Hmm ba komai Watarana ana kallo a gidan nan zan shanye fiya fiya ko Blitch na wanke toilet,Yace ke kika huta da duniya mu ina ruwanmu, bakin ciki ya kamani nace Allah sai na ma yanke gashina,yace kinwa kanki ke zaki daina kyau ki koma Horror me ruwanmu,nace hmm za a gani ai dai ko Allah ya kaimu gobe,naji yace ga almakashi ma yanzu zan baki idan kina so, na rasa ma me zance nace to in ba tsoro ba ace na tafi gidanmu na bar gidan nan a gani,Dariya yake a ransa,muryarsa naji yace target nake hada miki first,nan take na tabbatarwa kaina maganar nan gaskiya ce ni ake hadawa plan shi da Yarima suna so suga bayana,ni kuma sonsa ya min yawa,ban sanda na fara kuka a hankali ba,Yaji da gaske Kukan kuwa nakeyi kuma da gaske ba na wasa bane wannan,Juyowa yayi ya kara juyawa tare da cewa Hawayenki ne zai kare ki koma na jini, ina shesheka nace da...dama...Hawaye na ka..rewa?Yace sosai ma sai Jini ya biyo baya.
   Da Sauri na goge hawayena na daina Kukan nace kar naje jinina ya fito,sai kuma Hawayen ya zubo na goge da Sauri ina ta gogewa yana zubowa na fara yaki tsayawa wayyo jinina na kara wani Kukan nace wlh yaki dainawa,yace shike nan anjima kadan sai Jini saukar min a Bed kar ki shafa min a Bed,na Tsorata da gaske,yace kai kamar ma jinin ne yanzu ai gashi nan ya fada yana kallon idona ina kukan Kar jinina ya fito ta ido,Ya zanyi ni na furta da muryar kuka,

yace badan halinki ba matso na hure miki yanzu Zai tsaya Hawayen kafin jini yazo,da Sauri na matsa jikinsa ya daurani a samansa sosai kamar shine katifar tawa,fuskata a saman tasa ya gwale min ido yana Hure min ido,ni kuma jina a jikinsa ban san ma hawayen ya tsaya ba tuni,sai nayi tunanin da gaske shine ya tsaida hawayen,yace to ya daina saukar min a jiki, nace kai dan Allah daga dan hawa, ki koma wajenki ko na rama nima,jin haka nace wayo zan ma a raina,na ki sauka kuwa sai ma kara gyara kwanciyata da nayi a kansa,shima wani dadi yakeji yana godewa Allah,amma sai ya nuna na takura masa sai na bar masa jiki,saman Bed ya maidani shi kuma ya haye min jiki kamar yanda nayi Amma bai sake min nauyinsa ba,tunani na nice na iya shanye nauyinsa,nace ashe ma baka da nauyi kalli yanda na iya daukanka, dan munafunci irin nasa sai yayi wani likimo yana ta faman mutsu mutsu a kaina yana jin dadinsa Amma wai sai yace a'a ni kin dameni sai mutsu mutsu kikeyi,nace Allah kaine kake motsawa,sai ya sa cinyarsa ko da hannunsa ta dabara ya girgiza min jiki sai yace ke mene haka wai baki da karfi sai wani sukur sukur kikeyi duk abinki sai na rama abinda kika min, nace wlh kaine kake motsi fa baka gani wai? Ba wani nan ni me zaisa na motsa, yasa hannu ta dabara ya zame min rigata kasa Amma sai ya dinga masifa ke abin naki har ya kai haka?to duk abinda zakiyi ko tsirara zakiyi Bazan hakura ba sai na rama, Allah kaine ka cire min ai ina jinka,nan ya dinga masifa wai ba shi bane nayi masa sharri ina ji ina gani sai shuru nayi masa,can naji ya bankaro min kirji tare da manneni a kirjinsa da Sauri nace ka gani ko gashi nan wlh Allah kaine nan kake matseni sai kace wani nice gashi na kamaka,dariya yakeyi a boye yace a'a kawai dai kice min kin lalace yanzu haka kuma kika koma yarinya dake Amma kina son dadi kema,nayi fushi tare da cewa yaushe nace ma ina so duk kabi ka makalkalemin jiki zaka ce nice,ki fadi gaskiya yarinya ya furta tare da cewa juya bayanki bana son yanda kike bankaro min kirji haka bari na karasa ramawa a bayanki Allah yasa naga kinmin wani abu kuma zaneki zanyi, Nan kuma ni har ga Allah dadin abinda yake min nakeji bana so ma a daina ko kadan,har haushinsa naji yace na juya baya a raina nace bari nima na kala masa sharri  kawai na masa wayo naji dadina.

   Na juya baya na tare da kifa cikina uban Hips da tudun mazaunai na kara yin sama dasu kamar zasu tashi sama🤣 Aayan dadi ya kamashi a ransa duk ya zauce ya birkice abin ya sha masa kai,Sai da yasa hannayensa ta kasan cikina ya rungumo dukiyar Fulanina,da Sauri na lumshe ido na Gaza gane a ina nake ma,maganar naji can sama kamar irin da nisa tsaka ninmu haka nake Jinta,yace me ya kawo wannan abubuwan hannuna kuma? Ko kulashi banyi ba lokacin maganarsa gida biyu nake Jinta,iri biyu take tashi a kunnena bana ganewa ni kamar na sha barasa shi kanshi gani nayi ya rabu gida wajen biyar ban san wanne Aayan na gaske ciki ba.

     Wasu irin abu yake min a bayana masu nauyi da Wuyar fassara mun gama fita daga hayyacinmu niko ban san sanda na zake ba na koma ina masa abubuwa masu nauyi mun manta inda muke ko wannenmu yana jiyar da dan uwansa dadi marar misaltuwa,mun rabu da kayan jikinmu kaf ba tare da mun sani ba,Aayan ya kai kololuwa yau yaji bazai iya jurewa ba ya kamata ace yau ya gwada babbar harka,a hankali da kyar ya iya magana cikin dishewar murya tana rawa yace Babyna ki yarda yau muyi pls mu gwada ko za a samu Baby mu Haifa,Haushi ya kamani wato dan a samu da ma za ayi badan yana so na ba,nan naji gaba daya na dawo hayyacina ban nuna naji Haushin maganarsa ba nasan halinsa da mugun zuciya sai nace a'a ni bana so yanzun nan kace nice nake takura ma ina taba ma jiki, yaushene zaki daina wannan kuruciyar taki?bakya ganewa wai? Ke fa Matata ce mene idan munyi ai abin jin dadi ne ma,ga lada kuma mu Haifi danmu,a raina nace wai bazai ce yana so na ba ni ban yarda da wannan ba kawai ya min ciki ya juya min baya,gwara yasan daraja ta tukun ni ban gama yarda dashi ba kuma naji me suke Plan a kaina Bazan yarda ba,da ace dai banji hirarsu ba to ko dan na faranta masa zan yarda ya gwada ko dan mu tantance lafiyarsa ta samu ko a'a, a fili nace a'a ni bana so daga auren Business ai kai kace banda wannan , dadin aure Bazan sani ba Amma yanzu kuma kace sai naji dadin ni bana so, cike da marairaicewa yace baki san Allah yana canja komai ba? Pls ki bari muyi,na makale kafadata kamar zanyi Kuka,so kike na mutu? Baki san yanda nake ji ba baki da Imani?Nace ae ni dama bani da Imani bani da tausayi haka nake ni haka Allah ya yoni, Ok to Hakkin auren fa? Kin san dai ba wani Kasuwanci a aure ko wasa a cikinsa da gaske akeyinsa Ki bari mu sauke wannan hakkin,ni dai a'a ban yarda ba,aure fa da kike gani ba haka kawai ake yinsa ba,Sai da Allah ya saka dokoki tare da ka'idoji sannan ya gindaya sharudai ba wai kawai abinda kaga dama zaka yi ba,dole abinda Allah yace shi za ayi ba wai ra'ayin mutum ake bi ba dokokin Allah ne,wanda yanzu musulmai abinda sukeyi kenan aure ba a yinsa yanda Allah yace tare da bin dokokin Allah sai kawai abinda naga dama shi zanyi,shima mijin abinda yaga dama zaiyi shi yasa auren baya karko,idan ma yayi karko sai kaga ma'auratan basa jin dadin auren sam Sai fada yau fari gobe baki,kullum cikin bacin rai,daga mutum yayi aure 1yr tayi yawa zaka ji ana Complain both Maza da matan,bakin cikin da suke sha yafi farin cikin yawa,me ya jawo wannan? Sabo da ba a bin abinda Allah yace,ba aiki da fadar Allah abinda kowa yaga dama yakeyi a gidan auren,ya kamata Alumma musulmai Maza da mata mu san me mukeyi a aure wlh ba haka kawai akeyi ba,sai da bin dokokin Allah  dake cikin tsarin aure Amma kowa sai ka rantse ma ba Allah ne ya tsara sharudai a Cikin aure ba yanda naga dama,ko yaga dama,ko taga dama shi mukeyi a daure a nemi sani sannan ayi aiki dashi sannan komai zai tafi dai dai.

     Haka Aayan ya dinga min nasiha da wa'azi akan me Allah ya tsara a zaman Aure,nasan gaskiya ne kuma nima na sani sannan ina da burin aikata komai Insha'allah Amma a wannan bangaren Bazan iya ba yanzu bayan ina kokonto akan Aayan ba wani so na yake ba,kuma haka ma zan yarda ba wani gyara etc nima wlh kamar yanda Amare masu gata sukeyi nima haka zanyi nan gaba da Izinin Allah,ba irin salon da bai billo min ba,tare da rokona har ma wa'azin naki yarda,nayi tunanin Zaiyi fushi ya daina kulani sai naji akasin haka yace sha zamanki na fita hakkinki Bazan miki dole ko na takura ki ba, Allah ya ganar dake gaskiya,Dariya nayi nace Ameen kayi hakuri dan Allah sai nan gaba,ba komai karki damu ci gaba da dariyarki yanzu na tabbatar da Imaninki kadan ne ashe da gaske ne?Dan Kar ma yayi tunanin zan ji tausayinsa na canja shawara sabo da kuruciya ban san a me zai kalleni ba da Sauri nace ai ni haka aka haifeni bani Da tausayi ko kadan,yace Allah?Nace Imani ko digo bani dashi ni ko me mutum zaiyi ba ruwana,ya gane dalilina na fadan haka Amma sai ya fuske yace uhmm lallai kice ke ko dan mutuncin nan babu,gani nake nifa na gama birgewa nace ko na digo banda shi ni ai kowa ya sanni ni akan mutunci ma ko a Unguwarmu ba a shedata,Aayan yace kin birgeni ai yafi hakan,ban san kawai biye min yayi ba yana ganina yarinya me kuruciya,  da yawa yanzu mata da Maza sunfi so a yabesu ba ta Kalma me dadi ba,basa ma so ace wance me hakuri ce,me mutunci,me hankali,ko wane Allah Sarki ba ruwansa da duniya etc, anfi so aji ana wance ai shegiya ce,wance bata ji ai bata da kunya,ko Wane Allah yayi shege anan,wane tsinanne ne, ai shegiya wance bata da mutunci tana birgeni,bata dagawa kowa kafa sai kaga a haka wai dadi ake ji har ana kara zakewa ana kara goga iya shege dan ayi suna a shedar banza, muyi kokari  mu samu shedar arziki ta kirki a ko ina muka shiga.

  Aayan a ransa shi yasan ba haka nake ba ina da Imani da tausayina sai yace to karasa ladanki karki gwada min halin wannan Lalatacciyar unguwar taku tunda baza ki bani Babban ba karasa min sauran yar Mufeen Ammah ,tausayinsa dama nake ta faman ji sosai sai da na zage na tsundumashi a nishadi tare da faranta masa yaji shi fes kuma inda yaji haushi yau ma ya kara Releasing a banza naki yarda ayi.

    A hankali ya rada min a ina kika iya abubuwa haka? Murmushi nayi tare da rufe ido na sabo da kunya,nace karantawa nakeyi a wani littafi Sai watarana zan fada ma,to Kunji Readers wani sirrin zamu ji inda Mufee ta iya abubuwa na birge me gida a Bed,Aayan kuwa kullum mamaki yake yanda akayi Mufeeda ta iya abubuwa haka wanda bashi ya koya mata ba,kuma bai nuna mata ba,gasu gingima gingima ba kowacce kwararriya ce ta iya irinsu ba,yanda kuma take iya sarrafa shi gata yarinya abin yana daure masa kai,yasan kuma matarsa bata san Namiji ba ko kiss a kansa ta sanshi,wasu ma suna da aure ko sun san Maza tun awaje Amma basu iya sarrafa namiji yadda yakamata ba,kuma ba updated bane su kullum abunda suka sani shike nan ba canji,ba a ci gaba da samo new zafafa ana juyawa me gida Brain,iya style dinki ya gama saninsa a daina bacci Hausawa a daina tsayawa ana ci baya kullum maimakon ayi gaba,a dage a nemi Ilmi akan komai,a san abubuwa wanda zaki garara a wajen megida,a daina kunya ana cutar kai, Aayan ya tabbatar Mufeeda ta gama dashi gani yake ma ko wata ya aura baza ta iya gigitashi haka ba,baza ta iya da shi ba sai Mufee yar yarinya me zukar Fura.
     Kara makalkaleni yayi yana shafa gashina har bacci ya kwashe mu me dadi da nauyi.

    Nina fara farkawa washe gari da Safe ban iya janye jikina a nasa ba sai a hankali na zauna kusa dashi ina karewa suffarsa hadaddiya kallo a raina ina Allah yayi baiwa a nan Bazan iya rabuwa da shi ba, wani sonsa ke kara ratsani ina kallon yanda jikinsa ke sheki,komai sumul lumi ban san sanda nace  a hankali Allah ya barmu tare ya sa maka sona kamar yanda nake sonka,sumarsa taci kudi me santsi da laushi na kalla tare da shafata a hankali na zare hannuna tare da jinjina kyai a raina nace Allah me baiwa.
    Ina zaune sai naga ya juya tare da shafo gefen da nake da Alama ni yake nema jin bana wajen ne yasa ya bude idonsa a hankali ya sauke su a kaina tar dasu,wani shock naji har raina da bargo na,Murmushi ya sakar min nima na maida masa tare da gyara rigata da na maida jikina,da hannu ya yafito ni wai na matso ba musu na matsa jikinsa, kissing din bakina ya fara,lokacin na tabbatar mun cika masu Tsabta wanda dole nayi respecting dinsa shima dole yayi respecting dina ta wajen tsafta a ko ina,sabo da sai mutum ya cika me Tsabta ta gasken gaske ne zai tashi daga baci kaji bakinsa bai canja ba babu wani wari ko wani canji,mata sai dai an dage mijinki yaji ko daga bacci kika tashi zai iya yin kissing dinki babu wani fargaba ko zai ji wani abu daban,zai kara girmamaki ya kara sonki yasan lallai kin hadu a Tsabta, a dinga shan abubuwa masu wanke dirty na ciki sannan Brush atleast sau biyu Safe dare,sai kuma ki siyi aswaki kina yi duk time din da kika ci wani abu ko haka kawai ma,Ana wanke Harshe da can ciki wajen makogwaro,Ana amfani da gawayi toothpaste tare da gishiri,ko toothpaste da lalle, Baking Powder da Lemon tsami sai toothpaste,kullum da Safe ki samu ruwa me zafi rau rau a hada da gishiri kina kuskure bakinki dashi, a tabbatar ana yawan cin Fruits,ko lemon tsami da zuma a zuba a ruwa me dan zafi ko dumi 1  cup kullum zai wanke miki dirty ciki ba ruwanki da wari ya fito daga cikinki,na baki kuma ga yanda zaki tsaftasheshi,a dage ana samun matsala ta nan mata.
   Shima idan bai sani ba bayayi a dinga ganar dashi cikin dabara,ki dinga bashi yana yi ta sigar dabara.

     Aayan yasan lallai yayi dacen mata me Tsabtar gaske ko ba turare a jikinki baza aji wani ordor a jikinki ba matukar kina tsafta yanda ya dace.
    Zamewa nayi daga jikinsa tare da cewa ko Brush banyi ba fa,to so what? Ya furta yana kallona kamar maye, Ni na fara shiga toilet Sabo da ya fini dadewa wajen wanka,wanka nayi tare da Brush na fito shi kuma ya shiga,mun kusa makara da Sauri na shirya tare da tayar da Sallah ina idarwa ya fito shima ya fara tasa,munyi azkhar sosai sannan na cire Hijab dina tare da busar da gashi na na gyara shi Neat na maida kayan bacci na,shima haka sai muka koma bacci.
     Ma'eesha ce ta shirya mana Breakfast,sai 11am na bar dakin Aayan na koma namu tare da sake sabon wanka na cakare cikin Shadda Dark Brown yar gaske dinkin zamani doguwar riga,Na kafe dauri kowa yasan na gama haduwa kamar Balarabiya,Meenat tana schl zana exam,Maeesha sai koda irin kyan danayi takeyi kamar wata Hajiya haka na fito na zauna a Dining ina jiran Aayan.
    Kamshi naji ya cika sashin ba tare da na juya ba nasan ma waye wani sanyin dadi naji a raina ban ma san Sanda na juya na kalleshi ba cikin 3qtr da riga yayi matukar bala'in kyan da ban ma sanshi dashi ba sai yau, Na kalleshi kamar nace kayi kyau sai na fasa kar ya rainani,Shima yana ta kallona da kyar kamar dole yace u look Good,tnx nace tare da fari da idona ina wani wanashi warrr,bai san sanda yayi dariya ba yace naga wannan,Na kara waresu na lumshesu,murmushi yayi tare da cewa wannan ma na karba, na kara juya idona suka kalli up and down,Nice One yace dariya nayi tare da rufe idona da tafin hannuna yace wannan ma ba laifi na kara kyalkyalewa da dariya tare da fara zuba masa abincin.

     Ameer ne gaban Hajja yana zaune tana tambayashi to Ameer yaushe zamu je ne wajen malaman karfa muyi sakaci,dan karta gane yace ah Hajja ai na gama shiga jikinsu ni dama Umarninki nake jira muje kawai Saturday ko Sunday ba matsala,Hajja tana ta murna tana yawwa yanzu naji magana bana kauna na bude ido naga yaran nan a gidan nan,wlh bana kaunarsu,babu wata mace dana tsana a duk matan da Aayan ya aura sama da wannan,nema take ma ta rusa min kan zuria ta,abinda na dade ina ginawa take nema ta rusa,Ameer yace gaskiya dai nima bakiga yanda nake jin haushin shiga part dinsu ba,ba a son raina ba,bana so ko kadan basu da kunya,Hajja tace ai babbar cikin itace duk shegiyar ita ke juya komai Mufeeda ba,Ameer yaji haushin zagin Mufee da Hajja tayi Amma ya danne sai yace a'a Hajja ai ta tsakiyar data karshe Meenat da Ma'eesha sune shegun,Hajja taja tsaki jibi wani suna na Aljanu malam,tun daga sunan ma kasan na aljanune wai Ma'eesha,Dariya Ameer yayi yace Hajja kenan ni na matsu ma muje a gama da yaran nan baki daya,Hajja tace Allah ya kaimu asabar sammako za muyi asubanci da wuri.
     Ranar Asabar da wuri Hajja ta shirya tsaf ta nufi wajen Ameer, ta fara buga masa kofa yasan itace kawai sai ya koma kalar me cuta ya kwanta kamar me cuta ya fara numfarfashi kamar zai mutu,Hajja taji shuru ba a bude ba nan take ta tura kofar da kanta,ai ta hango Ameer na murkususu da Sauri ta shiga tana lfy dan nan ina can ina shiri ashe kana cikin wahala me ya sameka?ta furta kamar zatayi Kuka tana girgiza shi,Da kyar Ameer yace Hajja.....ba...na...boye..miki...komai...aure...nake...so...ciwon...sha'awa ne...Ya motsa...Me yasa baka fada min ba tuntuni idan ka mutu ka barni ya zanyi tashi muje asibiti,Ameer yace Nasha magani Likita ya kawo dazu yanzu zai daina,Hajja tace ai ko dole ayi maka aure ko da Sajeeda ne,Ni wlh idan aka bani Sajeeda sai dai ciwon ya kasheni bari zanyi ya kashe ni Bazan iya yin komai da wannan ba,Hajja tace to kwantar da hankalinka sannu kaji,mu bar tafiyar sai wani satin idan Allah ya kaimu,Allah baka lfy kaji,Ameer a ransa murna yake yace Ameen yana jin dadi an fasa zuwa.








AsmaBaffa
[1/21, 11:08 PM] Asmabaffa: 🌖🌖🌖🌖
🌖🌖🌖🌖

   KASUWANCI NA







         86-90







Official











By
AsmaBaffa








    
     AGAS, MMN HUSNA,AMINA AMINU, Mom Ammar page dinku ne domin jin dadinku.








      Ameer yana ta rashin lafiyar karya sai Sunday yace ya warke da yamma ya feso uban Wanka sai part dinmu lokacin kawata Nawwara sarkin son jin Gulma da munafunci tazo min ziyara nasan badan Allah tazo ba,ganin kwakwaf tazo taje ta samu labarin fesawa,Kuma Alhmdllh taga gida iya gida,yau ta tabbatar da gaske gidan kudi nake aure ba abinda ban bata taci ba na jin dadi munyi mata babbar sauka, taci kwalliyarta ta masu rufin asiri tayi kyau kuwa ba karya, muna Hira a palo ta dameni sai ta gano Cikin Bedrooms nace to muje na rakata ko ina ta gani banda dakin Aayan,wai sai tace to dakin mijin naki fa ko duk yanda muke dake baza ki barni na gano kayan alatun ciki ba? Shuru nayi mata,tace kefa Amaryace gidan Amarya nazo gani kinga kuwa dole na ga ko ina,Nasan gulma ce kawai Allah kiyashemu mu abinda akeyi kenan yanzu.
    Murmushi nayi nace banda dakin mijina ko baya nan baza ki gani ba bare yanzu da bacci yake ma,ina laifi da na nuna miki sauran me kike so ki gani?

   Tabe baki tayi tare da cewa a hankali zamu shiga na kalla bazai tashi ba ta ya zai san mun shiga ma tunda bacci yake,Hmm Nawwara kenan ki hakura haka yafiye miki Bazan bari ki jawo ya tashi daga bacci ba,bai dade da farawa ba ma da kyar na samu ma ya kwanta Sabo da ya huta jiya bamu samu munyi bacci da wuri ba shine kuma zan bari a tasar min shi,ke a hankalinki ya dace ki shigarwa mace har dakin miji? Bada ni ba,Nawwara tace yaushe kika koma haka Mufeeda? Dariya nayi kawai na jata muka koma kasa nan muka hango Ameer ya shigo yana zaune,Ameer lfy kwana biyu kuwa? Murmushi yayi tare da cewa ai baku da kirki kunga shuru ko ku nemeni,Nawwara ta gaisa shi ya amsa tare da dauke kai can gefe,Nawwara sai gyara riga take tana kara bude mayafi tare da karairaya don kawai ta birge Ameer yace yana sonta itama ta shigo gidan kudi Amma ko kallo bata ishe shi ba, waye wannan fa?Nawwara ta tambaya, cousin din mijina,tace ok,muna haka sai ga Aayan yana sakkowa daga samansa yaci uban wankan Wani danyen yard  Fari kar yanda ya hadu ba a magana ma,wani kishi ya soke ni bana so Nawwara ta ganshi kar taji tana sonsa nasan duk wacce taga Aayan sai taso ace shine mijinta,Aayan kuma shima bana so ya ganta Sabo da tayi kwalliya harda jambaki kar ya kyasa shine nake kishi sosai.
 
     Nan take na bata rai kamar na boye Nawwara Amma ba hali,mikewa nayi da Sauri na Isa gabansa,Murmushi ya sakar min tare da cewa zanje wajen Daddy ne sai na fita wajen Yarima akwai wani abu da zamu tattauna a kai,Baki na turo gaba ina shagwaba ni...to wai me zaku tattauna? Kallo na kawai yayi ya share maganar yana kokarin wucewa,Nace dan Allah zamu je Saloon anjima,na aiki Drivers din gidan nan basa nan gaba daya kowa da inda na aikeshi, sai muje a Napep ko Ameer ya kaimu,a'a ke baza ki fita ba fa yace Direct,na marairaice pls kaji,ki ebi kudi ki bawa su Meenat Ameer ya kaisu Amma banda ke, ki wanke naki a gida mana, ina nuna kaina ni din?Yace kefa din,ya wuce zai fita bai ma kula ko da bakuwa ba har ina murna sai ji nayi Nawwar tayi shishigi tace Ina yini, lfy Alhmdllh ya furta da fara'a tare da tambayata frnd dinki ce? Nace ae tare muka taso a unguwa daya sunanta Nawwara,yace Ok thts Good Amma kina gani zan fita baki fada min ba,da Sauri na share zancen ina jin Haushi ana kalle min Aayan dina nace Zaka biya Office ne? Me zai kaini Office yanzu kuma,a dawo lfy Allah ya kaika ya dawo da kai lfy,yace Ameen kafin ya karasa na bude masa kofa kawai Sauri nake ya bar gidan Nawwara kar ta ganshi,yana fita na rufe kofar sannan na kalli Ameer nace Ameer Saurayi mijin yan mata,masu tashe da ji da kai,Allah ya hadaka da mata ta gari zukekiya Amma da ta sha kallon wanka da iyayi,Dariyar jin dadi Ameer yayi yau Ina yabonsa da kaina sai yace haba Aunty  ai mijikinki ya fini,nace daga shi sai kai kusan irin halinku daya,wlh ya fini dan mijinki ne ba kya ganin laifinsa,nace uhmm to me kake so na baka kaci yau? tuwon danyar shinkafa miyar Kubewa danya da kifi Amma sai dare,Nace ka gani ko na fada ma irin halayenku daya da Mijina,Nawwara tana zaune tayi shuru sai tunanin Aayan take ya gama Tafiya da zuciyarta gaskiya zata dage da zuwa wajena kullum ko Aayan zai so ta ya kara ta biyu da ita ta shigo itama ta kwace gidan,ko hannunka ya rike ai ka dace wannan,cin Amanar Mata bama kawai a aureshi ba kawai a shigo a kwace gidan,a kori uwar gida ko a wulakantata su kuma su zama sune a gaba.

    Ameer ka kai min su Meenat Saloon mana dan Allah,Ameer ya turo baki Amma Aunty kin san Meenat bata girmama ni ko dama Ma'eesha ce Amma wannan sai girman kai bana son kulata ni dai,kayi hakuri ka jira yanzu Meenat Zata dawo sai ku wuce Ma'eesha tana daki,kasan ina ji da kannena nafi so kullum na gansu sun hadu,Ameer yace ai ku dama Hadaddu ne Aunty,amma in kana da kyau ka kara da wanka.

   Muna hira har dai Meenat ta dawo tana cin abinci nace su shirya,dama sun dameni zasu je Saloon,kudi na basu Ameer yace haba Aunty ina wajen sai kin basu kudi ina da kudi,Meenat tace mu dai a bamu kudinmu Sis Sabo da tsaro, na basu kuwa,tana karba ta Radawa Ma'eesha kinga munyi cuwa cuwa mun samu na kashewa mu kara a schl,shi kuma ya biya mana na Saloon babu ko sisinmu,Ameer yaji Me Meenat take fadawa Ma'eesha.

    Ya kaisu hadadden wajen Saloon tare dashi suka shiga yaki fita wai sai yaga kalar gashinsu kamar na Maza ne ko dogo ne yanda zai musu dariya da kyau, Meenat ta zauna tare da warware gashinta Ameer ya dinga mamakin tsayinsa kamar na larabawa,haka Ma'eesha ma yace Allah ya taimakeku kuna da gashi yau da sai na dauki pics nayi status a social media,Meenat tayi dariya tare da cewa ta Allah ba taka ba to yaro,nine yaron Amma kin san na girmeki nesa ba kusa ba ma kuwa,Maeesha tace kaine ma Kwaja karewar girma nan suka fara dariyar Kwaja,yace zanje na dawo kafin a gama muku,Meenat tace a taho mana da me zafi tare da Me sanyi,fada kawai tayi sai ko gashi ana gama musu ya dawo,suna shiga mota suka ga Take away guda Wajen biyar wai duk nasu ne har Nima da nake gida,Gasassun Kifi da chips,sai Hanta lafiyayya taji hadi,ga su ice cream da yogourt.

    Suna shigowa lokacin Nawwara ta min Sallama ta tafi har kudi na ebo cikin na Aayan na bata Dubu biyar da kayan kwalliya iri iri ta dinga murna tana godiya,ni kuwa Zama nayi na fara tunanin irin kyautar da nayi mata kamar wacce tazo da asiri na bata kudi masu Uban yawa haka kuma wai harda kayan kwalliya ma.

    Su Meenat ne suka gyara min gidan ni kuma nayi girkin na shirya komai a Dining sannan na Shiga wanka ina tunanin Aayan yanzu suna can suna Hada min plan a raina nace duk kuyi Ku gama zaku San dani kuke zancen,yau ba Sallah nake ba shi yasa kwalliyar da nayi har da Nail paint nasa a farcena sky Blue nayi wani red wani Blue ba karamin kyau yayi min ba,nasa wando tight 3qtr me kyau baki,sai rigata Sky blue ta hadu gashina yasha gyara sai kyalli da kamshi nake ta ko ina ka rantse Balarabiya ce ni,na fito tare da Shiryawa Meenat Abincin Ameer a wani kwando me kyau nace ta kaiwa Ameer can part dinsu sabo da shi yace bazai dawo ba na bayar a kai masa abincin.
    Meenat ta karba ba musu ta fita me aiki ce ta nuna mata ta shiga part dinsu su uku Mazan Ameer,Khaleel tare Mujaheed gaishesu tayi sannan ta ajiye a gaban Ameer tace ya Ameer gashi inji Sis,Yace na gode,ita kuma ta juyo zata dawo,Khaleel Kansu ya daure sai mamakin Ameer su ke yanzu abin nasa har ya kai haka? Gaskiya zasu fadawa Abbi me yake shirin faruwa kuma fa dasu aka cinye abincin nawa.

     Sajeeda taga lokacin da Meenat ta shiga ta fito daga part din su Ameer shike nan ta dinga fesawa cewar Meenat bin maza takeyi abin har part din su Ameer,da sauri ta shiga sabo da kishi ta samu Ameer ai wlh Allah ya Toni asirinka dama abinda kakeyi kenan,to sai kowa yaji macuci yanzu har ajinka ya zube da zaka nemi wannan?ai gwara ko me kake so kazo wajena.
   Khaleel da Mujaheed suka Mike tare da basu waje,Ameer ko kallonta baiyi ba har ta gama masifarta,yace ai ta fiki daraja da mutunci a idona ta kuma fiki class,asararriya me rabawa mazan waje,ke kike haka shi yasa kike tunanin haka kowa yake irinki,Sajeeda ta rushe da kuka tare da ficewa da Sauri.

    Washe gari Sayyah kawata ce ta min waya zasu zo min ziyara tare da wasu kawayenmu yan Schl Mardiyya da Islaha,So nake Aayan ya bar gidan kafin suzo kar ma su ganshi wata ta soshi,5pm suka ce zasu zo ni kuma 4pm ina yin Sallah na bar kitchen na shiga wani Palo da nasan Aayan yana can sunyi wani meeting da abokan kasuwancinsa,Nasan ba kowa yanzu shi kadai ne,yana zaune ya baje yana cike wasu takaddun Office,Sallama nayi masa a hankali tare da Zama kusa dashi har muna gogar juna nace sannu da aiki,lemo ya kurba sannan yace Yawwa har kin gama aikin? A'a wai yau baza ka fita ba har yamma tayi? Tabe baki yayi tare da cewa no,nace yau fa Tuesday guda ai ya dace ace mutum yana aiki,Yau bazan iya fita bane shi yasa,Shuru nayi can na kara cewa gaskiya kana hutawa da yawa baka fiye fita ba jiya ma fa baka fita ba sai yamma liss,yau ma hakan take ai sai yamma zan fita,gashina na gyara na gaba nace yau muna tare kenan har dare? Bironsa ya ajiye sannan ya kalleni sosai yace korata kike?so kike na fita kenan anya kuwa kina da gaskiya tsakanin jiya da yau,jiya ma fa har murna kike na fita,a'a ni bance ka fita ba tambaya nayi na Mike zan bar palon ya riko min riga na koma na zauna amma sai nace aiki fa nakeyi kasan zanyi baki, je ki karasa aikin to,mikewa nayi na fita,har na rufe kofar na kara budewa a hankali tare da leko da kaina muka hada Ido na washe baki tare da cewa to ko zaka koma Bedroom dinka zan gyara nan? Wai wayo zan masa kar ya fito yace zaije samansa bakina su ganshi, ban san me kike nufi ba zo ki kwashi papers din sai na koma can din,Da murna nazo na kwaso masa ina bayansa yana cewa mutum da gidansa sai yanda akayi dashi ya zanyi,ina dariya har muka je Bedroom din na ajiye masa komai tare da cewa asha aiki lfy ranka ya Dade,murmushi ya saki yasan dana ce Ranka ya dade ko Yanlabai wayo na shirya masa wai zan masa.

    Sai da na gama shirya lafiyayyan girki kala Hudu ga kayan Sha iri iri ko ina na gyara sai kamshi ke tashi,wanka na fada na tsantsara kwalliyata cikin fitted gown black and Silver,gogorona Silver na daurashi dan dagwas,sarka da abun hannu duka silver color wow ga red jambaki na saki gashi yalala.
    Ina fesa turaruka naji sallamarsu suna knocking, fita nayi tare da bude musu su uku  Sayyah,Mardiyya da Islaha yar gidan Wata babbar lauya, idanu suka zuba min yanda suka ganni kamar wata Queen,nan suka hau yabon kyauna Sayyah tace shegiyar kin ganki kuwa muna ganinki a Uniform muna rudewa Ashe kinfi ma haka gaskiya mijinki yayi dace ya huta,Mardiyya tace zai kwashi harkoki,dariya mukayi gaba daya nace kufa baku da mutunci,Islaha sarkin jiji da kai,bata kawa sai da me kudi,nima ganin mijin da nake aure masu kudi ne yasa ta biyo su dan ta tabbatarwa idonta,ta kuma taba ganin Aayan a TV tana sonsa sosai shine yanzu ta samu hanyar da zata ganshi face to face ko zata dace ni ko ban sani ba.

     Zama mukayi a Palo suna kalle kalle duk sun Zama yan kauye suna kallon haduwa,Maeesha na kwalawa kira,yau sabo da na kara kankaro girmana bance Ma'eesha ba wai nima fa na Zama yar gayu sai da nayi zaman Hajiyoyi a kujera irin me ji da Hutu da Naira sannan na wani Kebe baki tare da cewa Angel...sai ga Ma'eesha ta fito da Headphone a kunnenta tana Jin waka cikin English wear riga da skert tayi kyau, da fara'a tare da ladabi ta gaishesu suka amsa Sayyah tace Ma'eesha ko,Marrdiyya tace gaskiya kuna da kyau Mufeeda,nace tnx Dear, Islaha kuwa sai wani cin magani take tana yanga sai danna waya take,tana kishi da bakin ciki.
   Angel kawo musu ruwa,Maeesha ta cika musu gabansu da kayan abinci dana Sha iri iri,nace to ya akayi Frnds Gist me mene News?
    Sayyah dama itace muke so close tace bari mu fara cin abincin Amarya muji ko kin iya,Nace ai kema kin sani yarinya,muna ta hira sosai banda Islaha,ko abincin taki ci sabo da bakin ciki,mu kuwa bamu San meke ranta ba ko ta kanta bamu bi ba.
   
    Kamar Aayan yasan yau kankaro girma na da mutunci na nakeyi gaban Frnds,lekowa yayi ta sama tare da dafa jikin Karfen steps din sannan yace Baby ina kika sa min Envelop din nan,bana so frnds su gane min shi,amma munafuka Islaha tana Jin murya tasan shine da sauri kamar wata engine haka ta daga kai kamar kadangare tana ta faman kallonsa,wani haushinta na naji kamar na koreta daga gidana, gani nayi zai sakko kasa kuma yasha wanka da alama fita zaiyi, nace bari nazo na dauko ma,ina yauki da kisisina muka hadu dashi a steps,su Sayyah kallo kawai suke Sha,a gabansa na tsaya ina murmushi kamar zan shige jikinsa na zura hannayena na rungumo bayansa amma bamu hada jiki ba,kyakyawar fuskata yake karewa kallo da idanunsa masu kyau,hannu na zare tare da saka hannuna cikin nasa nace muje ka gani,ba musu ya Bini tare da zame gannunsa,ina gaba yana bayana ya daura hannayensa biyu a waist dina sai kare musu kallo yake har muka shiga Bedroom.
    Islaha kasa kallon tayi sabo da bakin ciki,Sayyah da Mardiyya kuwa kunya suka ji lallai Ashe suna ganina yarinya ba ruwana da duniya Ashe haka nake sai kuskus sukeyi suna dariya,Islaha na zabga musu Harara.

     Muna shiga yace na fasa fita ni duk ya wani birkice min,nace dan Allah? da ka kyauta dama a raina bana so ya fita su ganshi,yace amma sai dai in zaki zo mu kwanta,baki nayi kaga ai bazan kwanta suna Palo ba ka bari sai dare,to bazan zauna ni daya ba bari na fita,ba yanda zanyi dole na barshi ya fita tunda ina da bako,kallona yakeyi kamar zai hadiyeni kinyi kyau shine sai da zaki baki kika yi wannan kwalliyar su kika yiwa? Wani idan ya shigo fa ko Ameer,dadi ne ya kamani ko dai ya fara kishina,nace ai kasan dai ina yi kullum iri iri sai wannan kadai zaka ce tafi kyau?, bafa nufina kinyi wani kyau can da yawa ba,kin danyi dai kyau kadan,addini kuma ai baice kiwa wani ya gani ba sai Muharrami ba nufina wani abu ba is just tht na tunatar dake addi ne.
    Murnata ta koma ciki haushi naji,kawai nace tnx na dakko masa Envelop da ya nema nayi waje abina ko saurararsa ban kara yi ba.
    Ina fita muka dora hirarmu sai gashi ya fito zai fita,Sayyah tace ina wuni? Sai lokacin ya gane da mutane a palon,Amsawa yayi kawai da fara'a ya kara gaba,zumbur muka ga Islaha ta Mike wai ita gida zata tafi,Sayyah tace amma kin San haka ne yasa kika ce Muzo ki kawo mu a motarki? Sai Ku hau Napep ni na gaji tafiya zanyi,Nace ki Bari Driver na zai kaiku ga motoci a gidan nan sai kun Zaba,gaba tayi tare da cewa sai mun hadu a schl.

     Sauri take ta cimma Aayan dan ta samu dama amma karaf sai suka ci karo da Ameer zai shigo part dinmu,karo sukayi da kai,dama tun asali kun San yan gidan basu da mutunci ko wanne bako ne babu me kulaka,yana dagowa yaga tayi ma gaba abinta,cikin zafin nama ya jawo rigarta baya tare da wanke ta da mari are u Mad zaki buga min wannan katon kan naki ki wuce baki da hankali,Hawaye ne ya zubo mata ba Marin ne ya dameta ba irin asarar da ya jawo mata bata ga Aayan ba sai fitar motocinsa taji.

     Kyaleshi tayi ta wuce shima ya kara gaba yana takaici,Tana yin gaba ta hadu da Su Haneefa,Sajeeda tare da sauran yan matan,Gefe su Khaleel ne ke buga game,Tazo wucewa Haneefa tazo daukan Ball dinsu sai ta sata a kafa ta saita kan Islaha ta buga mata da karfi sai ga Islaha Tim a kasa nan ta saki Kuka baki ya fashe,su Khaleel da sauran suka dauki shewa da dariya,Bata kula su ba a tsorace da gudu ta fada yar karamar motarta ta bar gidan a gigice dama gidan idan rashin kunyarka bata kai karshe ba to baza ka iya shiga ka fita lafiya ba.

   Bayan sallar Isha nasa Driver ya maida su tare da kudi ko wacce Dubu biyar kuma a kudin Aayan nake shiga kawai na ebo na basu tunda ni ba wasu kudi nake kashewa ba kuma ba baki nake ba yana dawowa nake fada masa na ebi kaza yace ba damuwa sabo da yasan ina da hankalina.
   Aayan baya fita ya dade a waje ko wanne time daga aiki sai gida ko masallaci,Hankalina ya tashi Meenat bata dawo ba tunda ta tafi schl zana Exam,Kuma 4 zuwa 5pm take dawowa Normally amma gashi har bayan Isha bata dawo ba yau.

   Ma'eesha tace Sis  Meenat fa ya zamuyi Innalillahi har yau bata dawo ba,hankalinmu ya tashi sosai har na fara kuka ma ni ganin har Aayan naji shigowar motocinsa amma Meenat shuru,Kuka nake sharba ko sace Meenat akayi wayyo,Aayan yana shigowa yaga muna kuka yace lfy? Nace Meenat bata dawo ba tun safe har baki na sun tafi gashi mun kira mutane da dama har schl mate wai sunce ta taho gida,ina zata tsaya dan Allah idan ba saceta akayi ba,Aayan yace zata dawo ne ai mene na kuka bari ki gani,Aayan ya dinga bige bige waya ba labarin Meenat,Kawarta Husna na kira nace dan Allah da kuka tashi ko kinga Meenat sanda ta hau Napep ko Taxi? Husna tace wlh wani me Napep muka gani Anty yayi parking a bakin schl da yawa student sunje zasu hau yaki daukan kowa amma Meenat ganin yamma nayi taje tace ko zai kaita gida ba musu yace tazo su tafi yanzu Anty bata dawo ba? Ina kuka nace bata dawo ba wlh Husna an sace Meenat.

   Shi kanshi Aayan jikinsa yayi Sanyi ya rasa me ma zaiyi,amma baya so ya nuna mana kar hankalinmu ya kara tashi sai ma lallashinmu da yakeyi,Muna haka sai ga Ameer ya shigo shima yace lfy? Nace Meenat Babu ta bata an saceta ina kuka na bashi labari,shuru yayi tare da Zama a kujera yace maybe wani tayiwa rashin kunya ya saceta,nace zata aikata gaba daya haka muke ba a taka mu muyi shuru sai mun rama bama daukan raini.

    Ameer yana ta tunani sai kuma ya Mike yace Zo muje Ma'eesha mu bincika wani waje muji,da sauri ta maka Hijab ta bishi tana Hawaye, mota suka shiga ya figa da sauri,suna tafiya ya kira wayar Sameera Yar daba bugu daya ta dauka tare da cewa Hello waye? Ameer yace Driver din Rabiu Rabson ne yace na nemeki akwai Deal,Sameera ta kyakyace da dariya tare da cewa shege Rabson Ashe yasan dama ina nemansa,zo Ku dauki karamar shegiyar nan gata an kawo min ita har gida wlh sai sun gane cewa ba a ja damu,Ameer ya kara kumbura Murya ta yan daba yace kadan daga aikinki ice ko akwai kudi karfa ki mana yawa,tace ai ko nawa ne zan kashe akan wannan yarinyar yanzu ma nasa a sauya mata kamanni.
    Ameer yace wanne gidan kuke yanzu?gidan karshen layin nan can dajin da ka sani na wajen gari nan Sameera ta gwada gidan,Nan take Ameer ya kashe waya ya kira wani cikin yaran Sameera ya kara tabbatar masa nan ne gidan,yan Sanda ya saita da komai suka nufi gidan.

    Suna zuwa yan Sanda na labe Ma'eesha ta cika da mamakin Ameer yanda yake abu kamar babban soja ko Dan sanda,gashi da basirar gano matsalar abu har ya iya yin tunanin Sameera ce zata iya aikata haka,zauna a mota Ameer yacewa Ma'eesha shi kuma ya shiga gidan,ta kan me gadi yan Sanda suka fara Damkewa sannan suka shiga,Sameera na Zaune ta hakimce a saman kujera ga kartin Maza sun zagaye Meenat,mutum daya a ciki ne yake dukan Meenat duk ya fasa mata jiki da katuwar bulalar wire ta Wutar Nepa.
    Meenat sai kuka takeyi Sameera tace sai ta bata hakuri ita kuma tace akan ta bata hakuri gwara a kasheta.
   Yan Sanda tare da Ameer ne suka fado dakin, Meenat tana ganin Ameer shi kadai ta sani ta Mike da gudu ta fada jikinsa tare da kankameshi, Ameer yana tsaye kikam ya kasa komai,yan Sanda suka kama su Sameera da yaranta gaba daya aka hankada keyarsu,Sameera ta kalli Ameer tare da cewa u r smart zan dawo kanka sai na fito.
   Ko kulata baiyi ba ya dauki Meenat kamar jaririya sabo da sun mata rauni da yawa zata bata masa lokaci, suna tafiya yace ki min shuru ni ko na jefar dake,Meenat da iya shege sai tayi Murmushi tana share hawaye ta kara wani kwantar da kanta a kirjinsa,yace anji jiki me laushi da kamshi dallah tashi da badan Anty Mufee ba bazan zo ba,a hankali tace Na dai gode yaron kirki,nine yaron naki? Shuru tayi,Maeesha tana mota ta hangosu ta danji haushi a ranta kishi tana son Ameer amma kuma ta tuna ai yar uwarta ce ko Ameer din take so ma zata barwa Meenat shi kuma ma ai ga jikinta da rauni taimako ne,
    Sai murna takeyi ta fita da gudu,Ya sa Meenat a bayan mota sannan yaja sai asibiti,ya hana a fada min ina ta faman Kuka na Aayan yana lallashi,Anyiwa Meenat abinda suka dace a asibiti sannan suka taho gida,sai ganinsu nayi gaba daya Meenat na dingisa kafa,murna wajena da Hamdala ba a magana,Gaba daya muka zauna a Palo,Maeesha ta bamu labarin komai sai godiya mukewa Ameer har Aayan,Aayan yace ya akayi ka gane Sameera ce? Ameer yace tunda muka je Birthday party naji furucinta nasan sai ta aikata,ina jin ba Meenat nayi tunanin itace sabo da sunyi fada a wurin party Aayan yace sunyi ma da Wannan marar jin ya furta yana dungure min keya.

    Na dinga tsinewa Sameera kuwa,Meenat tace to sarkin Mita yau kwana za ayi ba bacci kina nanata zancen nan,ai kuwa Ameer har ya tafi idan na tuno sai nace Ohhh ke duniya Allah dai ya tsinewa Sameera,Aayan yace addua zaki mata,bazan bata bakina ba nace,Meenat sun kwanta nima munyi shirin bacci ina kusa da Aayan yana zaune Saman Bed yana danna waya, nace Hmm Amma Sameera Allah ya wadaran Halinta,kallona yayi yamin shuru har ya gama abinda yake yace kwanta ki daina damuna da wata Sameera,nace Allah ai Sameerance yar Iska ta bani haushi na kwanta a jikinsa,munyi shuru har bacci ya fara tafiya dani na tuna nace Wai Sameera tana da iyaye,tsaki yaja ya juya min baya,juyowa ya sakeyi tare da rungumeni ya fara Romancing dina na zare hannunsa daga jikina tare da cewa kyaleni naji da jimamin abinda ya Dameni Sameera Allah ya kwaso jarabar duniya data lahira ya.....bakinsa baji cikin nawa,Na kwace baki na nace inba sai naci uban Sameera ba Allah ya....Ni ba Uban Sameera ba dai cewar Aayan,sai na tuna me yake nufi nayi shuru duk yanda yaso na bashi dama mu Sha murje murjenmu naki yarda ni jimami nakeyi,muryarsa naji cike da haushi yace Allah ya isa tsakanina da Sameera tazo kawai ta Rusa min Harka,Dariya nayi tare da cewa kaima ka dawo hanya ke nan? Yace yau kwana zanyi ina kwashewa Sameera Albarka ta cuceni.
    Zancen muka Dena amma ya hanani sakewa da tabe tabe ban san sanda na mika wuya ba muka Sha romancing dinmu cikin nishadi da jin dadi.

    Kwana biyar tsakani yaune kuma Hajja ta tasa keyar Ameer suka tafi karbo magani dole ba yanda zaiyi gudun kar ta gane ya bita sai da suka gama zagayensu dama duk ta sanar musu a waya an hada komai, duk wajen Malamin da suka je sai Ameer yace Malam to kuma me zamuyi wannan magani ya karye ko munyi aiki dashi bazai ci ba?ya dace mu sani gudun kar mu bata rawar mu da tsalle,Hajja har murna take Ameer me kaifin basira ne,bata San so yake duk ya karya maganin ya watsar dasu ba,bai so ya kona kar azo wani abu kuma ya samu Su Mufee,gwara komai da ilmi.

sai da suka huce gajiyar Hanya tace to Ameer gasu ka tafi dasu duk nayi ma bayani yanda zakayi amfani dasu,dana abinci,dana sawa a cikin pillow,kasan gado,da wanda zaka samu ka yafa mata a jiki ba tare da ta gane ba,Ameer yace an gama ya wuce da magunguna,cikin dare duka ya fito dasu wani Malamin yace ana musu fitsari sun karye,nan Ameer ya fada toilet ya tsula musu fitsari ,wasu Kuma akace idan aka kona etc duk yabi yayi musu yanda Malam yace in anyi baza suyi amfani ba sun karye, sannan ya juye komai a toilet yayi Flowshing gaba daya suka tafi.
    Kwana biyu tsakani ya samu Hajja yana murna yace aiki ya kammala na gama komai sai saurare,Hajja tace badai su kamaka ba ko?yace haba ai na girmi tunaninsu.

   Kusan kullum sai na je na gaisar da Daddy haka Su Meenat ma, yau ma na shiga Bedroom din Aayan domin mu kwanta na tadda suna waya da Yarima,Aayan yana dariya da gani a raina nace ta mugunta ce wannan, sai naji yace Saura kadan da kanta zata San inda ta nufa ai komai ya tabbata na gane ta gama fadawa sai kuma yanda zan tarwatsa komai,baki na bude a boye na kara danne kirjina sabo da tsorata da nayi ba Shakka ni suke nufi, wani kuka yazo min a raina nace sai an sakeni,yana gama wayar kamar me Aljanu na fada kansa Saman Bed ina kuka sosai na fara cizonsa da yakushi ina kuka nace sai an sakeni wlh bazan zauna ba,yana kokarin cireni a jikinsa ya kasa,Mari ya kwada min har biyu wanda yasa nan take na dawo haayyacina amma ban daina kukan ba,kallo na kawai yakeyi da mamaki bai San me ke damuna ba,shi yasan bai min komai ba,ni kuwa kukana nakeyi,ya kasa cewa komai duk nasa fatarsa tayi jajir inda na yakusa da cizo,jikina yayi Sanyi kuma naga ban kyauta ba,da alama na bata masa rai matuka Allah sarki ina son mijina ni dai Bana fata a sakeni bacin Raine kawai da zuciyar banza me kai mutum ta baro sai an aikata ayi dana sani marar amfani,Shesheka nakeyi naga ya Mike tare da cewa miko biro da takarda a fusace,Nan take jikina ya fara bari ina addua kar ya sakeni,a hankali na kalleshi shima ni yake kallo,nace Dan Allah karka sakeni kaji? Tsaki yaja yace kawo min nace ko,nace dan Allah ni dai dan Allah pls na fasa wlh kuskurene ina son Aurena,Yace ni ance miki mahaukacine ko yaro ne irinki da zakice nayi abu ba tunani nayi,dakko min biro nace ko ya daka min tsawa,jiki na bari nace gashi na dakko na mika masa kuma na rungumeshi tare da dabaibayeshi ta ko ina,a hankali nace in dai akan na yakushe ka ne kayi hakuri bari na biyaka fatarka,Toilet na nufa ya Bini da kallo kawai,ruwa me Zafi a bowl tare da dan towel karami fari na dakko,ban kulashi ba na cire masa riga tare da kwantar dashi tunda yana daga Zaune, yana kallon ikon Allah na gasa masa jiki,yace kin gama?nace ae,yace to kawo min takardar da biron a rude na fara ina ina da soshe soshe na kashe light duf na cire kayana duka na shige masa jikinsa gaba daya na sukurkutashi,yace ba abinda kike nufi zan rubuta ba fa abu zanyi Jotting na Office nace ni gobe kayi banda yau,Sai salo nake masa,yace fada min me yake damunki?idan baza ki fada ba kuma fitar min a room,cike da shagwaba na sanar masa komai da na naji suna fada,Dariya ya dinga yi tare da cewa amma ke anyi sakarai,kin jawo na mareki A banza, to a  kan Business muke magana wanda ya hadamu da wata take shirin damfarar mu wai zata mana wayo mu kuma mun fita wayon shine fa kawai,dariyar jin dadi nayi nace budurwa ce ko bazawara? Yace Bazawara ce mene? Hmm ba komai dan Allah tana da kyau? Yace ae mana sosai,baki na tabe jikina yayi Sanyi nace nifa?Ina da kyau? Dariya shima yayi sosai yace ae kina da shi mana,nace hm yaudara dai ko,am serious ya furta nace taya zaka ce tana da kyau nima kace ina dashi ai daya zaka dauka.
    Kina da kyau to,nan ma nace ban yarda ba na fara ja da baya zan Mike na bar room din,ya fisgoni na fado jikinsa yace banda Negative thinking Baby ya hade bakina da nasa yana min zafafan kisses idon na lumshe ina mayar masa da martani tare da bashi hakurin abinda na masa shima yace kin jawo na mareki am so sorry,kumatuna  na shafa cike da shagwaba nace amma na Maru wlh da zafi kayi min











AsmaBaffa
[1/24, 8:17 PM] Asmabaffa: 🌖🌖🌖🌖
🌖🌖🌖🌖

   KASUWANCI NA







           91-95







Official











By
AsmaBaffa







       

        HAFSAT KHAIRAN, NAFEESAT UMAR,CATTY,SUBYUSMAN10  jinjina gareku tare da gaisuwa me tarin yawa ina godiya da Sharhi.


     Page na HADIZA MUKTAR  yar albarka ina godiya.












    Dariya Aayan yayi kadan tare da cewa bakya jine sai kin Sa mutum ya zaneki kin jawo yanzu Bazan taba yafewa Hannuna ba, ba wani nan dama ka saba Marina tun farko ba Imani ka min Dukan tsiya kamar nayi accident da mota ko ina muka hadu sai ka Mareni bai ma dace ace na kulaka ba shine Sabo da banyi ma tunani ba na aureka, Murmushi yayi tare da cewa na daina to ko me zakiyi as from today  hannuna bazai taba jikinki da niyyar duka ba,sai da niyyar me to? Romancing,Caring etc ya furta wai dole bazai ce love ba shi, har yau ban gamsu ba ni nafi so a dinga cewa ana sona Amma sai na hakura nayi shuru.
    Na manta ban fada ma ba na bawa bakina kudi da kayan kwalliya cikin wanda ka siya mana sai an siyo min wasu na bayar da nawa Sababbin, nawa kika basu,nace hm nayi Barna fa ni kaina naji kyautar nan da nayi har tunani nakeyi ban kyauta ba kayi hakuri Dan Allah dubu goma na kwasar maka,murmushi yayi yace me yasa kika basu har goma bayan ke nasan baza ki iya kashewa kanki goman ba? Hmm kawai naje ne naga kudin naka sunyi yawa wlh gasu a jere a jere suka birgeni naji nima yau so nake na kankaro mutunci na, na zama Hajjaju kawai shine na irga na basu,amma fa a schl suna koya min abubuwa sosai kuma ko me nake so suna min musamman Sayyah,ina wannan rigunan baccin dana dinga sawa masu kyau har kala biyar ka tuna su? Yace ae na gane to Maman Sayyah ce ta bani su da naje gidan,shine na basu dubu biyar biyar ita da Mardiyya,Badan Allah kika basu ba ke nan? Dan ki kankaro mutuncinki kika ce,kin basu kuma kina jimami kina tunanin kyautar da kikayi bata dace ba dama baki basu ba,kinga ba lada kenan kuma Sabo da suna miki kema shine kika rama musu,ba haka ake kyauta ba,iya wacce kikayi niyya ita zakiyi kuma da zuciya daya kisa Iklassi dan Allah kawai ba wani tayi min bari na mata ko ki Bada ki koma kina tinanin kudinki dama baki bayar ba,kinga ba lada sai ma ko Zunubi,kuma 10k ma tayi kadan nayi tunanin ma sunfi haka,amma abinda bana so shine indai kaya ne ni na siya miki to bana so baki amfani dasu ba ki bayar wata tayi,ke na siyawa ke nake so kiyi kwalliya dasu Sabo da ina so naje na siyo da hannuna wasu ma baki san tsadarsu ba shi yasa,idan kina son kyauta to ki karbi kudi wajena kije kisiyo ki ajiye duk wacce zaki bawa ki bata a naki,wanda na siya miki sai in kinyi amfani dasu ko na canja miki new sai ki bayar da wanda kike amfani dasu, haka akeyi ba a daukan kayan miji da ya siyo ki masa kwalliya ko amfani baki dashi ki dauke ki bawa wasu in kina haka Bazan kara bari Frnds dinki su zo.
   Mata wasu don son gwaninta sai miji ya siyo miki kaya dan ki masa kwalliya ki birgeshi sai a dinga gayyato Frnds ana basu maza basa Jin dadin hakan.
 
     Sai kuma tambayata yaushe kika je gidan su Sayyah ban san zancenba baki fada min ba? Jikina yayi sanyi nace daga schl rannan mun tashi frnds da yawa suka ce ba nisa daga schl zuwa gidan su Sayyah zasu je gaida Mamanta shine nima na bisu muka tafi tare,su basu da aure ai?ae duk yan mata ne,ke kuma fa? Ina da aure mana, sai akace miki matsayinku daya yanzu? Zaman kanki kikeyi da zaki je wani wajen ban sani ba? Da kika dawo baki fada min ba mala'iku na tsine miki,shi yasa mazaje da yawa basa so matansu suyi aiki ko makaranta idan sun aure su sai a fake da wajen aiki ko schl ayi ta yawo mara amfani,wasu ma daga can suke samun hanyar bin malamai da bokaye ko tarbiyyarsu ta lalace yanzu badan Allah ya kawo zancen ba baza ki fada min ba kenan? Kuka na fara yi masa to kayi hakuri Bazan sake ba tunanina ba wani abu bane,Shi yasa har kasuwa na raka wasu ma daga schl,munje gidajen wasu ma siyo wasu abubuwan da yawa Ban fada ma ba kayi hakuri na daina,kishi ne ya kama Aayan harda kasuwa ma gidajen mutane Maza nata kallonki kamar budurwa? A rude nace ai ban kula su ba Allah duk da yawa sun tareni wai suna sona nace ina da aure,Aayan takaici ya kara rufeshi ana gane masa mata wasu sunji muryarta ma yace daga yau ko an koma schl kin daina zuwa tunda bakya jin magana ni bana son irin wannan, kuka na nakeyi nace ni me nayi to dan Allah? Kayi hakuri Bazan kara ba daga schl wlh sai gida, na yafe miki ai Amma karki sake ki san kina da aure bana son irin shirmen nan na student,kamar an matse bakikin ki gashi kinzo kin fada min ana miki fada ki fara wani kuka,

 nace to yanzu duk abinda kaine ka siya min kar na bawa kowa? No ba haka nake nufi ba,sai kinmin kwalliya dashi sosai idan na canja miki wasu sai kwashe sauran ki bayar tht's what I mean, na gane Insha'allah ba matsala,dama kana son kwalliyar tawa ne? A'a kawai dai ke kiyi kyau,wani haushi ma naji kawai nayi shuru har bacci ya kwashemu.
    Sati biyu tsakani Meenat ta gama Exam tare da Ma'eesha suka shirya zasu tafi can kauyen Ammah wajen dangi za suyi sati daya daga can su Wuce Maiduguri nan dangin Abba za suyi sati daya, na hada musu goma ta arziki tare da Driver suka tafi abinsu,ni kuwa ina gida tare da Aayan,sai Ameer da yake dan shigowa idan yaga dama bai son yazo yaga muna tare da Aayan kunya yake ji,na tambayi Aayan ya bani kudi na fara zuwa gidan su Sayyah wajen Mum dinta gyaran jiki,haka take gyaran tana bani kayan tsumi,duk na kara cikowa skin dina sai sheki,santsi tare da kyalli ga uban laushi.

    Nawwara ta min waya zata zo min again nace bana gida munyi Tafiya bana so tazo,amma Sabo da naci yau Saturday ina kitchen Aayan ya ce na mishi Shawarma na gane yana son Kalar tawa,knocking naji sai da na leka ta yar kafa naga Nawwara ce,abin ya daure min kai to uban me tazo yi nace mata bana nan ana dole ne,komawa nayi kitchen naki budewa tayi ta danna Door Bell shuru.
   Khaleel yazo wucewa ta wajen ya ganta a tsaye tsawa ya buga mata wanda ta kusa sumewa uban me kike mana a gida kamar na ubanki anki bude miki ki tafi mana kin cika mana gida Nonsense,jiki na rawa Nawwara ta kama gabanta,Haneefa tana kallonta ta saman Bene tunaninta daga wajena take zata tafi shine taji Haushi an fara cika musu gida da baki,Sajeeda ma tana wajen suna kallo akwai ruwa a hannun Sajeeda roba guda ta dakko zata sha sai ta fasa sha ta saita kan Nawwara ji kake Gaf zafi ya ratsa Nawwara tunaninta Bom ne ya fashe ta kurma ihu ta fadi kasa tana Bom...Bom...ta mike da kyar tana faduwa tana tashi da Rarrafe ta Isa bakin gate,Haushi ya kama masu gadi ta ruda su tana Bom tsawa suka buga mata tare da turata waje suka jefar kamar wanki suka kulle kofa.
    Nawwara tana karasawa gida ta fada Toilet tare da barkewa da zawo ga gefen gashinta ya fashe.

    Na gama hada masa Shawarma na shirya komai a tire na wuce Bedroom dinsa zan kai masa na bude zan shiga kenan Naji  Aayan yana amsa gaisuwa da Alama da mace suke waya da Sauri na shiga Amma sai naji yaci gaba da wayarsa, kwana biyu kiyi Hakuri Ban kira naji ya kike zama a kasar ba,Da Sauri na zauna a gefensa tare da gwara kaina da nasa na jonesu waje daya wai so nake naji Muryar macen ko Budurwa ce Amma bana jin komai,Ya matsa nima na kara matsawa jikinsa,ya matsa na kara matsawa again,kasar akwai dadi yana Murmushi harda wani Ladabi yakeyi na musamman ina jinshi ya gama wayar sannan yace min Allah ya shuryeki nace Ameen ina turo baki idan wayar gaskiya ce a fadi sunan wacce ake waya da ita Mana aji,yace to yar Us ce Sarkin zargi, wa kake dashi a can me jin Hausa na furta nayi kicin kicin,ki bari zata zo Soon kasar nan zan kawo miki ita idan tazo sai ki fada mata haka in kin Isa, baki na turo tare da cewa ni mutunci gareni an cema Allah bata Isa ta zo nan gidan ba ko wace sai na balla yarinya,murmushi ya saki tare da cewa ai ni zan tare mata fadan,da kai zan hada ai sai na mayar mata da fuska ta koma baya,keyarta ta dawo itace fuskarta,Dariya yayi yace Allah ya kaimu dan baki san wace ba shi yasa, ki shirya min kayana zanyi tafiya,gaba na ya fadi rass nace ina zaka je?Us daga can zan wuce Saudiya,Hawaye na fara tare da turo baki cike da shagwaba nace yanzu ni kadai zaku bari? Amma kasan Tsoro nake ji ko ni kadai ban iya zama a gidan nan,Ga Ameer nan zai dinga zuwa yana tayaki Hira Amma da dare kuma sai dai ki kwana ke daya,Yarima na jirana tare za mu tafi zanyi 2-3wks, ganin kamar bai damu dani ba nima kawai na share shi nace a dawo lfy bari na hada ma kayan, zuciya ta a jagule gaskiya baya so na ya kasa sanar dani zai Tafiya sai yau da zai tafi kuma ko ajikinsa irin bai damu da rabuwa dani ba,Allah ya gani nayi kokari na da zan iya,da ace bana sonsa da tuni na fita daga harkarsa Amma zuciyata ta kasa hakura dashi na rasa me yake damuna gaba daya,shi kuwa shawarmarsa ma yake ta ci ko a jikinsa dama Already naga yayi shiri tare da hadewa cikin kana nan kaya.
  Harda goge yar kwallata ina hada masa kayansa na gama komai tsab yanda ya dace na ajiye a gabansa, yana cin abincinsa na dauki paper da Biro nayi dan dogon rubu a takardar me Santayana mutum zuciya amma fa ba na love ba,na adduar Tafiya sannan na Sa a tsakiyar kayansa ba tare da ya sani ba.

    Yana gama ci ya mike yana kara shiryawa ni kuma na sauka kasa ina palo a zaune saman kujera duk raina a bace yake kadan nake jira sai gashi ya sakko cikin shiri ya kalleni tare da zuwa gabana ya zauna a gefe na jikinmu na Gugan na juna a hankali yace zan tafi Baby, ban san sanda na zabga masa uwar harara ba nace Ina ruwana to ni na nasan da wata tafiyarka ne,Kallona yayi tare da cewa shirya mu tafi tare am serious wlh i wl be missing you is Better na tafi dake,Harara na kara watsa masa ae ai dole kace haka tunda zaka tabe min jiki to Bazan je ba,ba Us ba ko birnin Sin ne Ban zuwa,Har fa Germany? ban san sanda nace Allah yasa Agadaz zamu je hhh ya dinga dariya in bake shashasha ba kin taba ganin inda Agadaz tafi Germany zaki Hada Niger da Germany ne,ina turo baki nace to ko Birkinafaso ce ehe,Dariya yayi yace ke ana maganar Europe kina kawo África,nace to ko Egyft ce harda Morocco kai ko Algeria ce,nan ma yana ta dariya,yace to Saudiyya fa? Nace ko Qudus ce,dan Allah shirya a yau za miki komai mu wuce bana son bana ganinki kusa dani,uhm sai kayi kuma zancen kake so Karuwa taji me Wa'azi tace aiki ne bai isheka ba, Marairaice min yayi sai da nayi mamakinsa kamar wanda ke so na da yawa, wai sai kuma naji tausayinsa Amma na rantse Bazan bishi ba,nace ni Bazan je ba fa,wai harda jin haushina ya juya tare da fara Tafiya,nace Aayan... Juyowa yayi nace zo pls,tunaninsa zance zan bishi ya dawo nace nasan me kake so a jikina tattaba ka tafi abinka kaji,wani haushina yaji me nake nufi?au tunanina ma jikina yake so shi yasa yake taba ni etc Amma tunda haka nake tunanina zai nuna min,tsaki yaja ya juya abinsa,nace a dawo lfy Allah ya kiyaye Hanya ayi addua me yawa Sabo jirgi zaka shiga ba dabara ga wanda aka kwashewa kafafu kasan duk wanda aka kwashewa kafafu kana sama to dabara ta kare sai du'ai,dariyarsa ya danne kawai yayi gaba,Yana fita Ameer ya shigo nasa Katon Hijab dina,jefi jefi muke hira yana ta bani labarin yan matansu da suke yaudara muna dariya, gaskiya Anty gidan ba dadi Ba Maeesha da wannan yarinyar da na sani ma na bisu munje tare naga Kauyen,Bani Address na bisu Allah zanje,Ni kuwa ya ban mamaki kawai dai na bashi Address din, tun daga Lokacin Ameer yacewa Abbi da Hajja tare da yan gidan kaf wai ya tafi Abuja interview Zai nemi Visa a wani Embassy idan ya samu,Hajja tace bazai tafi a mota ba Amma yace a mota zai je,Nufinsa tunda Rimin Gado zai bi su Meenat sai ya kaisu a mota har Airport su shige jirgi sai Maiduguri gaba daya har da shi,Hajja ta damu ita bazai je har Abuja a mota ba sai a jirgi haka ya hakura Driver ya kaishi har Airport,Driver na Tafiya ya shige Napep har inda zai hau motar Rimin Gado ya shiga Drop fyalleliyar mota karama ya biya kudi shi kadai har Cikin kauyen Rimin Gado can rugar fulani.

    Da tambaya ya gane gidan da su Meenat suka sauka yan fulani sukace yan matan Larabawa yan birni ga gidan can,Ameer sai wani make jiki yake yana karkabe kayansa tare da tabe baki yana kyankyami wai,a kofar gidan ya tura yaro wai Meenat da Ma'eesha suzo inji Ameer dan Birni,Meenat ce ta fito kofar gidan tasha Atamfa riga da Zani me style tayi kyau,tasha mamaki ganin Ameer ne da gaske to ko lfy ko Mufee ce wani abu ya sameta Meenat ta tambaya da tsoro a fuskarta, kin wani tareni da tambaya zuwa nayi naga kauyenku to Anty ce ta bani Address bakwa gida duk ba dadi shine nazo,Murmushi Meenat tayi tare da cewa kayi Kokari bari na fadawa Inna to,
   Wajen Inna tsohuwa tazo ta sanar mata,Inna tace to kuma sai ki barshi a waje gidan tsohuwa ne kice ya shigo,Maeesha ce ta fita tana dariya tace lallai ya Ameer kayi Kokari ina motarka?ke zan mareki ko wacce sai tambayar tsiya,shugo to ciki,Ameer yabi Bayan Meenat suka shiga gidan,komai na kara ne dakuna Uku irin na ruga,Tsohuwar yayar Ammah ce ita kadai ce a gidan sai jikanta babba kuma ya tafi kiwo can wani daji sai shekara ta zagayo zai dawo gida tare da shanunsu.

    Gidan Babba ne me dan fadi tare da katuwar bishiya a tsakar gidan,yasha shara tsaf dashi,Ameer da Ladabi ya gaisar da Inna,da Fara'a ta Amsa sannan tace to ajiye kayan naka ga dakin da zaka zauna can,ke Meenatu kai masa kayansa,Meenat ta rakashi dakin tabarma ce katuwa sai katifa yar siririya dai dai mutum daya ko juyi sai daí ka mike sannan ka juya,Ameer ya dinga dariyar katifar tare da cewa sai kace ta jarirai wannan har katifa ce,ni Yanzu ya zan iya kwana a nan kato dani? Daki yasha tsafta dai ba laifi Amma katifar nan gaskiya kice ta canja min wata,Meenat da Sauri ta sa Hannu tare da toshe masa baki tare da cewa rufa mana asiri kunnenta kamar micijiji yake masifaffiya ce wlh ta gaske bar ganinta haka kunyi faran faran yanzu tayi mana tatas a gidan nan.

    Hannunta ya janye a saman bakinsa tare da cewa ke baki da kunya ni kamata zaki toshewa baki kamar yaronki kato dani,ni gaskiya ki fada mata ta canja min katifa,Ai ko karaf a kunnen Inna sai muryarta suka ji tace Iyyeeeeeee... Kai kake bani kudin?ko jikana yana gari ai bazai canja ma katifa ba,duk girman wannan makekiyar katifar yo ni Allah na tuba duk ranar dana kwana a saman ta kasa Sallar asuba nakeyi,har makara nakeyi sai rana ta fito nake tashi Sabo da laushi da girmanta,ba karamin daraja mutum nake Ba zan barshi ya kwanta saman wannan katifar tawa,ai wlh ko su Meenatu basu Isa ba,amma zaka nuna min kai dan birni ko kinibibinka ne? Murmushi Ameer yayi jin yanda take ta mita tana yabon katifar da take duk ta jeme  duk ta side tudun babu Sabo da taci duniya ta gaji gata siririya ta gaske,Ameer ya fito wajen Inna yace Inna ta dakina da nake bacci a birni sai tayi girman tsakar gidan nan gaba daya,kinga Bed dina kuwa like...Hannu Inna ta daga masa kaji shakiyin yaro yo ko Sarki ne ina zai samu katifa kamar girman tsakar gidan nan in ba karyarku ta yan boko ba,sai dai ka shiga gidan Radio a Sa zancenka a labarin nishadi na tatsuniya  Amma ba a wajena ba baza ka samu karbuwa ba

   Dariya Ameer yayi tare da cewa dan kawai baki sanni bane Inna kalli fatata fa kalli kyauna, me yasa kasan da haka baka Sako gadon naka a mota ka taho dashi ba karka dameni kaje kayi wanka ga abinci miyar harda Naman Zabo,Maeesha sai dariya suke har suka kai masa ruwan wanka bayi,yaga bayi ba rufi ba komai fayau ko murfin kofa babu gashi na kara da Ameer ya fito tare da cewa shi ya fasa wankan Tafiya gida zaiyi kar dare yayi masa bazai iya amfani da toilet dinsu ba,Toilet ce kadai zata koreshi daga kauyen,rokonsa sukayi yamma Liss yayi Manage zuwa gobe sai ya tafi,ya shiga haka ba yanda ya iya kayansa ma daya cire sai ta saman katangar ya mikawa Meenat ta rike masa su,

Ya mike yana wanka jikinsa duk kumfa wata yar fulani da kwaryar nono ta bayan gidan zata wuce sukayi ido hudu da ita ta kalleshi ya kalleta Amma iya kansa zuwa kirjinsa take iya hangowa ta wajen gidan,Ameer yaga taki dauke idonta ya ware mata hannu alamar zagi dakuwa yace karbi wannan kan Uwarki,bata gane ba ta tsaya tace me kace yace baki gane ba? Hakan nana yana ware mata yatsu wai yaren mutan kauyen ya mata na zagi Haka nanan,Tace ni yace a'a ubanki nake nufi baza ki bar nan ba sai na fito na fasa miki baki,Yar fulani tace yo ni ina ruwana da kai dan zanje tallana, ko tsirara na kalleka me zai firgitani,Kaga naga kalar ta Iro,Nasan ta Ja'e,har gaisawa na kanyi data Lawalli duk ranar kasuwa iya kaci kace ta wani fara ta wani ba to duk cikinsu ta Ja'e ce Baka wuluk me zaka bude min ido dashi ta ja tsaki tayi gaba,Ameer ya zaro ido waje tare da bude baki yana mamaki yace Ana iya shege a kauye ba kunya ba komai,ana cewa yan Fulani masu kunya etc ashe duk karyace, ya kwalawa Meenat kira ta bashi kayansa nan ma sai kanta ta sadda kasa sabo da kunya kar ta hango kirjinsa.
    a gaggauce ya karasa wankansa ya karbi kayansa ya fito,Abincin ma ba dadi kasa ci yayi yace shi wlh gobe zai tafi da Safe,Gari na wayewa ko karya wa yace bazai yi ba,dama tun jiya ya karbi number din me motar da ya kawoshi jiya yace ya dawo gobe da sassafe ya daukeshi,Me mota yaji yanda ya samu kudi da Sauri ya Amsa, ai kuwa 8am sai gashi yazo daukan Ameer back to Cikin Gari,Ameer da murna ya dauki jakarsa tare da basu kudi da yawa har Inna sai godiya take tana Sa masa albarka, ya musu Sallama Meenat da Ma'eesha har mota suka rakashi ya shiga yana musu gwalo ta Glass suna dariya sai gida.

     Yana dawowa Yace wai ya fasa Interview din ne shi yasa ya dawo ya bincika yaji bazai yuwu ba,Hajja sai murna take ya dawo lfy,  toilet ya fada ya dinga dirzar jikinsa ya dade sannan ya fito ya shirya sosai ya nufo Part dinmu.

    Ina kitchen ina Hada Chips na ganshi,Na dinga dariya naji abinda ya koroshi,nace ai kyaleka kawai nayi,Gaskiya Anty baku dace da Ruga ba ina sam kauyen baiyi ba,Abinci na zuba masa ya dinga ci Sabo da ya kwaso yunwa,yana ci yana bani labarin irin wahalar da yasha,Anty toilet ba rooping bare kofa ina Bazan iya ba, yasu Meenat fa? Ameer yace sunfi kyau acan,a kauyen zasu fi kyau Ameer? Ameer yace sosai Anty baki ga Meenat ba har wasu kumatu takeyi,Ina ta dariya nace to ko dai ita zan baka? Ameer yace wannan Masifaffiyar ai sai ta kashe ni ma gaba daya.

    Yau kwana biyar da tafiyar Aayan kenan da kyar nake bacci tunaninsa ya Addabi zuciyata,na ma rasa inda zan Sa kaina gaba daya duniyar bata min dadi kullum ni kadai gashi yace Bazan fita ko ina ba, sai gyaran jiki da nake zuwa, tunda ya tafi bai kirani a waya ba nima ban nemeshi ba Amma ko bacci bana iya yinsa sosai Sabo da tunaninsa, Shima can Aayan hakan take baya iya komai sai tunanina,Yarima ya gama gane Aayan so ne kawai ya kamashi,ya kasa nutsuwa,baya iya bacci,abinda ya kaisu ma ya kasa komai,har Zazzabi yakeyi cikin dare na rashina kusa dashi.

Ameer ne kadai yake debe min kewa idan yazo muyi hirar ya tafi,idan ina bukatar abu shi zan bawa kudi nace ya siyo min Amma bazai taba karbar kudin ba da kudinsa zai siyo min komai me tsada da kyau, kullum idan ya dawo daga Office sai ya shigo kuma bai taba nuna min ko sona yake ba,ko wani abu na banza bai taba shiga tsakaninmu ba,mutuntani yakeyi yana bani girma na yanda ya kamata,
Shi Ameer ma tuni ya tuba da son Matar wani tunda yaji wani Wa'azi me Zafi,yaga ina bai kyauta ba,nan take ya fara Istigifari ga Allah ya cire komai a ransa,kawai ganin mutunci na yake dana Aayan sosai,sai kannena yanda suka daukeshi kamar dan Uwansu.

    Idan ta kama watarana ko kitchen ya shiga idan yaga wanke wanke banyi ba sai ya tsaya ya wanke min ya gyara min kitchen sannan ya tafiyarsa,hakan yasa abinci sai kalar da yake so nake mishi ance ka kyautatawa me kyautata ma.yau da dare ina bacci wayata ta shiga Ruri ina ganin Number ce ta kasar waje naki dagawa nasan Aayan ne,kullum haka yake min har sai da muka kwashe kwana Uku kullum sai ya kirani yafi a irga Amma bana daga masa waya,har ya cika sati yana kirana kullum kuma bana dagawa.
    Muna haka dashi katsam da yamma nasha wanka na cikin doguwar riga Ready made ina palo gidan yasha gyara littafin Hausa nake karantawa a wayata ina ta dariya ni kadai ashe Bell nata kara banji ba sai gani nayi an turo kofar a hankali har ya shigo ban sani ba,sai kamshinsa naji kawai ya cika wajen,da Sauri na daga kaina sama da Sauri ido hudu muka yi ba karamin Kyau yayi ba cikin kana nan kayan ya hadu karshe, Sallamar na Amsa kwarjini yasa na kasa yi masa abinda nayi Niyya,wani dadi,Sanyi,farin ciki,sonsa ya kara shiga jikina gaba daya na wani diririce,nace sannu da zuwa ka dawo lfy?kai da kace 2 to 3 wks zakayi Amma yau Sati daya ka dawo lfy? Harara ya watsa min tare da zama gefena muna gogar juna yace Baki da kirki Mufeeda,bani wayarki ya furta tare da fisgewa yaga Number ta kasar waje da ya kirani da ita har Saving nayi da sunansa Amma naki dagawa,kallona yayi yace kin ma san nine kika ki dagawa saima Saving da kikayi kin kyauta.

   Kallonsa nayi nace kayi hakuri,kin hanani yin abinda ya kaini gashi dole na dawo me zaki fada min,Yaushe na hanaka? Yatsuna ya rike ya fara wasa dasu yana mirzasu ina ji har na fara jin wani canji a jikina,Gaba daya naji wani yarrr,shi kuwa har idonsa ya canja,ban san sanda na rungumeshi ba, mun dauki lokaci ya kankame ni a jikinsa sosai Nace ina zuwa na mike tare da nufar kitchen,

   Da kallo ya bini kamar zai hadiyeni Sabo da canjin da ya gani a jikina komai nawa kara canjawa nake na kara cikowa,ga kyau dana kara ina sheki,  lemukan dana hada na fruits na kawo masa tare da Dambum naman Kaza da nayi na ajiye a gabansa tare da zuba masa lemo a glass cup na bashi a nutse, yana kallona yana sha abinsa ni kuwa shuru na masa tare da dauke kaina har ya gama ya mike tare da da cewa bari nayi wanka naga bakiyi Missing dina ba,shuru nayi masa,yace sabo dake fa na dawo,a raina har ga Allah dadi nake ji marar adadi baya misaltuwa Amma a fili nayi masa banza sai ma turo Lips dana shiga yi.
    Mikewa yayi yana murmushi yaja akwatinsa yayi samansa tare da shiga wanka yana tunanin canja masa da nakeyi kwana biyu bayan bai min komai ba.

    Su Abbi da Hajja sun sawa Ameer ido a boye ba tare da kowa ya sani ba sun gano cewar karya kawai Ameer yakeyi ashe soyayya yakeyi da Kanwata Meenat,sun gama tabbatarwa ne lokacin da suka Sa CID daya ya dinga bin bayansa har lokacin da ya bisu Kauye ya dawo kuma,tare da Sauran bincikensu,nan take Hajja ta fusata me tsanani haka su Abbi ma,Abbi yace kyale shi zanyi maganinsu gaba daya Har Ameer din,Hajja tace Yaro ya maidani sakara lallai bai san wace ni ba idan na gano cewar mutum ya munafunce ni,wlh wlh nasan Malamaina basa karya Amma dan Iskan yaron nan nasan shine ya lalata komai,kuma ba shakka shi yasa yan fashi suka tare mu kwanaki tare da amshe maganin da muka karbo,Amma kyaleshi zai san ni yayiwa haka kuma sai ya auri Sajeeda.

    Abbi yace abu na farko da zamu ladabtar dashi shine mu kwace aikinsa da na bashi a Company na,da mota sannan muce ya bar mana gidan gaba daya,kuma nasan basa shiri da Aayan bare yace zai taimakeshi,Abbi Sani yace ai ko suna shiri da Aayan kasan shi Aayan bai shiga sabgar mu bare zuriarmu,sabo da haka bazai taimakeshi ba.
    Bayan sun gama shawara suka nemo Ameer ba mutunci suka masa tatas yana basu hakuri yana Abbi kai fa Mahaifina ne amma kamar baka so na? Abbi yace nafi son uwata da kai dan Iska ajiye min mukullin motar dana sai ma,amma ai da kudina na siya,Mari Hajja ta watsa masa a dalilin wa ka samu kudin aikin ai shi ya baka har ka siyi motar,Abbi yace na kwace aikin ma kuma ka bar gidan nan Banga Amfaninka ba baka bina baka bin uwata har ita zaka yaudara? Abbi bani da kamar ku fa bani da inda yafi nan ina kake so naje? Abbi yace part din nan kasan dai namu ne to kaje wajen ubanka Aayan ya baka inda yafi nan,Umman Ameer ma tana kuka tace kayiwa kanka wlh ba ruwana,kasan dai danginmu kaf talakawa ne baza su iya rike ka ba bare nace kaje can kai ka jawowa kanka kuma kasan Aayan bazai saurareka ba,Abbin America Baban Aayan kaine ka fara masa rashin kunya ko kulaka baya yi ka san da haka,kuma ka sani nan gaba zasu ce ka dawo gida kasan ba a ja dasu dole ka dawo kuma lokacin zasu daura ma aure da Sajeeda.

   Ameer takaici ya kamashi yasan dama ko dansu ne na cikinsu basu da imani idan ya musu laifi horo me tsanani suke masa, ya shiga part dinsu ya kwaso kayansa da dan yawa ya fito yana jan trolley dinsa idonsa Jajir ya fito lokacin zan shiga mota zanje Gidan gyaran jiki,tunda na hangoshi nasan ba lfy.

    Su Abbi duk sun leko ta saman Bene suna kallonsa yanda zai kare,Sai suka ga na fito da Sauri har wajen Ameer nace Kanina lfy?Ina zaka je haka? Murmushin karfin Hali ya kakalo tare da cewa Abuja Abbi ya aikeni,wlh ban yarda ba Ameer da gani ba lfy kuma nasan bazai wuce a kan kana shigowa part dinmu suka ce ka bar gidan ba nasan tsab zasu horeka ta haka baka ji maganarsu ba,shuru yayi min,nace haka ne ko? a hankali yace ae hakane Abbi ya kwace aikina da motata, to amma ai iya part dinsu zaka bari tunda gidan ba nasu bane su kadai ko?kai ya daga min gwanin tausayi,nace  muje ga Bedrooms da yawa a part dinmu sai ka Zaba ma fa ka dawo namu,Anty kina ganin ya Aayan zai yarda? Kuri na nayi nace ai sai abinda nace a gidan nan ka kaddara nawa ne ma,Dariya yayi kawai ya biyo ni su Abbi suna kallo ta sama baki bude.

    Muna shiga na bashi Bedroom daya me kyau a kasa Kusa da na su Meenat,yace ki fara fadawa Ya Aayan nace yana Office zan masa waya karka damu,Bari naje gidan gyaran jiki yanzu zan dawo akwai komai a kitchen idan kana so na fita abina na barshi ciki yana Hamdala ga Allah.

    Waya nayiwa Aayan na sanar masa komai yace ba Matsala alfarmarki ce Baby baki da damuwa komai kikayi nasan ba matsala I trust u,kuma nasan Ameer baya shirme irin na sauran na yarda dashi bazai yi abinda zai sabawa Shari'a ba da matata ko wata. murmushi nayi nace na gode.






AsmaBaffa
[1/27, 11:26 AM] Asmabaffa: 🌖🌖🌖🌖
🌖🌖🌖🌖

   KASUWANCI NA






          96-100






Official









AsmaBaffa








    
     MEENAL AMFAL and MMN ADNAN ths page is for u tnx


   MMN AMATULLAH Ina turo gaisuwa me tarin yawa.

 REAL MAMAN WALEEDA jinjina da godiya Littafin yana Sweet yanda kika fara Lfy Allah ya baki ikon gamawa lfy tare da mu masu karatu,Allah ya kara Basira.



    Kuyi Hakuri Fans yan ASMABAFFA FANS CLUB ne suka ce sun bani hutu na kwana biyu weekend na huta ba laifi na bane su suka jawo muku,kuma ko yau suka ce na huta zan huta😅





      Na wuce gidan su Sayyah inda Mum dinta ke koya min yanda ake kula da miji etc sannan ta fara min Gyaran jiki ina shan na tsumi,sai wurin Magrib nayiwa Driver waya yazo daukana muka tafi gida Sayyah sai tsiya take min an kusa gamawa Aayan ya kwashi harka, ina dawowa na Iske Aayan da Ameer suna hira a palo kamar wa da kani na jini da Alama wata muhimmiyar magana sukeyi ta sirri, Ameer yace sannu da zuwa Anty nace yawwa ya hutu,Ya Aayan nace tare da daga masa hannu zan wuce Bedroom ya yafito ni da hannu ina karasawa ya miko ko min kumatu nasan me yake nufi cut nabashi kiss a kumatu na wuce, duk da cewa tunda yayi Tafiya ya dawo bama wani shiri dashi dan Romancing dinma da mukeyi ya daina taba jikina ko da wasa akan nace jikina yake so shine zai nuna min ba jiki na yake so ba,da dare da kyar muke iya bacci Sabo da mun saba idan mun kwanta muna yin abubuwa masu dadi tare da shiga rai,ina ta faman gyaran jiki Amma baya nuna min komai ko irin nayi kyau ko Ya rude a akaina abin yana kona min rai Amma ai ni na jawo.
    Wanka nayi tare da shiryawa cikin wasu arnayen kana nan kayan da ya kawo min daga tafiyar da yayi,nayi kyau na fitar asiri sai Hijab na Sa har kasa Sabo da Ameer,Kitchen na shiga na fara shirya mana abincin Dare kamshin girkina ya cika gidan.

    Ameer kuwa tuni Aayan ya bashi mota guda fyalleliya yana shiga su Abbi sai mamaki sukeyi,Daddy kusan kullum sai naje na gaisar da shi mun sha hira abinmu in ta bashi labarin mu,Sameera yar daba dukansu tare da yaranta an yanke musu hukuncin a gidan kaso na watanni 8 Sabo da Sameera me kudi ce ta basu cin hanci maimakon na shekaru sai na watanni kuma a hakan ma sunce baza suyi 8 mnths ba wata daya ma za a sakesu Sabo cin hancin da ta basu,kasar nan ba gaskiya a cikinta, Aayan kaji wai 8mnths kacal za suyi nace masa ina tura baki,yace Hmm bana son halaka ne da sai na Bada kudin wanda yafi nata a barta a ciki to Allah ya hana cin hanci da me karba da me bayarwa akwai ranar da Allah zaiyi maganinta gaba daya,Amma in kina so a bayar hakan to? Nace ae a bayar kawai dan ubanta ai akan gaskiya ne,a Bada kudin a tabbatar musu da hukunci me tsanani,Kanwata guda da aka bar min Amana nice kamar Uwarsu fa ai wlh Bazan yarda ba da Ammah na da rai kake jin zata yi alfahari dani Na karasa ina zare masa idanu kamar shine Sameeran,Dariya yayi yace to ke mene tunda Allah yasa ta fito lfy? Bazan yarda ba sam kamar kudin ubana haka nake fada Bazan yarda ba dole na tsaya a tabbatar da gaskiya a sharia ka bani kudin Kasuwanci na sai na biya dashi a tabbatar da anci uban Sameera a gidan kaso,yace za a baki tsigai,nace ae a bani kuma dole muje da kai ka wuce gaba ayi komai da kai,yace an gama Uwata, da kansa yaje ya kashe case din ya biya kudi masu mugun yawa aka canjawa su Sameera shekaru Har uku ba tare da nasan anyi ba,sai da ya dawo ya sanar min,nace kash Uku kacal? Laifin Kidnapping tare da niyyar kisan rai? Uku fa ai wlh ba a ci uban Sameera ba sam baza ta koyi darasi ba,sai kace kasar turai da suke da Imani,a Nigeria muke fa inda ba Imani ba a dauki dan Adam da daraja ba,Dariya ya dinga yi to so kike a kasheta wai ko ba a kashe ta ba nafi so ta tsufa a prison,sai gashinta yayi fari tass lokacin na kusa aurar da yan biyun da zan Haifa nan gaba yan mata,Aayan ya bude baki dama har yan biyu kike so ki Haifa?Nace ae Insha'allah su dinga min girki kullum,Aayan yace sai ki dage ki haifo su ai,Wai Ya Aayan ta ina ake Haihuwa kuwa? Yace ta cibi zaki ga ta bude kawai jariri ya fado,dariya nayi nace ba wahala ashe ma.yana ta min dariya yana tunani Allah yasa ya warke ya yi maganin gaba daya.

   Bayan na gama girkin daren nawa Ameer yau bai dawo da wuri ba daga ni sai Aayan muka ci,.  8pm nayi shirin bacci da komai a dakinsa shi kuma naga yana ta cin kwalliya kamar ranar daurin aurensa sai fesa turaruka yake faman yi,nace ina zaka je? Yace wajen yarinyar nan ta Us ce tazo kuma a Hotel ta sauka ba dadi Budurwa kamarta ta zauna a Hotel ai ba mutunci ko kawai zanje dakko ta ne ta zauna damu kafin ta koma.

   Kamar ana zuba min ruwan zafi haka naji a zuciyata,ji nayi kamar zanyi hauka gaba daya hankalina baya jikina Sabo da tsananin kishi,nace idan an Isa Allah ya dau raina yau ba sai gobe ba, nace Wayyo Jama'a ga Kwarto,Ameer ya dawo yana kasa yana juyowa ina ta ihun Kwarto a sama,shi dai yasan Aayan yana gida Amma yace bari ya gani kar ko wani ne daban da Sauri ya karaso Saman yace Anty Mufeeda lfy waye,Aayan ne ya fito cikin shirinsa yace kyaleta jeka kuruciyarta ce ta motsa,Ameer yana dariya yace Ya Aayan kaine kenan Kwarton Aayan yace ae fa gani,Ameer ya juya yayi tafiyarsa yana dariya a ransa yace Mufeeda itama irin yan fulanin garinsu ce kenan,Ni dai ko a jikina na fara kuka yana daukan Agogo zai fita na dakko Jambaki da Sauri na bude shi na dinga shafa masa a rigar ta ko ina na jefar da jambakin na kama rigar na dirje lips dina da ita kalar pink jambaki ga wancen Red,yace kinyi ta banzan dole zanje ya bude kofa kenan na jawo rigarsa ta baya,ina ta uban nishi ina Hawaye,hakan baza ta kaini ba na tsuguna na kwaso kafafunsa Amma ko motsi baiyi ba,sai ya biye min ya tsaya don yaga me zanyi masa tunda Hannunsa nake ta ja da karfi,sai ya biyoni tunanina ni nake jansa ta karfi ina nishi na jawoshi har Jikin Bed,ya tsaya kuwa,nace kwanta to dan Allah kaji ina ta kukana,yaki kwanciya na kara mikewa na danna shi kan Bed ta karfi,nan ma gani nake ai karfi nane ya kwanta sharab,yana kokarin mikewa na fada kansa na kwanta daf daf tare da rufa mana bargo tare nace ka dubi girman Allah ka kwanta,Sabo da me? Aljanune suka ce kar na barka ka fita kana fita zaka samu matsala,a lokacin kuma da Aayan yake son fita lokacin Abbi ya barbada masa Wani garin magani a kofar fita wajen part dinmu suna jira ya taka wajen,mu harga Allah bamu san da wannan ba kishi na ne yasa na hanashi fita.

   Sai da Abbi Sani ya Kira Aayan a waya wai ya fita yanzu ga abokan Daddy nan sunzo duba Daddy daga Abuja kuma karya yake burinsu kawai suga Aayan ya taka maganin kafin gari ya waye,idan har gari ya waye to ya karye maganin ko an taka bazai yi ba,shine suka rasa yanda zasuyi ya fito suka hada abin da Wai Bakin Daddy sun san yanda yake kaunar Daddy dinsa.

     Ta inda Allah ya tsare Aayan sai a ransa yace bari ya tsokaneni yaji shine yace ai wajen wata zaije,ni kuma uwar kishi shine sai da nasan yanda zanyi na hana fitar ta dole,a hankali na kai bakina zan masa kiss yace karki taba ni,why? Kince Sabo da jikinki nake taba ki so na daina taba ki,to Sabo da me kake tabani? Fadi gaskiya naji?  Murmushi ya saki sannan yace Do not judge a person by their looks or the things they have. You do not love some one for their appearance or their nice cloths but because of their personality, their thoughts etc u have to Understand kinji?
   Shuru nayi ina jin dadi yaci gaba Sometimes people don’t tell you how they truly feel about you but they will always show you so pay attention ki gane ba sai ance kullum ana sonki ba kamar yarinya ku yan mata haka kuke.

 Baki na turo tare da cewa ni dai duk da yanzu ina jin turanci kayi min da Hausa yafi shigata sosai kai turancinka na turawa kakeyi duk a harde, murmushi yayi yace Ok ku mata sai kuyi shekara yafi goma tare da mutum yana ta nuna muku yana sonku Amma wai in dai bai ce i love u ba to kawai ba sonku yake ba,wani ma sai ayi ta cewa ai kawana ne,kuma in ka sake kana gani zata auri wani ta barka,sai kace daga baya ina sonki tace me yasa baka fada min da wuri ba bayan duk abubuwan da ka nuna mata na zallar so ne.

   Murmushi nayi nace uhm munfi so muji gar da gar, kumatuna yaja da dan karfi sai da nayi kara sannan yace I LOVE YOU......I DO REALLY LOVE YOU,I NEED U,I LOVE EVERYTHING ABT U,U ARE MY SOULMATE BABYNA ya karasa furtawa tare da hade bakinmu waje daya yana sha,Dadin da nake ji ya wuce a fade shi,nan take na kara kankameshi,naji yana nema ya zarce nace bari nayi fitsari,a hankali ya sakeni na shiga toilet,na kulle tare da jingina da jikin kofar ina sauke numfashi da ajiyar zuciya bakina yaki rufuwa Sabo da murna,dama Sabo da kar ya gano ni yasa na gudo toilet Sabo da nayi murnata ni kadai,harda tsalle da murna ina yarfe hannun dadi,sai da na dade ina murna sannan na hade rai na fito daga toilet irin ko a jikina bana murna, gefensa na kwanta ya kalleni tare da saka hannunsa cikin nawa Baki ce komai ba Baby, akan me fa na furta ina yanga,do u love me too? Yatsina fuska nayi tare da cewa sai nayi tunani na duba naga ko ka dace,Murmushi kawai yayi tare lumshe ido ya jawo ni jikinsa Amma Sabo da iya shege sai na ja baya kadan tare da kwace jikina.

     Shima bai takura min ba ya kyaleni kawai tare da daukan wayarsa dake uban ruri sunan Abbi ne a jiki,sai yanzu ya tuna Abbi ke neman Sa yaje tarbo Bakin Daddy,amma abin mamaki baki daga Abuja su rasa lokacin zuwa sai dare kawai dai yace gani nan yanzu su jirani,Abbi yana ta masifa ka wulakanta mutane Sabo da kai ga me kudi ko to kayi gaggawar fitowa,burinsu ya fito ya taka maganinsu,Ni kawai ban yarda da fitarsa ba kishi nake ko wayo zai min macece da yace daga U.S take,nan take na fashe da kuka ganin ya mike da gaske fita zaiyi, a hankali yace mene ne? Ni..Allah ba inda zaka fita,Indai ka fita Bazan kara tayaka kwana ba kawai baka so na,mirmushinsa me tsada yayi tare da cewa kina jin yanda Abbi ke fada bakin Daddy suna jira na kiyi hakuri naje naga ko su waye mana,Yanzu wasu bakin kirki ne da Dare haka ni Dai Allah baza kaje ba na sani ko wajen budurwarka zaka je.

    Hakura yayi kawai da fita Sabo da yaga da gaske tunanina yana da budurwa gudun Zargi sai yace Ok na fasa to,murna na fara yi tare da kashe wayoyinsa gaba daya na ajiye gefe,shi kuma yana zaune gefen Bed na zagayo ta bayansa tare da Zura hannayena ta cikinsa na rungumeshi gaba daya a jikina,bai san sanda ya lumshe ido ba jin yanda Albarkatun kirjina suka sauka a bayansa,Kasa jurewa yayi ya juyo tare da matsane a kirjinsa gaba daya kamar zai fasa min Kashi, gaba daya ya tafi dani ban san sanda na biye masa ba alhalin nace na daina yarda yana taba min jiki yanzu sai na bashi wahala Amma sai gashi na kasa jurewa,har mamakin kaina nakeyi yanda nake da Feeling me karfi kan Aayan bana jurewa.
   Da Zafi zafi muke Sarrafa juna kowa na nuna kwarewarsa Har Aayan ya dauki Hanyar Cinma burinsa Amma sai kawai sha'awarsa ta tsaya cak ya gagara komai,ni kuwa dama gyaran jikin da nayi nace shike nan na hakura ya samu abinda yake so Sabo da son kudi na bana so nayi asarar kudin gyaran jikina gwara ko mutuwa zanyi kawai ya Mori kudinsa tunda dama danshi nayi gyaran idan ba ayi ba ai na rafka asara tare da bata lokacina.

     Kallonsa nayi da tausayi sosai Sabo da yana da sha'awar abin Amma kuma bazai iya ba wannan Masifa ce,sai dai yayi ta shan wahala,shuru kawai naga yayi ya fada dogon tunani,Nace Man ya akayi ne? Har yau baka warke ba ko? Kai kawai ya daga min,da kyar yace min am so sorry na kasa baki hakkinki shi yasa bana son auren nan,amma kiyi hakuri idan kinga da matsala ko zaki shiga wani Hali tunda ban san ranar warkewa ta ba ki fada min duk da ina sonki nasan da kyar idan zan rayu babu ke zan iya hakura, Hawayen tausayinsa ne ya ziraro min nan take nayi Sauri na rufe masa baki nace karka kara ambata in Bazan iya ba zamu iya rabuwa ka daina ba kai ka daurawa kanka ba Allah ne kuma watarana zaka warke,kayi hakuri itace Kaddararmu ba shi nake so a tare da kai ba wlh ko shekara nawa zakayi a duniya zan iya hakura mu zauna tare,Allah idan har kaji ni Mufeeda nace ka sawwake min ko mu rabu ko zan bar gidan nan abu na farko da zaka min kawai ka kaini gidan malamai masu Rukiyya kawai ba kalau nake Ba ko Aljanu sun shafe ni ko an min asiri kaji na rantse.
   Ka daina damuwa ko kasawa kanka tunani, na gode Baby Na gode yake ta maimaitawa I love u so much My wife,yanzu in naji kince mu rabu ko zaki barni na...da Sauri na karasa ka kaini Ruqiyya wajen Malamai kawai asiri aka yi mana,Dariya yayi kadan tare da kara kankameni a jikinsa.

      Can kuwa su Abbi suna ta faman kiran Aayan a kashe ma wayar,Abbi yace iyyeeeeeee ehhh lallai yaron nan fa ya fara tsallake iyaka dan muna daga kafa ne kawai idan mukayi sake muna jiran Hajja to lokaci zai kure mana,da gani yar iskar matarsa ce ta hanashi fitowa wlh bazai wuce ita bace,Abbi Sani yace dama naga Alama yanzu sai abinda tace Gwara mu fara maganin shegiya,akwai Maganinta Hanifa ko Sajeeda zan bawa aikin su zuba mata a abinci inda da kanta zata bar gidan a nemeta a rasa taje can tayi ta garari a duniya.
   Abbi yayi dariya sannan yace ai har kannenta kar a bari su dawo tunda sun tafi dangin ubansu to su zauna can ko su Bita ita Mufeedan su karata can,da banyi niyyar kulata ba Amma yau ta shiga gonarmu,Washe gari da Safe Saturday Ameer yana Bedroom muma haka na hada mana break na shirya a Dining na koma ina taya Aayan shiryawa Sajeeda ta samu yanda zatayi ta bude kofar ta shigo a hankali tare da kallon gefe da gefe ta tabbatar ba kowa a wajen sannan da Sauri ta karasa saman Dining ta bude duk kalolin abincin dana shirya ko wanne ta barbada garin maganin sannan ta rufe a hankali ta juya zata tafi duf Numfashinta ya dauke na wasu dakiku sakamakon ganin Ameer da tayi tsaye a bayanta ya harde hannaye a kirjinsa,yana mata wani wulakantaccen kallo.

      Nan take jikinta ya fara mazari, ba zato taji mahaukacin Mari ta ko ina,zafi ya hada ta kamar an dosana mata wuta a fuska,Fisgo wata waya yayi ya fara tafkarta yana Ball da ita,tun tana neman agaji har ta garara,ni kuwa munji kamar hayaniya amma hankalinmu bai kawo ba,Ameer ne ya samu Kwalaba ya fasa tayi cako cako ya jawo Sajeeda kiiii har palo ya zauna saman Kujera,Fuskarta ya rike da karfi tare da dagata,tana kuka tana bashi hakuri tasan Ameer bashi da Imani zai iya yankar jikinta da Kwalaba,kamar me aski ya fara karta mata Kwalaba tun daga goshi jini na tsatsafowa,Sai yanzu muka fito nan muka hango irin muguntar da Ameer ke aikatawa,Aayan ne yayi magana da karfi Ameer me ya faru wannan wanne irin rashin Imani ne?

    Gashin Sajeeda ya fisga da karfi tare da cewa confess dan uwarki,nan take Sajeeda tana kuka ta fara tonawa kanta asiri da Abinda Abbi ya sata aikatawa,Ni Mufeeda Salati na fara nace Ameer hada da kirjinta duk ka karce shege a Zane mata ko ina,Aayan yace no..Ameer kyaleta taje mun godewa Allah ma haka tunda ya nuna mana,baki na turo nace ni dai baza a barta ba sai an cire mata farcen kafa na Babban yatsa ta karfi zan tsige shi,Aayan yace ba a nan gidan ba ke tashi ki tafi,tana mikewa na damkota  tare da yarda ta kasa Aiko Sajeeda ta fini karfi kawai sai ta rufeni da Duka sosai na koma neman a taimakeni,Aayan yace au Sajeeda naji tausayinki an barki shine zaki dukar min Mata to na fasa,Sajeeda da fuska duk zanen Kwalaba da jini tace ae din tare da gallawa Aayan Harara kafin ta maida idonta ya kafeta da Mari hagu da dama tare da bude kofa yayi short da ita waje ya maida kofar ya rufe,Ameer yace na fada ma basu da kunya.

    Nace ai wlh sai naci ubanta idan na kamata sai na karya mata hakori sai na tsoma mata yatsa a ruwan zafi, dariya Aayan yayi yace ai tafi karfinki gashi zata ji miki rauni a banza nan nace ai kyaleta nayi kawai Amma mu fada a wajenmu harda na siyarwa dan Babanta. Kwashe abincin nayi gaba daya na juye a leda na kai Dustbin Ameer ya fita dasu waje,haka na dan dafa mana saukakakken abinci abincin mu me dadi muka karya,s ai mita nakeyi na hana kowa sakewa.

    Tunda Hajja da Abbi suka ga abinda aka Yiwa Sajeeda suka shirya Tafiya can kasar Kudu cikin wani kauye wajen Babban sabon bokan da aka basu lbr anyi,
   Har wanda ya basu labarin bokan gaba daya da shi aka shirya yayi musu Rakiya banda Hajja ta dai ce Abbi yayi komai.
   A jirgi suka sauka a Enugu daga nan suka dauki Taxi wai ya kaisu wani daji ko a garin Enugu tsoron bin hanyar Dajin akeyi Sabo da matsafa sunyi yawa a dajin, Driver yayi ta Maza yana Tafiya dasu yana tsoro ko yan yankan kaine,yana Tafiya yana jan tsaki yana Chaiiiiii Alaji,suna jinsa har dai ya kaisu dai dai inda zasu dan shiga dajin da kafa mota ko machine basa shiga sai da kafa,Suka sauka tare da bashi kudi yace Alaji always making juju Money,go and Meet ur Malam is Better than to visit ths land wooo, u have to be very careful with ths place,ahhh see me see troble because of Money so people can do anything in ths world they can even kill them self,Abbi yace Abeg carry ur Wahala and Go stupid Taxi Man,shi dai me Taxi ya figi motarsa bayan ya gama surutunsa.
     Dan cikin dajin suka shiga kadan sannan Me Rakiya yace anzo wajen,Abbi yace ya sunansa kace? Mutumin yace sunansa SHAKYLGANCY sai kace dan India cewar Abbi,ai a india ya koyi har kar nan Alhaji cewar me Rakiya.

     Suna zuwa wajen anyi Ado da komai Red Abbi yace Shakylgancy.....Shakylgancy.....Sai ga Shakylgancy bugul ya bayyana kamar Aljani wani me mummunar suffa,Cikin harshen turanci Abbi ya koro baya nansa,Shakylgancy ya kece da daria sannan yace shima cikin turancinsa yace 1million Amma baza a biyashi sisi ba sai in magani yayi suka ce Shakylgancy baza mu iya dawowa nan ba karbi kudi kawai ko yayi ko baiyi ba karbi kawai zamu dinga contacting dinka a waya idan ta kama dole nayi kokari mu dawo,Shakylgancy ya washe hakoransa tare da wani hancinsa kato kamar tattasai ya karbi kudi yace suje zasu ga aiki.

    Bayan su Abbi sun fito gefen titi tare da Dan Rakiya suna neman Taxi wata mota ta yan Mafiya matsafa ta shararo da gudun tsiya dan Rakiyar su Abbi shine a gefen titi motar na zuwa tayi gaba dashi ta markadeshi a titin fit kansa ya dinga gare gare kamar Ball a saman titi,su Abbi sunyi mutukar firgita shi da Abbi Sani nan suka ga fa an kashe banza motar ko slow down bata yi ba,aiko su Abbi suka take da gudu suma suka mike titi sambal suna ta yi kamar yan tseren gudu basu san sanda suka watsar da takalma tare da babbar rigarsu ba,dama Abbin Sajeeda cewa yayi suje sun wakilceshi shi tsoron zuwa kudu yake yi tunda watarana a Crossriver akasace wani a gaban sa shike nan ya firgita.

     Sai da su Abbi suka yi Nisa sannan suka samu Taxi da kyar ta kaisu Har airport a Hanya suka siyi Sababbin takalma Amma Sabo da rashin Imani ko Jimamin Mutuwar abokin Rakiyar tasu basu yi ba sai Abbi da yayi karfin halin daukan hoton gawar a waya Sabo da ya nunawa iyalansu gashi wancen talaka ne shi da iyalansa Amma an mutu a shirka,nan ba aci ba can ba a ci ba,a kiyaye talaka ka lallaba kanka ka samu a Aljanna.

    Yau ni kuwa shirye shirye mukeyi Su Meenat zasu dawo daga Maiduguri Ameer yafi mu Zumudi wurin Magrib sai gasu kuwa da kaya Niki Niki sun shigo sai murna lokacin Yarima yazo sun finta tare da Aayan,sai hira mukeyi muka ci muka sha,Ameer yace Duk kunfi kyau a Kauyen Rimin Gado har kumatu kuka yi,Meenat tace ai baka kyauta ba tunda ka wani gudo,yana dariya yace tab ina wani zan iya zama a wannan garin toilet ce tashin hankali ana kallonka a waje,ga wata katifa kamar ta jariri,dariya mukayi gaba daya muna haka sai ga Aayan tare da Yarima,Yarima yana ganin Ma'eesha wani sanyi ya fara ratsa shi ita kuwa Ma'eesha kunyarsa takeji kwarjini yake mata wata uwar signa ya mata da ido ai ko Nan take gaban Ma'eesha ya fadi rass Sabo da lokacin Ma'eesha ta cire Ameer dama shakuwace Sabo da yawan mu'amula da sukeyi ganin kuma kamar shi wata mace bata gabansa yasa tace ke Ma'eesha shafawa kanki ruwa,
    Ma'eesha tana Satar kallon Yarima ta gaisheshi ya amsa cike da fara'a, duk ta kasa sukuni ni kuwa ina gefen Aayan nayi shuru na lula tunanin asara da zata hau kaina kwanan nan na gama kashe kudin gyaran jiki mijin bai mora ba,danni a kan ayi asarar kudin nan gwara na kusa mutuwa na farfado kawai.
   a hankali Aayan yace ya akayi? Ya rada min a kunne,ajiyar zuciya na sauke nace kai dai bari kawai asarar kudade nake ta yi kwanan nan,ina ta zuba adashin da ba a dauka,Aayan bai gane me nake nufi ba yace ke na rasa inda kika gado son kudi haka wacce asara kikayi na biya ki? Nace baza ka gane ba a bar zancen Amma ko ka biyani Bazan iya daina tunaninsu ba,tunda har yau me kayan ma bai yabe su ba ko da baki yace kayan nan sunyi sun kuma hadu etc ba a ce min kala ba bare naji dadi da kwarin gwiwar karbar asarar danayi tunda bai samu damar siyan kayan ba.

    Aayan iya tunaninsa ya kasa ganewa me nake nufi wani kuma waye wani?to Business sukeyi? Nan fa kishi ya cika shi tab yasan zata iya indai Mufeeda ce zata iya, Yarima Ya rasa inda zai saka kansa dama yake jira kawai su dan kebe da Ma'eesha ya karbi Number ta kullum cikin tunaninta yakeyi,Sai ko Ya mike yace zan tafi Aayan sai mun hadu,Aayan yace bari na rakaka,a'a zauna ban son Rakiyar Katon Gardi ni Ma'eesha kawata ce zata rakani,Dariya mukayi gaba daya Ameer yace da Alama Ya Yarima girma ya fadi ka fada akan yar wannan yarinyar,Meenat tace Ss1 kawai fa,Ma'eesha ta harari Meenat tace Gwara dai ni ko a hanya duk mutanen kirki ke tareni suce suna so ke kuwa fa Kwaja,Fela etc ku bari na dawo wlh na fasa rufa miki asiri dama kince kar na fada na yarda to na fasa Bari na dawo na baku latest a Maiduguri da Rimin Gado,Ameer dama kadan yake jira yace muna jira Sauri yau wlh komai dare bazan kwanta ba sai naji.

   Aayan yana Dariya yace gaskiya a rufa mata asiri,Meenat tayi mukus tasan yau Tata ta kare,Yarima ya dan jima yana jan Ma'eesha da hira sama sama duk shima akwai ji da kai bai fiya magana ba Number dinta ya karba ya bata tasa sannan ya bata kudi taki karba,babu yanda baiyi ba Amma taki karba nan ta kara birgeshi sosai.
   To yan mata pls a rage nuna zalama wajen Saurayi ko idan kika ga mutum ya fiye yi miki kyauta dan Allah watarana ki dinga jayayya kice baza ki karba ba ko da kina so ki dan dinga kai zuciya nesa sai ki kara birgeshi,sai masu jarabar Rokon Samari abu kawai yan mata Direct kice yi min Kaza ko bani Kaza ko yaushe kuma ba kunya ba komai wlh ba tarbiya ce ba,kina zubarwa kanki mutunci da na iyayenki a dinga daga kafa ana hakuri da yanayi na  Babu ba har ayi ta roke roke ba, ko ina wasu zakiji suna wancen ina ba yar manya bace Bazan iya ba na tsani me roko etc.

     Ma'eesha na dawowa Ameer yace matso nan Hajiyata ki bamu mu musha,Meenat tace Sis Mufee kin gansu ko,Mufeeda tace nima baza kunne nayi yarinya, Babbar banza cewar Aayan,dukan wasa na danyi masa kadan tare da kwanciya a cinyarsa , Ma'eesha tace kai Allah ya bawa Meenat farin jini samari iri iri tun daga Rimin gado yan fulani suka dinga cika kofar gida.

    Farko mun fita siyo pure water muka hadu da wani zai je kiwo da shanunsa ya tare mu yana washe baki idan kun ganshi abin dariya yana busa hayakin wiwi Yace hooai Yan Birni aradu wagga Bingel tana Burgeni, wannan ke nake so ya nuna Meenat tare da cewa Sunana TSITO, nan muka fara dariya jin sunansa Ma'eesha tace in kun ganshi wlh yaci sunansa Tsito wani siriri ne kamar a busheshi gwara Kwaja ma yana da Katon ciki Amma Tsito shi ba dan cikin ma,Meenat tace to Dan Uwarki ai Tsito yafi Kwaja lfy da ganin cikin Kwaja ai na cuta ne,kuma Tsito kyakyawa ne,Ameer yace mu dai ba ruwanmu Tsito muka sani,Ina dariya nace karki kara zagar mana Uwa akan kice dan Uwarki gwara kice dan Ubanki Better,Make min baki Aayan yayi shi Abban shine ba a so ba kyau,baki na turo cike da shagwaba nace da zafi fa...Zan rama ne.

    Ma'eesha tace Daga Tsito kuma sai NA AGWAGWAJI  shi kuwa a yan fulanin ma dan Daba ne duk wanda yaga Meenat tayi masa magana sai ya farfasa masa jiki,Ameer yace kice dan karamin yaki ta hada,Meenat tace Allah ya bani ya zakuyi dani ehe,Dariya muka dinga yi Jin har Dan karamin Saniya Na Agwaji ya bawa Meenat tana can gidan Inna an daureta za a sata cikin Shanu ana kiwata mata ita,Nace Business Sabo Sarkin Kasuwanci cewar Aayan jin yanda nake ta murna Meenat ta samo Saniya zata girma ta Haifo yayanta.
    Ma'eesha tace Arzikin Meenat bai tsaya a nan ba kullum samarinta suna hanyar kawo mana kaji da zabbi muna yankawa mu sha farfesu iri iri,Na ciji yatsa nace me yasa kika cinye a ciki banzaye maimakon ku siyar ku tara kudin ku kawo min ko dankunnen Gold na siya muku dan karami,Aayan ya kalleni baki bude yace da kudin kajin? Nace of Course.

   Ameer yace inye to wannan buhun kayan naku fa? Ma'eesha tace duk Samarin kauye ne suka tara mana su danyar Gyada,gero,wake etc,A Maiduguri kuwa samarin Meenat harda Conductors na mota,yan Napep etc me dubu daya me dubu biyu haka muka cinye musu kudi,Nace to ke kuma fa in haka ne kece me bakin jini,Meenat tace tsakani da Allah duk wani me kudi indai kinga rantsatsiyar mota ta tsaya to ba shakka wajen Ma'eesha aka zo zance,ni dai Meenat ina ga asiri akayi min daga me kaji sai me Saniya,gyada da gero tare dasu waken Suya hhhh muka dinga dariya,Aayan yace sorry Sis zaki samu wanda yafi kowa kudi kuma na gari kema,ni kuwa nace Meenat haka Allah yake lamarinsa ni kam Ruwa ta sha aradu,Rankwashi Aayan ya zuba min,Ameer yace ni wlh ji nayi gwara haka ita ba iyayi ba dama Allah yasan manufar jaki shi yasa ya hanashi kaho.

     Meenat ta gaji da abinda Ameer yake mata ta mike cike da shagwaba tayi kansa wai zata kwala masa spoon ya mike suka fara zagaya mu a palon muna zaune, sai da na gaji nace Meenat kun damemu can u stop ths Nonsense pls? Meenat tace ai kuna jinsa abinda yake ce min kun kasa yi masa fada,Maeesha ce abar duka ai ba Ameer ba tunda ita ta fada mana,Haushi Meenat taji ta jefar da spoon din tayi Bedroom abinta .

    








AsmaBaffa
[1/28, 10:00 PM] Asmabaffa: 🌖🌖🌖🌖
🌖🌖🌖🌖

   KASUWANCI NA







          101-102








Official









By
AsmaBaffa







   
         Mun dan jima muna hira bayan tafiyar Meenat sannan na mike nabi bayan Meenat Bedroom dinsu,Maeesha ma ta shigo,Ameer ma ya tafi shirin bacci,Aayan yana samansa jirana yakeyi nazo mu kwanta,Ni kuwa yau dakin su Meenat nake son kwana Sabo da musha hira ta ganin juna,Meenat tace ban gane ba?Ya zaki zo nan ki Kwanta mana mijinki fa?Nace hira zamuyi,Maeesha tace shike nan mun shiga Uku Meenat baza muyi bacci ba yau,Meenat dariya tayi hmm ai mijinta zan kira mata idan mun gaji,ina kallo sukayi shirin bacci nima na mike na feso wanka na shafa turarukan kamshi iri iri sannan na kwanta gefe,Maeesha tace wai Mufee har yau baki ciki ba? Gaskiya ya kamata ace kina da cikin Aayan,baki na tabe tare da cewa mu ba yan iska bane a kujera yake kwana ina Bed,dariya sukayi Ma'eesha ta kalle ni lallai Sis maida Karuwa yar Iska ni mamakina Banga kinyi rashin ko yar lfy ta first night ba,nima kullum zura ido nake Amma ai nasan tuni Su Mufee an san kan harkar Cewar Meenat, zanci ubanki wlh ni sa'arku ce wai dan kunga kunyi saurin girma,so kuke ko me na kwashe na fada muku? Meenat tace mu ina muka Isa daukan wannan maganganu na manya ki rike abinki dama shawara zamu baki munga ko kamar Aayan yana da matsala ne shine muka samo mafita a Maiduguri.

    Masifa na fara wacce mafita uban wa yace muku mijina nada matsala idan banda ta Family nifa bana son Sa ido Meenat ku kiyayeni,Allah baki hakuri ai gani mukayi mu da ke duk daya ne ba wanda ke boye maganar dake damunsa yaushe Mama Mufee ta dawo mana haka bamu sani ba bayan Ammah ta bar mana wasiya rike zumuncinmu,yau miji yafi mu daraja shike nan.
   Jikina yayi sanyi nan nace ai kune wlh bakwa ji sam Amma akwai matsala Meenat,lokacin Aayan yana can yana ta faman jira nazo muyi baccin mu Amma shuru shuru sai tsaki yake faman ja yana juyi.

    hannun Meenat na rike muna kwance nace Meenat kuji ni ina cikin neman taimako na addua Asara ta hauni,na tafka babbar asara,jikina da kyauna duk nema yake ya kare a banza,jibi uban Hips dina,kalli tun ina karama Allah ya hore min na shanu masu kyau da birgewa,kalli skin dinmu,amma a haka aka ce idan kana da kyau ka kara da wanka kalli yanda nake zabga uwar kwalliyar da shiga iri iri a gidan nan,yanda nake kashewa jikina kudi bai tsaya a nan ba sai da na dangana ga zuwa gidan gyaran jiki na biya makudan kudi an tsunami nasha an gyara skin,lungu da Sako anyi masa filla filla Amma ku kanku da kallona kun san na kara kyau da canjawa,kalli yanda nake sheki da walwali,kalli yanda nake kamshi ko abu na rike sai ya tafi da kamshi na,kalli ku kanku yanda kuka rude da kyauna gashi komai ya kara cika duk da cewa kun sanni Amma sai da kuka Koka yanda nake sheki da uban kyau,

   Meenat tace mun gane,to asarar tayi muni da kashe kudina yayi yawa Amma kun san Aayan asiri na jikinsa har yau bai warke ba,bazai iya komai ba sai tabe tabe,kinga ko ba komai Sabo da lafiyarmu ma ya dace ace an daina taso da sha'awa kuma taki kwanciya,kamata yayi ace mijina yana alfahari dani kamar ko wacce mace,amma ni kaina nake zargi ko nice ban iya yanda zansa yayi amfani dani ba,bayan wannan asarar kudin gyaran jiki so nake nima ace kwalliya ta biya kudin sabulu ace mijina yana yabo na yana susucewa a kaina,amma ace ina sheka Ado bana ganin ya zauce ina kanta.
   Dariya Ma'eesha tayi tare da cewa wlh ya susuce kece bakya ganewa kinga yanda yake binki da uban kallo duk inda kika Gilma,kuma kin gama zautar da shi,bakya ganin yanda yake kishinki me kike so kuma? Meenat tace akwai matsala ace mijinka bazai biya bukatarsa da kai ba,kuma ribar soyayya da aure a hayayyafa,to ki kwantar da hankalinki kinga Wani Saurayina a Maiduguri dan gidan gawurtaccen malamin Sunna ne Malamine na Sunna basa tsafi ko shirka addua zasu baka kayi suma su tayaka kuma ba kwandalarku ana dacewa,Maeesha kin tuna Masa'udu Shekare wanda akace yayi shekara da shekaru a Cikin Uwarsa kwantacce kafin a haifeshi? Wanda ke zuwa kusan kullum yana damun mu da Fassarar Hadisai? Ma'eesha tayi dari tare da cewa au wai Shekarau kike nufi? Dalla Shekare yake ba Shekarau ba,ae gaskiya ne kam malamai ne,ni kuwa nayi tsalle na dire cewar Bazan tonawa mijina asiri ba gaskiya,Meenat tace to kin gwammace ya zauna da cutar wani abun sai ana fada ake samun mafita,ai ba wanda yafi karfin cuta a duniya ba a kunya a cuta gwara a daure a fada muji shawara ina da Number su,kinga ko a nan talaka cikin Samarin za suyi rana,shi yasa ba a raina dan Adam kowa da ranarsa kuma da baiwarsa,nace haka ne Meenat Allah ya kaimu gobe sai a kirashi.

    Da haka muka fara baccinmu bilhakki,Aayan yana can yana fama da rashina,sai faman jirana yakeyi har ya gaji da latsa waya da laptop ya mike nan take ya sakko kasa tare da nufo dakin su Meenat,Yana zuwa knocking ya shiga yi yaji shuru sai da kyar Meenat ta farka taji tsoro ko abin cutarwa ne tace Mufee ku tashi yan Fashi ne,Da Sauri na fada lungun Bed nayi flat,Maeesha ta fado kaina itama,Meenat ta mike tare da bude sip ta shige ciki ta dunkule waje daya,jikinmu na rawa gashi sai bugawa akeyi,Da kyar nace waye? Nine naji Muryar Aayan,Nan Naja tsaki ina tsinewa Meenat dake fitowa daga Cikin Sip,Maeesha tace Amma kin cuce mu saura kadan hawan jini ya kamamu,a hankali na bude kofar kawai naji yayi sama dani ya tura kofar da kafa ya daukeni kamar Jaririya haka muka je har Bedroom dinsa, nace me ya faru muna baccinmu wlh ka Tsorata mu,Murmushi yayi tare da cewa akwai wani babbar kyauta da zan miki amma ba yanzu ba,tunanina kudi ne na fara Murna nace sai yaushe? Hararar wasa ya min tare da cewa nasan kyautar tafi kudi tafi komai na duniya a wajenki Amma sai ranar nima da nake cikin nishadi wanda soon nake Sa rai,a kirji na cijeshi kadan tare da cewa Allah ai ni babu abinda yafi kudi a wajena a yanzu ko mene shi tunda ba kudi bane na daina murna.

     Murmushi yayi me sauti tare da cewa wannan kayan baccin fa? Karki kara Sa min su sunyi nauyi da yawa gashi sun matseki sosai Bazan iya ciresu da wuri ba,Ai yau banyi niyyar kwana nan ba dumin yan uwana nake ji, a kunne ya rada min pls ciresu ni ki daina Sa su bana sonsu kawai,suna miki kyau Amma wahalar cirewa zasuyi harda wani Wando me tsayi fa, kunya nake ji bana son na cire sai na daga zan cire sai na fasa shi kuma ya kafe ni da ido yana faman kallon kirjina tun kafin na cire ma,nace ka kashe light to na karasa a shagwabe kamar zanyi kuka,Kara wani kishingidewa yayi kamar Sarki yana kallona dai dai tare da murmushi,a hankali naji muryarsa yace Babyna kin san me? Nace a'a sai ka fada yace Kinfi kowa kyau a duniya wanda na taba gani komai kin hada Allah ya baki,Murmushi kawai nayi nace hmm tun baka je Palace din ba kenan ka gano haka,Baki ya bude dan baiyi tunanin nasan harkar ba ma,idona na rufe ina dariya hannuwa na biyun ya rike kam yana kare min kallo harda wata Palace da ake zuwa dama? Nace uhm am just kidding u fa,Sai kin fada min naji,Nace to kaima ka sani ai Kingdom kenan ai me matakan tsaro,au wani sunan ne wannan? Nace ai Baza ka gane ba sai ka tsallake border Amma ai kaima yaron ne tunda ba sani kayi ba sai lbr kamar ni.

   Ido ya dan ware kadan tare da cewa bacci nake ji pls cire  kayan mu kwanta,jikinsa na kalla daga shi sai Boxers dan gutsul,Haka cike da kunya na fara zare rigar tun kafin na zare ya fara Murza Albarkatun Kirjina.

      Abbi an dawo ana jiran Boka Shakylgancy ya aikata Aiko sai waya da sukeyi,Cikin dare Boka ya Cillo tsafinsa zuwa jikin Mufeeda sai akayi dace Aayan yasa munyi wankan tsarki don shi ba a ko kara 1hr da najasa a jiki ko na Sunna ne,Yace to Ki daure muna Nafeela ko raka'a biyu ne duk dare mu daina bacci ,Mufee ba musu na bi bayansa muka fara Nafeela,lokacin Boka yana ta jefo tsafinsa baya Tafiya,ya buga ya buga shuru,bayan mun idar sai da sukayi dogon Azkhar lokacin boka yana ta faman jefo bala'insa Amma shuru,Har ya hakura yace sai gobe zai kara yi.
   Washe gari da sassafe ya fara tsafin irin ko muna baccin Safe kawai lokacin nan ma azhkar mukeyi na Safiya,da rana bai samu nasara ba lokacin karatun Qur'ani Meenat take kara min,yamma ya gama shiri tsab lokacin kuma Azhkar na yamma nakeyi zuwa Magrib,still daga Magrib zuwa Isha duk bashi da sa'a.
    Kwana na biyun kuwa na fara period Amma ko yaushe ina da Alwala,ga addua a bakina har kitchen ni ba wake wake nakeyi ba sai addua nan ma boka ba labari,lokacin kuma mun kira Saurayin Meenat Shekare ya hada mu da babansa na bashi labarin komai nan Malamin ya bamu adduoi ta waya da yanda zamu yisu, na fara ma yau kuma Ma'eesha ta tuna min zamu je gidan kawarsu ana bikin yayarta,haka na damu Aayan ya barni naje da kyar ya yarda yace Amma sai daí Ameer ya kaimu,Haka muka ci uban kwalliya bana cikin sahun matan aure,a gaban Aayan sai nasa Katon gyale Amma muna shiga mota na cire gyalen na ajiye a bayan motar Ameer gashina na saki jelarsa,abinda mata keyi yanzu kenan Ba a gane wace matar aure,nima sai na birge kawai,muka je Dinner wurin 9pm ana ta rawa da kade kade,Har wurin 11pm muna ciki ana cashewa na manta da wata addua ma gashi nasan mijina bai so a kalle masa ni,amma na zalunceshi bai sani ba na bari Maza na kalle min sura tare da gashina wanda nasa ne shi kadai Allah ya halitta masa,tunanina na masa wayo ban san kaina nayiwa ba,har shiga filin rawa nake muna gogaggaya da matan manya kowa ya ganni yasan matar hamshaki ce ni ko yar gidan wani ce yanda nake zubar da Naira.
     Abin haushi Boka shi aikinsa yakeyi dama aikinsa ne kullum ta nan yake samun kudinsa kamar yana Office ne,kuma basa saurarawa kullum aiki sukeyi suna gwada sa'arsu ko zasu samu wata dama daya tak su samu nasara musamman yare da zaka ga sunfi Musulmin bahaushe Amana basa karya alkawari.
    Wufff Ya turo min Aljani ta tsafinsu yana zuwa yaga na shagala ya samu dama nan yayi wuf zai shigeni Amma ba ta inda zai iya shiga jikina da wuri ai tuni ya ankara cewar Gashina gashi nan a waje nan fa yayi wuf ya bi ta gashin ya shiga jikina,nan take naji kaina ya fara ciwo sosai sai nayi tunanin ko Gajiya ce,kawai nace suzo mu tafi,haka muka dawo gida ina fama da ciwon kai me tsananin gaske kamar kaina zai tarwatse,na fara Hawaye na samu Aayan a daki yana jirana yana ganina haka yace mene lfy?,nace kaina ciwo kin gani ko sai da nace karki je kika ki yarda,zo ki kwanta na baki magani,kafada na make tare da cewa Bazan sha ruwan gidan nan ba,indai ruwane na gidan nan Bazan sha ba,Aayan ya zata tsokanarsa nakeyi yayi dariya yace kwanta,nace na rantse Da Allah me Rahma in na kwanta a gidan nan yau Allah ya tsine min albarka,bude baki yayi yaga fa da gaske ne dan ba alamar wasa a tare dani,yace to ina zaki kwana nace wani gidan Amma ba wannan ba,kaina na dafe nace wlh ni a fitar dani daga gidan nan idan na zauna a gidan nan shegiya nake,wlh in dai na kara kwana a gidan nan Allah ya tsine min albarka wannan tsinannen gidan dukka ma tsinannu ne ku yan gidan,Aayan ba a kanta ya fara ganin hakan ba tunda Mommynsa tayi da suka mata asiri haka matarsa Nafisa tayi itama da Ruky, Amma ai munyi alkawari dake baza ki bar gidan nan ba,Alkawari? Amma ka cuceni Allah ya Isa me zanci da wannan gidan,nan na sauka kasa da gudu na fara hado kaya ta ko ina,nace Meenat ku tashi mu tafi,sis lfy? Zanci kutmar ubanku dan uwarku dan ubanku ku tashi mu tafi wlh idan baza ku taho ba ku zauna,Ba yanda su Meenat basuyi dani ba Amma zagi kawai suke sha iri iri,haka Ma'eesha tace mu Bita Meenat kar a samu matsala ta fada hannun bana kirki ba,haka suka kwashi akwati har Uku,Aayan tuni ya fito ya nemi Ameer ya kora masa bayani,nan Ameer yace shawara ka bawa Meenat key din Wani gidan naka can daban sai na kaisu can su zauna,Haka Aayan a gigice ya mika masa yace kuje dayar sabuwar GRA ka gane gida Dana siya last wk pls ko me Mufee na take so a bata, kar ka dawo gidan nan ku zauna ka kula dasu kafin nazo,Ameer yanda yaga Aayan ya fita daga hayyacinsa gaba daya abin ya bashi tausayi kamar ya masa kuka ya ma rasa me zaiyi gaba daya baya hayyacinsa za a rabashi da Mufee dinsa wayyoo.

    Yana gani Yanda Mufee ta gigice sai gumi take hadawa ta fita da gudu har Jikin mota hakanma da kyar Ameer ya lallaba ta hau motar tasa cewa tayi in dai motar ta gidan ce baza ta hau ba,Aayan ya Kira Meenat da suke kuka ganin abinda Mufee keyi ya zarta hankali,kwantar musu da hankali yayi tare da cewa karku kara kuka kinji ko,kai kawai Meenat ta daga Masa Kudi ya mika mata masu yawa yace rike zanzo ltr kuyi amfani dashi.
   Meenat ta karba ta fada Mota suka tafi,Abbi yana Saman Bene yana dariyar mugunta dan sunyi waya da boka,Aayan Innalillahi yake maimatawa kawai sai Hawaye sharrrr ya kwararo masa da kyar ya lallaba kansa ya mike,ya fito a fusace fuuuu sashen Abbi ya farayi yana shiga ya shaki wuyan Abbi ya bugashi da Bango nan take idon Abbi ya firfito ya shakeshi iya Shaka sai kakari yakeyi,su Haneefa suka fara ihu nan fa su Hajja da kowa ya hallara ana kokarin cire Aayan Amma an kasa Abbi na neman shekawa Lahira,Hajja ta fashe da kuruwa za a kashe mata da ta fara Dukan Aayan,Aayan ya make Hajja ta fadi kasa dabar yace wlh akan a taba Mufee gwara kowa ya mutu a gidan nan bana ubanku bane,ku bar min gida, nan ya saki Abbi ya shiga daki daki yana watso musu kaya tun daga Sama zuwa kasa komai nasu jefowa yakeyi,nan take yace Duk na kwace aikinku kar na kara ganin kowa cikin ku a Company na kuma duk dukiyar bata Daddy bace bare kuce dan uwanku idan baku sani ba ku tambaya kuji kudina nane dukiyata ce gaba daya,Nan fa suka rude harda Hajja sun san tasu kuma ta kare yace wlh wlh ko mota daya baza ku fita da ita ba,nan take yace na baku 15mnt ku bar gidan nan,Nan ya Kira Sojoji har mota biyar suka zo da igwa ta feshin ruwan zafi tafashashe,ba shiri suka tattara kayan da zasu iya dauka na sawa suka fara fita manya da Yara daya bayan daya Maza da mata suna kayi hakuri mun tuba zamu karya asirin,Aayan yasan karya sukeyi kawai yasa Sojoji suka rakasu kaf suka bar gidan,Abbine bai fita ba wai zaiga Daddy haka Hajja ma tace dole zamuyi magana da Dana ehe,nan ma Aayan yasan so take Daddy ya tursasa shi dole ya Barsu kawai yace ba inda zasu Sojoji suka tasa keyarsu sai da suka hau Taxi har guda hudu sannan Aayan ya sallami Sojojin ya koma part din Daddy.

    Tunda Daddy ya ganshi gabansa ya fadi yasan ba lfy ba,Gefen Bed din ya dire gwiwoyinsa tare da daura kansa saman Bed din da Daddy ke kwance ya fashe da wani kuka me tsuma zuciya,Daddy ma tunda yaga Aayan yau yana kuka haka to matsala ta afku babba ma kuwa,a hankali yace me ya faru ne My Son? Nan Aayan ya sanarwa Daddy komai,Daddy murna ya fara yi Aayan yanzu yana son matarsa,amma bai ji dadin abinda ya Samu Mufee ba Amma yasan Allah na nan kuma da saninsa, Daddy ne ya kalleshi be a Man Aayan kamar mace ba abinda zai faru Insha'allah muna addua karka damu nan Daddy ya shiga lallashinsa sosai yana kwantar masa da hankali har ya hakura yace Daddy bari a rufe gidan nan kawai mu koma wancen,sai lokacin Daddy ya san Aayan ya kori duka danginsa har Hajja mahaifiyarsa,fada ba irin wanda baiwa Aayan ba ko ba komai ai Uwa Uwa ce sai na bita zan shiga Aljanna,Aayan yace ai zan dawo dasu Amma ka kyalesu Daddy su dandana wahalar,shi dai Daddy masifa ya dinga yi Amma Aayan yayi mursisi dashi haka yasa masu kula da Daddy suka daukeshi har mota suka koma sabon rantsatsen gidan Aayan wanda su Meenat ke ciki yanzu,ni kuwa sai da muka fito daga gidan hankalina ya dawo jikina,sannan na samu nutsuwa ko ciwon kai bana ji sai ma hira data barke a tsakaninmu dasu Ameer.
    Gaskiya gidan ya hadu fadar kyansa da haduwarsa bata lokaci ne,nan Ameer ya zabi Bedroom,haka su Meenat ma,nima sai da na zabi nawa sai yanzu nake tunanin ina mijina Aayan ina ya shiga? Ameer banga Aayan ba lfy? Ameer yace yana nan yanzu zai dawo unguwa yaje,nace Ok to Amma bai fada min ba,Ameer ne ya shige Room ya Kira Aayan yana sanar masa me nace murna Aayan ya farayi yace gamu nan zamu karaso,Aayan suna karasowa yasa suka kai Daddy can part dinsa daban tare da abincinsu gaba daya sannan ya wuce Direct part din da muke gidan baya bukatar gyara ko ina fes yake Sabo da ma'aikata ne ke yi kullum,wanka nayi da ruwa me zafi daga ni sai towel na gama shafa turaruka na masu azabar kamshi ina taje gashina cike nake da tunanin ina Mijina ya boye,ina haka sai ji nayi an rungumeni ta baya wani shock naji da ban taba jin irinsa ba a duniya, da Sauri na juyo tare da rungume Aayan a jikina ina kare masa kallo yanda duk ya wani hargitse me ya faru Muka dawo nan gidan My Man? Kallona yayi yace kece kika ce bakya son wancen sai na canja mana nan,na cika da mamaki sosai Hawaye ya zubo min sharrr,A hankali ya girgiza min kai tare da kawo fuskarsa saitin tawa sannan ya fara lashe min Hawayena da suka ki tsayawa,saki na yayi ya shiga toilet da Sauri,ni kuwa ina nan tsaye inda ya barni ina Hawaye har yayi wanka da Komai ya fito da towel yana goge jikinsa,Sai da ya gama feshe feshen turarukansa tare da shafa Lotion sannan yasa Boxers still ina tsaye ina ajiyar zuciya na Kukan da nayi,Har gabana ya karaso sannan ya tsaya kamar zai shiga jikina a hankali cike da nutsuwa ya hade hancinmu waje daya yana gogawa a hankali ya ciji kunnena kadan,nayi yar kara tare da murmushi kadan yanda nake jin sha'awar yau ta wuce hankali ban taba jin irinta ba ban san dalili ba,shima a wajen Aayan hakan take Amma yasan ba lafiyayye bane,Bakinmu ya hade waje daya kalar numfashin da muke fitarwa ya zarta hankali,a hankali ya zare min Towel dina tare da jefar dashi gefe ba tare da na sani ba sabo da dadi, Saman Bed ya daura ni shima ya kwanta yana min abubuwa masu rikita tunani yau a Romancing dinmu yafi na kullum da mukeyi mun kasance cikin Nishadi da jin dadi, yanda Aayan ke Surutai ka rantse babbar Harka ake bugawa,cikin kalamansa yace My  wife pls love me, say u Love me,do u love me?,sabo da na tsokaneshi nace a'a ni dai,cik ya tsaya da tsotson albarkatun kirji na tare da shafasu,why Baby nan da nan naga ya birkice min,cike da shagwaba kamar zan narke nace ai baka so na tunda ko yabona bana ji kana yi,kuma ma ai ni baka lallaba ni kana ji dani kamar kwai,duk ba wannan ne zai hanaki so na ba sweetheart,Tunda bakya so na Bazan miki dole ba yana gama fadar haka ya mike zai bar saman Bed din, na riko hannunsa ya dawo saman Bed tare da cewa da cewa Lfy? Bana so na takura miki ne, a hankali na kara bakina a saitin kunnensa tare da cewa I love u My Man nayi shuru tare da rufe fuska da tafukan hannuna.

    Cike da farin ciki kamar an masa Bushara da Gidan Aljanna yace Are u serious Baby?yeah My Man,harshena kawai naji ya cafko yana aika min da sakonni masu zafi nima na shiga maida mishi da martani,kukan dadi kawai mukeyi abin ba a cewa komai Haushi nake ji nayi asarar kudina na gyaran jiki nasan bazai iya yi min komai ba, nace Allah ya baka lfy My Man banyi tunanin yaji ba ashe yaji a kunnensa,nan take ya shiga neman Hanyarsa ni kuwa na saki ma jiki bazai iya ba tunda bashi da lfy sai dai naga yau yanayinsa daban yake da kowanne,a hankali yace kin shirya Mufee na? Murmushi nayi da kyar nasan bazai yuwu ba nace why not am Ready, wani Radadi naji marar misaltuwa a kasa na kamar an zuba min Attaruhu a Cikin gabana,cike da Rauni nace wayyo....Allah....zafi.....Amma Aayan baya gane me nakeyi gaba daya aiki yake yi bilhakki,sambatu da Kukan Dadi kawai yake min iri iri wanda ni Sabo da zafi bana kulashi Amma kuma banyi kuka ba,har naga an kwashe lokaci me tsawo yana aikinsa bai gaji ba,kamar raina zai fita haka nake ji,sai da ya dade Sabo da gwarzontaka kuma shima yasha wahala yaune na farkonsa, sai da ya kawo sannan ya wani ki zare jikinsa wai a kasance a haka har abada kawai ya kwanta a kaina da zafi da wahala gashi a jikina ya kwanta,sai da ya huta sosai sannan ya zare jikinsa ya koma saman Bed ya kwanta sai kuma naga ya kara dawowa ya makale a jikina,Aayan yafi mace son jiki,sai murna yakeyi ya rasa inda zai Sa kansa yace ashe alheri ne da muka bar gidan can? Sannu Babyna Allah miki albarka na wahalar dake gashi ban san zamuyi ba ko sallah bamuyi Nafeela ba ta Sunna,amma tunda nayi addua ai ba komai ko Ya karasa yana kallona Sabo da ya kunna haske,nace uhm shike nan dai ai za muyi ltr,amma kin bani mamaki Mufee na bakiyi kuka ba sannan duk kin jure wahalar da karfina,a hankali nace kwalliya ta biya kudin sabulu yanzu banyi asarar kudina ba,ai dama ni asarar kudin ce bana so ayi,kuma gashi kaji dadi Alhmdllh Allah yasa ka warke gaba daya,kasana ya kalla har jini yake Sabo da raunin da yaji min gashi farkon mu ne,yace Bari muyi wanka nace to Amma kaji dadi? Babban yatsanta ya daga min tare da cewa babu wacce za a samu kamarki Baby ni a wajena Bazan ma samu ba,,ai kinga yanda na zauce ke dai bari ba a magana,ni kadai nasan kyautar da zan miki,duk zafin da nakeji sai da nace kudi? Yace ae harda abinda yafi kudi na washe baki nace kayan dadi ne? Yace ae harda su kullum daga yau zaki samu,ban gane ba nace tam Allah ya kaimu zanji dadina,wani kallo yake bina dashi na musamman wanda sai kin cika mace Namiji zai yi miki irinsa,Na daure nace ya dai? Yace  Carkwai matsagwai sarkin dadi,Allah ya taimaki Mufee,Allah ya taya miki,Allah ya rika miki kuma Allah yaja zamaninki Mufeedan Ammah Amma yanzu ta Aayan ce,ban san sanda na fara sheka dariya ba yanda yake ta yi min kirari harda daga hannu kamar yana gaban Sarki, kamar ba Aayan ba ban taba sanin haka yake ba sai yau.

     A raina sai dadi nake ji yanda naga Aayan ya wani rude ya gigice sai tarairayata yake kamar zai cinye ni,a raina nace dole na ci gaba da bashi hadin kai yana nuna min so haka,dauka na yayi da kyar na bari ya gasa ni sosai sai shagwaba nake masa har yayi min wankan Sabulu nayi na tsarki shima yayi ya dauko ni muka fito,take away din daya shigo dasu dazu ya bude mana kaji gasassu sun sha hadi,ga kayan sha iri iri ya hada min ruwan tea me kauri,bayan mun shirya jikinmu Sallar Nafeela mukayi tare da addua tunda dazu bamu yi ba,sannan nace yunwa,zaman ma da nakeyi sai da dabara da kansa yayi Feeding dina naci na koshi shima haka,Brush mukayi sannan muka kwanta nan ma yaso yayi kari da kyar na lallabashi sai gobe da sassafe,bacci ya kwashe ni shi kuwa farin ciki da murna da kyar ya samu yin bacci yana tunanin me zai min a duniya ya faranta min.

    Abinda ya jawo Aayan ya warke shine asirin dasu Abbi suka masa a wancan gidan sukayi sun haka rami suka binne,shi yasa malamin nasu yace bazai masa tasiri ba sai in yana wancan gidan,amma idan baya wancan gidan sha'awa ta motsa masa me karfi to zai iya saduwa da matarsa,shi yasa suka zuga Hajja kan Aayan ya dawo su zauna tare,duk kuma matan nasa dama bai gwada saduwa da su ba sai niyyar ya fara kuma aka samu akasi,yanzu sun manta da hakan burinsu su raba Ni da gidan tare da kannena sai gashi ta wani bangaren Ashe alkhairi ne.
 
    Hajja basu tsaya ko ina ba sai gidan Abbi dake Na'ibawa can cikin yorubawa dake zaune a unguwar,gidan kuma karami ne rashin dabara yasa suka kasa yima kansu planning su mallaki gidaje,motoci etc gaba daya sai suka dogara da Arzikin Daddy suna ganin babu abinda zai Sa a raba su da wannan katafaren gida,Abbi ne kadai yayi karfin Halin siyen karamin gida a Na'ibawa gidan kuma ba wani babba bane ba kuma me kyau bane can,gashi duk Aayan ya kwace motocinsa,Sai Gold din matansu kawai da suka mallaka gashi basu da aikinyi,Khaleel da Mujaheed suka ja tsaki tare da cewa Ameer yayiwa kansa gata gashi yana can cikin daula. Abbi da yan uwansa sai bige bigen waya suke yi,haka Haneefa dasu Sajeeda sai hararar Hajja suke kan wai dole ta tursasa Daddy ya dawo dasu,Hajja tace gobe zamu koma Insha'allah Allah zamu je mu sameshi dole zai barmu.
    Hajja bata san basa gidan ba sun barshi kuma basu san sabon gidan da suka koma ba,g ashi duk wayoyin basa shiga .











AsmaBaffa
[1/30, 1:28 PM] Asmabaffa: 🌖🌖🌖🌖
🌖🌖🌖🌖

   KASUWANCI NA






          103-104







Official









By
AsmaBaffa






         Kai Fans Masoya wannan Novel nawa sunyi yawa wai wa zan bawa page ne ma a cikinku ko wanne Gp gaku nan da yawa,ina Godiya fans dina wlh ina matukar jin dadi kuna birgeni.
     Kuma ina rokonku dan Allah ko wata tayi min magana taga banyi reply da wuri ba,ko ta kira ban dauka ba dan Allah ayi min Uzuri ba yanga bace kuma ba wai wani abu bane sai in bana kusa ko ina wasu aikin,sannan Dan Adam ajizi ne a dinga hakuri da Halina,ko a gp za ayi comment aga banyi magana ba ayi min Uzuri kwana nan bani da time sosai ne.love u all.


    Wannan page kacokan na yan albarka ne YAN NIGER naku ne Masoya na yan Niger band yan Nigeria.😅



 






       Koda gari ya waye da kyar Aayan ya iya fara farkawa ya lallaba yayi alwala ya fara Sallah ya idar azhkar din ma kadan yayi ya koma ya kwanta kawai tare da kara kallona yana murmushi nan take ya kara makaleni a jikinsa sai baccinsa, jin laushin jikinsa yasa nayi mika tare da kara shigewa jikinsa harda Kukan shagwaba shi kuma yana wani jijjigani kamar Jaririya,haka har bacci ya sace shi again,bacci muke ba ji ba gani.

    Meenat tace Ma'eesha abin nan na Mufeeda na lfy ne kuwa? Kema kya fada gashi har mun gyara ko ina yan aiki har sun gama nasu suma sunyi gaba,Ameer da Alama yunwa yake ji muna ta jira muji me zamu dafa kin santa sai tace mijinta baya ci sai an sake wani kalar,Meenat tana dariya tace muje muyi iya namu kawai,Suna kitchen sai ga Ameer ya fito a birkice daga gym yake ya motsa jiki sosai kamar zai fadi Sabo da yunwa,gashi bai iya shan fresh milk ba Amai take sashi idan ya sha da Safe,
    Gefen Meenat ya tsaya tare da cewa ya akayi ne ta Tsito?  Harara Meenat ta aika masa,Maeesha bata ma san me suke ba tana can tana fama da tunanin Handsome Yarima da yake kasheta da kalamai masu dadi ita kadai take murmushinta.
    Meenat tace Ameer da kasan kyau irin na Tsito da baka yi magana ba,Ameer ya tabe baki tare da cewa ai dai nasan kaf kauyen su Tsito basu da kamata yarinya bare ki min gori,Handsome kamata kema dan kin sanni ne kina ganina a banza kije kiga yanda yan mata suke rubibi na kulasu,da ace baki sanni ba da tuni kin mato a kaina,Allah ya kiyaye ai ni shekarunka sunmin kadan yaro dakai, Wukar da nake fere dankali ya karba ya fara taya mu yace ku matsa so kuke yunwa ta kashe mu a gidan nan, hmm Mufee ce taki fitowa ko lfy? Cewar Ma'eesha,Uwar Sa ido ina ruwanki dan bata fito ba mace da Mijinta ya kamata a aurar daku kuma ku daina sawa mutane ido,Maeesha tace mu ina ruwanmu dan tani su shekara a Bedroom in dai lfy shike nan, wurin 11am da kyar Aayan ya tasheni nayi wanka tare da Brush na sake gasa jikina na daura alwala tare da tayar da Sallah,Lokacin Aayan ya shirya cikin wani yard me Laushi Dark arsh color,Ina kallonsa yanda yayi kyau ya zarta kwatance, nayi adduoi na mike a hankali kamar yar kaciya na lallaba na shafa Lotion da turaruka tare da Sa Gown me kyau simple English wear doguwace har kasa sama ta dan dame kasa ta bude pink color nayi kyau sosai,powder kawai na shafa tare da lipgloss red sama sama na yafa dan siririn gyalena a kaina,uban gashina nayi acuci dashi.

    Aayan sai bina yake da kallo so yake sai ya kara yi Amma na ki yarda ko fuska ban bashi ba,na dan dingisa har gabansa na zauna gefensa a saman Bed na kwantar da kaina a cinyarsa ina kallonsa nace ina kwana ya rufe min baki da Sauri tare da cewa ni ya dace na duba lfyr ki My Dear,ya jikin?Nace da sauki yunwa nake ji kasan bana jure yunwa ni,Ki kwanta bari na kawo miki abincin da kaina nasan su Meenat sunyi ma yanzu,Yatsunsa nake wasa dasu nace so kake su gane sai yanzu ka angwance gashi sai murna kakeyi kana fita zasu gane tunda ka kasa boyewa jiya ka kwashi dadi,Dariya Aayan yayi ashe dai matar tawa bata da kunya da yawa,fuska ta na boye a kirjinsa,tashi muje Amma tafiyarki ta canja ya za ayi kawai ka rikeni sosai irin soyayya ce,haka za ayi.
    Hannunsa ya zagayo ta kuguna ya manneni a jikinsa tare da rikeni sosai muka fara Tafiya a hankali,nace wash Allah ina famuwa wajen da zafi kawai ka daukeni Bazan iya bin Steps ba.
    Ba musu ya daukeni kamar Jaririya tare da cewa kin tabbata baza kiji kunyarsu ba? Nace waye bako na ciki,Ameer ne kuma shi baya shiga sabgar wani bazai ma kalle mu ba.
    Suna Dinning suna Break suka hango mu muna sakkowa,Meenat ta Radawa Ma'eesha sabon Salo yau suka canja,Maeesha ma a kunne tace Mufeeda yanzu ko kunya bata da ita,Ameer yace nima dan rada min naji,Dariya sukayi Ma'eesha tace Bada ni ba,Meenat tace dole kai sai kaji nan a hankali ta karkata gefen Ameer tace Sabon salon su Aayan muke kallo a sama ko kunya babu kallesu,Ameer yana dariya ya dan Saci kallon yace uhmm wannan harka tayi nima Allah ya kawo ranata har sun tayar min da tsohon tsumina.
    Suna ganin mun karaso suka daina kuskus duk na tsargu nasan halin Meenat.
   Aayan suka fara gaisawa sai ni,sun saba kullum faran faran ina jansu da wasa Amma yau suka ga shuru sai dai na kwanta jikin Aayan lagwaf, Aayan yace ina abincin fa naga Table sai kadan? Meenat tace bamu dafa daku ba Sabo da Sis sai tace baka cin Kaza da Kaza shi yasa muka yi iya namu in ta fito sai mu tayata tayi muku naku.

    Aayan ya janye na gaban Meenat ya mikawa Mufee,ya janye na gaban Ma'eesha da Ameer ya mikawa Mufee Amma na Ameer shi ya cinye da kansa matarsa baza taci ragowar wani ba,Meenat baki bude take kallonsu hankali kwance suke cin chips and Egg dinsu harda tea din,Aayan yace kuje ku dafa wani ku in kun gama kuci,Mufee ko magana banayi cin abincina nakeyi duk Aayan ya wani rude ya rasa inda zai Sa kansa ya rasa ina zai sani ko me zai min bakinsa a washe yau shi kadai yake ta hira a Dining Ameer mamaki ne ya kamashi dan shima bai san Aayan haka yake ba da surutu gashi ya kwace musu abinci sun cinye musu,Meenat ya kalla da suke ta kallo na yace kuje ku dafa ma kanku wani abun,Darling me zaki ci? Ko kin koshi yanda yake min maganar ma a hankali kamar Jaririya sai da naji kunya,ido na daya na kashe masa sannan nace farfesun Kifi nake so da dambun naman Kaza,Aayan yace to Kunji ayi mata yanzu da wuri kar a dade kai Ameer kuje ko wanke wanke ka tayasu,Dariya Ameer yayi tare da cewa Yaya harda ni ina namiji kasan ni ban iya shiga kitchen ba bayan haka ma Meenat ta gama rainani a gidan nan zagina takeyi,Meenat tace wlh sharri yake min ni ko hararar Sa ban taba yi ba fa, Ma'eesha tace dan Allah muje muyi Sauri zanyi bako ni anjima,Meenat ta kalli Aayan Ya kasan Bakon nata? Aayan yace pls kuje mana kun dameta da surutu kanta zai fara ciwo,ina jinsu sai dai nayi musu Alama da hannu kamar wata sarauniya wai ni ga me miji ana so na nace kuje pls da kyar na furta hakan cike da yanga.

    Kitchen suka wuce har Ameer din shi abin ma dariya yake bashi na Aayan to yau me Mufee ta bashi ne haka,Maeesha sarkin kida bluetooth speaker ta dakko ta ajiye a kitchen tare da hadawa da wayarta ta fara Sa musu kida sun cika kitchen da kida, Ameer da Ma'eesha sai bin wakokin sukeyi dama sune sarakan waka,Maeesha ita a wajen rawa ba kunyar uban kowa takeyi ba rawarta take cashewa suna aikin,Ameer kuwa Babban yaro ne sai dai yayi Alama da hannu,Meenat kallo take kawai tana dariya suna girkin suna cinyewa duk dambun naman sun cinye rabi dama kadan sukayi,Farfesun kifin ma haka,Ameer yana ma Meenat magana a daina cinyewa bata ji sanda yayi maganar ba ya dauki spoon daga Cikin farfesun ya dau zafi sai da ya dan tsaya yanda bazai Konata ba Amma zata ji zafi ya daura mata a bayan hannu,a zabure Meenat ta juyo tana yarfe hannu nan take ta koma gefen sink Bowl dauke da ruwan da suka wanke kifi da nama hannayenta biyu ta tsoma ciki ba tare da Ameer ya sani ba sai jin tafin hannayen Meenat biyu a fuskarsa gefen sajensa tana shafa masa kamar me shafa mai, karni yaji da Sauri yaja baya yana dauke numfashinsa ga Ameer da tsantsami  baya son karni ko kadan yanzu zai fara Amai,Meenat bata sani ba har sumarsa ta bi ta shafa masa ta karfi yana zillewa.
    zuciyarsa har ta fara tashi da Sauri taga Hankalinsa ya tashi ya fito da Sauri tare da wuce mu a Dining ya fada Bedroom,tunaninmu da Meenat sukayi fada Aayan yace Meenat ce ta bata masa shi kuma ga fushi wlh aure zan daura musu,Dariya nayi nace hmm Ai Ameer ke tsokanar ta.
   Ameer yana ciki sai wanka yake shekawa kamar zai cire fatarsa ya dade yana abu daya ya fito zuciyarsa na tashi still haka ya shafa Lotion yayi sabon shiri kayan da ya cire a leda ya zuba su tare da fitowa ya wuce mu ya jefa su a dustbin na Compound,Ya kara dawowa Bedroom da Sauri sai kakarin Amansa muka jiyo,Kaji kamar Ameer Amai yakeyi,Aayan yace wani abu ya gani na kyankyami ko karnin kifi yaji haka yake yi,Amma kasan haka kace ya taya su? Na manta ne sai yanzu na tuna Amma tambayi Meenat ko dama bashi da lfy ne.

     A hankali na mike da kyar nake Tafiya har kitchen nace Meenat me ya samu Ameer,ba komai spoon me zafi ya Dora min a hannu shine na shafa masa ruwan kifi a fuska,Maeesha tace wlh har sumarsa ta shafa masa,fuska na bata baki da kunya dalla jibeki ta Tsito kawai sai kije kiyi jinyarsa gashi can yana ta sheka amai a toilet Aayan yace baya son Karnin kifi danye baki kyauta ba,Kirji Meenat ta dafe tare da cewa wlh ban sani ba Sis Allah Sarki to me zanyi in na je ma? Harara na watsa mata ki wanke toilet ki gyara ko ina.

    Lokacin Aayan ya shiga wajen Ameer dake toilet yana ta faman Amai,Doctor ya Kira tare da sanar masa nan take Doctor yace ga magani nan ya bayar a kawo,15mnt  wani Nurse yazo a mota har gidan dake Aayan duk ya sansu suka gaisa ya Bada magani a leda tare da yanda za a shasu ya tafi,ni kuwa uwar son abin duniya har Dustbin naje na zakulo kayan Ameer da ya jefar nace wannan ai fariya ce na bawa me wanki nace ya wanke su ya goge idan ma Ameer baya so sai na kaiwa Shehu me kanti na tsohuwar unguwarmu wanda muke buga masa waya ya kaiwa Ammah.

   Meenat Zata shiga Bedroom din Aayan yace ai sai kinyi wanka sosai zaki shiga Sabo da kina zuwa kusa dashi yaji wani karnin amai zai kara yi,Cike da tausayi Meenat ta wuce Dakinsu a ranta tace shi yasa suna fara taba kifi yaja baya ya koma karshen Kitchen ya zauna a can,amma kuma yana cin kifi kadan kadan kawai danyen ne bai son karninsa kuma.
    Ma'eesha ce ta karasa komai tare da shirya Dining ta gyara kitchen da komai ta wuce Bedroom lokacin Meenat har ta gama hadewa cikin Lace Sky blue riga da skert tasha kyau ga iya kwalliya,turare tayi ta shafawa iri iri Sabo da kar taje Yiwa Ameer Sannu yaji Karni a jikinta ya fara Amai,ta fito Aayan ya mika mata maganin ki tambayeshi me zaici ki bashi,ina kwance saman cinyar Aayan nace Meenat kar ki sake wlh ki masa rashin kunya Kinji na fada miki,Dariya Meenat tayi sannan tace to ni ina ruwana dashi?
    Shiga dakin tayi da mamaki yanda Dakin yake komai Neat kamar na mace,saman Bed ta hangoshi ya dukunkune cikin bargo yana rawar Sanyi,Meenat ta karasa gefensa da Sauri tace Sannu Ameer kayi hakuri ban san Baka son Karni ba,duk da ciwon nasa sai da yace ta Tsito in ba shirmenki ba wa yake son Karni? Murmushi nayi me zaka iya ci yanzu? Ba komai,to tashi kasha magani inji Ya Aayan,haka yace ai sai dai ki hauro saman Bed ki bani Bazan iya tashi ba, farko dai Dan zuba min ruwan tea me zafi ki zuba zuma spoon Uku sai ki matsa lemon tsami kadan ki kawo idan na sha sai na iya shan maganin,dan da nan tayi yanda yace ta Hau tsakiyar Bed din sannan ta bude blanket da kyar ya fito tare da dan Zama kadan,ta daura masa cup a baki ya shanye zumarsa tas,sai ta mika masa ruwa da magani kala biyu ya shanye sannan yana rawar sanyi ya koma ya kwanta, Amma ba amai kawai ya saka harda zazzabi ba? Meenat ta tambaya, Ameer wanda yasan shi dama ciwonsa na Sha'awa na motsawa sama sama to harda shi yau,Yace baza ki gane ba Meenat ciwon biyu ne suka hadu,Da tausayi Meenat tace Sannu Allah baka lfy.

    Ameer ya dan kalleta kadan yaga zata bar dakin nan take ya fara nishi yana ohhh wash cikina da Sauri Meenat ta dawo gabansa a gigice ta haura saman Bed din tana ciki kuma again?ko maganin ne ai Ameer fari ya kama yi da ido wai ya sume,Meenat ta rude harda kuka tana dan Allah ka tashi karka mutu kaji tana jijjiga Ameer ya kara lumshe ido Meenat taga fa kamar ma ya dauki hanyar mutuwa gashi ya wani kankame cikinsa dai dai mararsa ya dafe wajen kam kam,Meenat da kyar ta iya cire hannunsa saman Marar ba riga a jikinsa sai Wando 3qrt Shakewa taji yayi yana shidewa kawai sai taa maida hannunta saman Marar tasa tana latsata ko ina ba tare ma da tasan me take ba,Ameer dadi ya gama kasheshi sai nishin dadi yake da numfarfashin dadi, a ransa yace Hajja ma na girmi wayonta bare ke,zaki kasheni ban shirya tafiya ba, ita kuma tunaninta zafin ciwo ne sai ta kara dagewa tace kana jin sauki?Yace da kyar banji me kika ce ba fada min a kunne na,so yake kawai tayi masa magana ya kara Jin sweet, haka ta kara bakinta a kunnen Ameer tare da cewa kana jin sauki? Wani sanyin dadi yaji nan take kafin kace me Ameer ya wani rike Meenat gam gam yana shidewa Meenat ana kukan Tausayi wai yana jin jiki, sai ga Ameer har ya warke ras ya samu nutsuwa zazzabi ya sauka sai gumi ke keto masa Sabo da dama cutar tasa ta Sha'awa ce kuma garin latse latse ta sauke masa ita ya dawo hayyacinsa.

     Muryarsa taji yace ba kyau Allah ya hana taba mutumin da ba muharraminki ba kin jawo min Allah zaiyi fushi dani ki tafi zan fito naji sauki na gode,da Sauri Meenat ta cire hannunta daga Cikin Ameer tana Harararsa ta sauka daga Saman Bed din da Sauri tayi waje abinta ta bar Ameer yana dariyar jin dadi yasan yau daba dan Allah ya kawo Meenat ba da maybe mutuwa zaiyi da ciwon Sha'awarsa tuni dan rage zafin ma da yakeyi da mata ya daina,yanzu ya tuba baya kula ko wacce ya mace Sabo da yaga duk bata lokaci ne.
   Meenat na fitowa ta tarar na zauna daram a cinyar Aayan yana bani farfesu ina ci,sai shagwaba nake masa ina Hawaye yana lallashi, tunanin Meenat zanji kunya kawai sai taga nayi mursisi ko a jikina sai ma kara lafewa da nayi a jikinsa ina shakar kamshinsa,da Sauri Meenat ta fasa wucewa ta koma dakin Ameer Sabo da wai taji kunya, dariya nayi kawai,Meenata a ranta tana to wai Sis me aka yi mata yau ne komai kuka shi kuma yau ya Zama maye a kanta gaba daya lfy kuwa?

    Ameer lokacin ya shiga wanka Meenat ta dan jira wai ko zata ga mun tashi Amma sai ta dan leko ta kofa taga muna nan muna Holewa haka ta hakura ta fito da Sauri ta shige Bedroom,Maeesha kuwa tana palon baki tare da Yarima suna hira.
    Aayan ne ya daukeni tare da cewa an koshi haka muje ki kwanta zanje wurin Daddy, ka gaishe min dashi   sai na warke zanje,h ar Saman Bed ya kwantar dani tare da rufa min Blanket bai dade da fita ba bacci me nauyi ya kwashe ni.

    Yau Daddy kansa yasan Aayan yana cikin farin ciki me tsanani,Daddy ya kalleshi tare da cewa fada min Son wanne abin farin ciki ne ya same mu?Aayan ya fara dariya wacce Daddy ya rasa gane ta mene,Aayan nasan baka boye min komai sanar min mene? Daddy kunya nake ji fa abin kunya ne,Sanar min naji muyi farin cikin tare,Daddy na Warke jiya ya fada tare da rumtse ido wai kunya,Murmushi Daddy yayi na jin dadi tare da cewa Alhmdllh Son Allah ya kara lfy me dorewa da nisan kwana, jeka tunda yau kunyata ka koma ji,da Sauri Aayan ya bar part din Daddy ya dawo namu,kayansa ya cire da Sauri daga shi sai boxers ya shigo blanket dina ya shige jikina sai bacci.

   Sai wurin 3pm na farka na ganshi a jikina kara lafewa nayi a jikinsa ina shakar daddadan kamshinsa me sanya nutsuwa,hannunsa ya daura saman kirjina yana baccinsa cikin nutsuwa,tunawa nayi bamuyi Sallah ba ga La'asar ta kusa fuskarsa me matukar kyau tare da sajensa na shiga shafawa a hankali,shima a hankali ya bude idonsa ya saukesu a fuskata me cike da nishadi,bamuyi Sallah ba muna ta faman bacci na karasa ina sauka daga Saman Bed din sai toilet, nayi brush tare da wanka nayi alwala na fito sai lokacin ya shiga shi ma,ban jirashi ba na fara yin sallah sannan na shafa Lotion tare da turaruka nasa kayana lokacin ya fito La'asar tayi na yi Sallar sannan na zauna gaban Mirror na tsantsara kwalliya tare da Sa Atamfa green riga da skert nayi kyau na mamaki,ina gyara Bedroom din ya idar da sallolinsa tare da addua,na gyara room din har toilet komai Kal kal duk da ba wani lfy ce dani ba Amma Haka na daure na yi.

    Hajja ce Tare da Abbi suka shigo gida sun dawo daga gidan ko zasu ga Daddy Amma gidan an kulle ba kowa haka suka dawo jiki ba kwari,takaici ya damu Hajja,Abbi yace yanzu ina zamu gansu? Hajja bakin cikinta bata dauki kudi ko sisi a gidan ba,yanzu bata da ko kobo,haka kowa na gidan babu me shi,Gold din matan su Abbi ma iya na kunnensu ne da abin hannu basu da komai,ga ba abinci,har Companies na Aayan sunje bai je aiki ba kuma an hanasu shiga,zama sukayi kowa yayi jugum jugum,Abbi sani yace Hajja bafa aci ba,me zamu ci a gidan dole ciki sai ana bashi hakkinsa,Abbin Ameer yace idan fa na gaji wlh zan tsinewa Ameer na huta yaro dan iska tambadadde ya barmu ko kallonmu baya yi yana can yana jin dadinsa, dama Hajja tana cikin fushi ai ko ta hayayyako da masifa rufe min baki dan Iska da bayanka me zubin na Kwadi, Ameer din nawa zaka la'ana ahir dinka duk jikokina nafi sonsa, Mujaheed yace ai ba shi ya kar zomon ba,duk ba kece kika jawowa kowa ba yaja tsaki,Hajja ta Harare shi da gogoronta irin na yorubawa tasha bakin kwalli a ido bajagau,Khaleel yace mu kawai a san yanda za ayi damu muci abinci,Umman Ameer tace ga dankunnen Gold dina a siyar a siyo abinci,Haka ma matar Abbi Mustapha,da Abbi Sani sai Matar Abbin Yara duk sun Bada nasu,Hajja tace Kai Sani kaje ka siyar dasu ka siyo kayan abinci,sannan ka kawo min dubu goma a ciki zan ajiye a aljihuna kasan zama ba kudi masifa ne,Abbi yace haba Hajja ko masu dankunnen ba a bawa ko 1k ba sai ke za a baki har 10k kin san fa abinci har kayan girki sai an siya,Haneefa ta bude Jakarta tace ni gashi na taho da 10k gashi a bawa Hajja mu huta,da Sauri Hajja ta fisge kudin ba ko godiya,Sajeeda tace dubu biyar gareni kwandala Bazan bawa wata katuwar tsohuwa ba gashi Mujaheed da Khaleel ku rike a hannunku,haka Meenal duk cikin yan matan tace ga Wata 3k Ni Abbi Mustapha zan bawa nawa Sabo da shi ke bani kudi idan na rasa ku kuwa dazu duk ni na siya muku Waina da miya kuka ci kuka koshi Bazan kara muku ba.
    Hajja tace Allah sarki duniya Aayan da Daddy tunda suke mana komai basu taba yiwa kowa gori ba.

   Wani dan yaro Sabeer yace Mommy ruwa zan sha babu,Hajja ta taso da Masifa zaka ci ubanka kai baka san babu ba ance ba ruwan roba a nan ko purewater babu dan Iskan yaro matsiyaci,Sajeeda tace kaje ka balle kan pampo yaro ka kwankwadi ruwa idan typoid ta kamaka ne hanji ya bule ka sheka lahira dan ni nasan wlh indai a haka zamuyi rayuwa ba shakka mutuwarmu ta gabato cututtuka kadai sun ishemu ruwan pampom ma wasu gurbatattun abu ke fitowa ta ciki.

   Haneefa ta sosa cinyarta tace karzuwa ce zata kamani kwanan nan ,Meenal tace ya Ilahi muna karbar rayuwa,Mujaheed ya sheke da dariya tare da cewa ths is just the begining matukar Hajja na raye,kwana biyu kacal, dundu Hajja ta zuba masa a baya.
   Kuka akaji Hajja ta saki tana komai ace nice Allah ya Isa abin ya kai har mutuwa ake jawo min da lfy ta da kwari na, Abbi yace kiyi hakuri baza su kara ba,Hajja ganin yayanta Maza na wajen ta fara shure shure tana mutuwa zo ki daukeni na huta ga jikoki birjik suna ji sai Khaleel ne yaja tsaki tare da cewa wuya kika ji shi yasa kike kiran mutuwa da sanda muna gidan daula da jin dadi me yasa baki nemo mutuwar ba,ki rufawa kanki asiri wlh karki mutu yanzu sai kin tuba idan ba haka ba Ki ci duka wajen walakiri da bulalar wuta, Hajja tana Hawaye tace ubanka da uwarka ka fadawa haka Mutuwar tazo ya fiye min wannan rayuwar ta talauci.

   Su Abbi an dan siyo kayan abinci matan suka siyo kayan girki tare da na cin abinci duk na talauci haka gidan sai Abbi ne yaje ya karbi bashinsa hannun wani da yake bi Dubu Dari sune ya samu ya siyawa kowa katifa karama sannan aka sawa gidan kaya da sauran kaya haka na talaka,kitchen ma aka kara yan kayan cin abinci da kayan abinci ana dan cin garau garau, duk yanda suka so ganin Aayan ko Ameer ya gagara,har Yarima sun nema yaki saurarar su,ganin haka Hajja tace su hakura ai indai Daddy ne zai nemeta tunda uwarsa ce kuma yana yi mata biyayya su danyi hakuri na dan wani lokaci,gashi yan samari da yan mata sun hana a siyar da wayoyinsu manya tare da laptop dinsu sunce a mutu da yunwa akan a siyar gashi abincin da yan makaranta duk sun cinye kudin su Abbi,a bincin ma sabo da suna da yawa da wuri ake cinyeshi gashi babu me aikin yi ko fita basa yi a unguwar yaran ne kadai ke zuwa schl Abbi yace kudin makaranta na karewa sai dai a maida su ta Gomnati,Mujaheed  da Khaleel kuwa su Abbi sunyi sunyi dasu su karkade takardunsu su fara fita neman aiki amma sunki Sam,sabo da ba a musu tarbiyar neman na kai ba,ba a nuna musu tun farko cewar ka nemi naka yafi akan ka dogara da kudin wani ko na ubanka,basu san wahalar duniya ba.
    Su Haneefa yan mayuka masu kyau duk sun kare an fara duhu duk da cewa suna da haske amma sabo da ba irin rayuwar da suka saba ba kenan duk sai suka fita daga hayyacinsu sai masifa da rashin kunya da suke yiwa kowa a gidan musamman Hajja da suke ganin laifinta ne. Saurayin Meenal ne ya bata Dubu ashirin suka samu aka sa carpet a Palo da bedrooms,shima sai da ta dinga rokar shi ta zubar da ajinta sosai ya dan Sha minti da ita sannan ta samu kudin.
    Matan su Abbi kuwa yanzu yar biyayyar da sukewa su Abbi Ashe duk ta kudi ce yanzu fada da masifa kawai ke tashi a gidan babu me Zama lfy,Hajja da tayi magana su zageta,Hajja ba kudin zuwa wajen bokaye sai cin goro da take tashen yi ba dare ba rana.
   Tun daga wannan Rana Hajja Sabo da bata son talauci take kiran mutuwa ko a dakinta sai kaji tace mutuwa kizo ki daukeni da wannan rayuwa,tace to yaran wai ina suka buya haka ko ina an kasa ganinsu da ace sun bude mana gidan ma sai mu kwashi yan kadarorinmu da kudadenmu ko banza ma kafa kanmu cewar Hajja,Haneefa tace ah Hajja kiwa Daddy da Aayan baki mana wlh da nice ke tsinewa Daddy kawai zanyi.

  Harara Hajja ta zabga mata tare da cewa to ai yafi ubanki dan uwarki ubanki Abinci kadai ya kasa daukan nauyinmu bazan tsine masa ba idan uwata ce ke sai kisa na tsine masa munafuka da hakora kamar na gafiya.
   Kullum yan gidan Hajja ta Gallabesu da kiran mutuwa kawai sai dan  Matashi Sabeer yau da dare ya shirya cikin fararen kaya tas,komai fari yasa tare da shafa chalk a fuskarsa ya koma kamar dodo,ya shiga dakin Hajja cikin tsakiyar Dare ya wani tsaya a kanta tare da canja Murya yace Hajja.....firgit ta buga ihu daga kwance taga haka tunaninta Mala'ika ne ko Aljani,yace kin dade kina kiran mutuwa yau gani nazo nine Mutuwa yanzu zan daukeki,Hajja sai ta fara ihun Kuka tana bada hakuri,Sabeer ya fice da gudu ya boye a dakinsu ganin Hajja zata tara masa jama'a.
   Tun daga wannan rana Hajja bata kara ambatar sunan mutuwa ba.
 
   Abbi cikin su uku kowa yana da daki shi da matarsa,sai na Hajja daban,Yan matan gidan kuwa manya da yara gaba daya daki daya suke gwamitsa wurin su takwas,kowa da shimfidarsa anyi kwanciyar kai da kafa,Haka mazan ma Kowa a daki daya jal manya da yara haka kullum Suke fada da masifa ba ji ba gani ba zaman lfy a junansu sai dambe,Hajja ma ta Bullo da rigimar ta gaji da zaman banza gwara a siyo mata taskira hhhh irin ta tsofaffi da Mazarin kadi tare da Alli zata fara kadi tana murza Mazari tana saka zaren auduga,Khaleel suka dinga dariya tare da cewa anji wuya za a kare a taskira kuma wato yanzu kin yarda kin tsufa har zaki hada Taskira guda ana tauna goro anci goggoro ana kadin Zare,hhhh yaran kowa yana dariya wa Hajja,Hajja anji wuya cewar Meenal sanda ake goge hakora da Cinyar kaji ba a gode Allah ba sai yanzu da ake gogesu da goro,Nan take Hajja ta fashe da kuka amma ko kiran sunan mutuwa ba a ji tayi ba kus kake ji sai hawaye.

    Aayan kuwa shi tuni ya hana Ameer fita kuma kar ya kunna wayarsa yanda su Hajja baza su samu ba,yace sunyi hutun zuwa Office ba me fita ba me shiga sai ya gama Amarcinsa zasu tafi Abuja,Yarima kadai ke zuwa wajensa ko wajen Ma'eesha,Daddy kuwa shi kanshi yanzu hankalinsa yafi kwanciya yafi jin lfy ma a jikinsa amma duk da haka indai Aayan zaije wajensa sai yace ya maida Su Hajja gida sai yace to amma yayi shuru abinsa.
   Aayan ne ya sameni a Bedroom ina karanta Novel a waya yau kwana uku kenan naki yarda Aayan ya kara ko kissing dina ba yanda baiyi ba naki yarda, gefen bed din ya zauna jikinmu na Gogan juna wayar ya karba a hannuna tare da ajiyeta can gefe yana kare min kallo na maita,Kunyace ta kamani duba da kayan dake jikina riga ce me dan fadi me hannun vest iya cibi tsayinta sannan sharashara komai a na gani kamar mataci,sai wando Jean white pencil nasha kyau gashina kamar na Baturiya.
    Hannun Aayan naji na yawo a kirjina yana murzasu,ban hanashi ba sabo da nima wani dadi nake ji sai dai shagwabe fuska da nayi kamar zanyi kuka.







😍😘😍😘
Afwa fans abubuwa kwana biyu ne suke dan min yawa shi yasa zaku ga bana baku pages a kai a kai ba haka na so ba.
❤❤❤❤❤






Typing error ko kuskure ayi hakuri idan an gani.






AsmaBaffa
[1/31, 10:53 PM] Asmabaffa: 🌖🌖🌖🌖
🌖🌖🌖🌖

    KASUWANCI NA







            105-106






By
AsmaBaffa







   ZAINAB ATIKU SALAMA ths page is for u tawajena.















           Shuru nayi sai ma kara gyara masa nayi ina so na hanashi amma bazan iya ba gaskiya,bazan iya shanye wannan shagali ya wuce ni ba banma san sanda na fara mayar masa da martani ba cikin salo da birgewa,muryarsa naji da kyar yana I need u Babyna pls ki yarda a hankali zan miki ba zafi,Yanzu Yamma tayi ka bari sai dare maybe na yarda,no ni ban yarda ba yanzu nake so sai dai idan baza ki bani ba dama tunda ni bakya so na,Haka nace ma bana sonka? to in kina so na ai zaki ji tausayina amma ke ko daya babu a idonki, murmushi nayi sabo da ina sonsa bana son na yi masa laifi ina ji ina gani cike da tsoro nace to ka kara yi kadan amma,yace dan mitsili zan yi,nace to tunanina da gaske dan mitsili din zaiyi,jikinsa na rawa ya fara sarrafani a Fagen sarrafawa sai dai mu sarrafa juna sabo da ta nan ba a bari na a baya sabo da dadi ne ke kwasata kawai nima naji na iya na fara nuna kwarewa ta,a hankali yake bi dani har ya samu Hanyarsa Yanda nake da Niima sai dai a shafa Fatiha, Kai..kai..yau ma da zafi Allah ni bazan yarda ba,Aayan a lokacin yayi nisa kara kankameni yayi ba ta inda zan iya motsi,a hankali yake aikinsa ina ihun Zafi bakinma toshe min yayi da nasa sai Sambatu yake iri iri,in nace ya dagani sai yace dan Mitsili zaiyi sai da ya mugun dadewa sannan ya samu nutsuwa,ya gamsu sosai.

    Kukan Shagwaba nake masa yana ta lallashina tare da rada min dadadan kalamai,yau ma naji jiki a hannunsa,nace aka sake Allah Hijira zanyi na bar garin,Dariya yayi ina zaki koma? Can yankin Mambila sai muyi Hijirar tare kafata kafar matata,Ina shafa kirjinsa nace ai bazan je da kai ba tunda kai zaka jawo nayi Hijira, Do u knw what? Sai ka fada, I love u,i love ur everything,u r so sweet Baby ban ma san yanda zan miki bayanin ba, kwanciya ta na gyara tare da juya masa baya,Juyowa dani yayi tare da cewa wa yace miki ana juyawa me gida baya? Mantawa nayi shi yasa wanka za muyi haka ya daukeni har toilet na Sha gashi sannan mukayi wanka tare da tsarkake jikinmu.
    Sai da muka kwanta har bacci ya kwasheni naji Aayan yana shafani sai Shan albarkatun kirjina yakeyi,a hankali na tsinci muryarsa yace My Mufee pls dan Dis nake Needing,baki na turo kamar zanyi kuka haka dazu kace Dan mitsili yanzu kace Dan Dis Allah akwai zafi in ba so kake wajen ya   samu matsala ba,Insha'allah bazai samu ba dole na hakura ya kara yin na biyu.
    Amma wannan kam kasa hakuri nayi kuka nayi ta barkawa sabo da zafi,na tabbata da ace akwai wasu kusa damu sai sunji irin yanda nake Magiya da kuka,Aayan shi baya gajiya ko kadan Sambatunsa kawai yake yi wanda bai ma san inda yake ba.

     Washe gari ma again da safe kasa tashi nayi sabo ya min raga raga jiya,Shi ya min komai da komai ina jin Brush kawai nayi da kaina sabo da duk kakale kakalena Aayan uban gida nane kamar zai cire makoshi ni ko nace ya bani nayi, har shafa mai tare da sa kaya shi yayi min mukayi sallar Asuba da Azkhar ya kara gyara Bedroom din sannan muka koma bacci sabo da Bala'i kari naji zai nema kawai nayi baccin karya daga haka na gasken ya daukeni,shima yasan idan ya sake nema baiyi adalci ba haka ya danne jarabarsa yayi bacci da kyar.
   Meenat ma yau shuru suka jini sun kasa gane kaina kwana hudun din nan,yanzu basa jirana ma Kansu suke mawa girki in na fito aci damu idan bana ci su dafa min wanda muke so ni da Aayan,Ameer kadai suke kira suci abinsu.
    Suna kitchen duk kusan Meenat ce ta gama komai Ma'eesha waya takeyi da Yarima da safen nan tana yanga tare da kashe murya.
    Hello Dear cewar Ma'eesha,yeah ina jinka,Yarima ya wani yi juyi saman Bed tare da cewa am just missing u,Maeesha tayi wani murmushin jin dadi Miss u much more Dear,me kikeyi yanzu,Ina kitchen,wow shi yasa naji kamshi cewar Yarima, uhmm kai ina wani kamshi a girkina na yan koyo,Ba wani yar koyo ai Ameer yace duk kun iya girki kinga na huta.
   Dariya kawai Ma'eesha tayi sannan yace ltr,ok Allah ya kaimu sukayi Sallama lokacin Meenat ta gama komai har gyaran kitchen.
  Tace gashi nan Ma'eesha ki shirya Dining ni kuma bari nayi wanka,wa zakiwa wanka yanzu ki Bari muci sai kiyi ke wai ko da saurayin ki a gidan nan ne?bakya ko fitowa Palo sai kin yi kwalliya.
    Meenat jin sharrin da Ma'eesha zata kulla mata ta fasa zuwa tayi wankan,doguwar rigar ta bari Blue a jikinta da dan siririn gyalenta tace muje to mu karya.

    Sun Zauna Dining kenan sai ga Ameer yaci uwar wanka kamar zaije wajen Daurin aure shadda light blue tasha aiki dinkin kamar a jikinsa aka dinka das das dashi sai kamshi yake bulbulawa yayi wani Fresh sumarsa me yawa sai sheki take ga gemu na matasa dan firit tare da saje kadan.
   Ma'eesha tayi dariya tace gaskiya yau kayi fa, kafi ko yaushe kyau amma Yarima ya wuce ka,Meenat kuwa na kallon Ameer sai ko tayi sauri ta tsuguna a kasan Dining ta buya gyalenta tasa tana ta goge fuskarta wai kar aga maiko, Ameer yace Yarima Din me yarinya Bobonki bai kaini haske ba,amma dai baza kace baki ko chocolate bane ka sani dai ga Hanci kamar biro dan gayu na karshe,Dariya Ameer yayi yace ke kika sani kuma wannan.
   Kamar naga Meenat a nan Ameer ya furta,Maeesha tace tana kasan Dining yau aljanunta ne suka motsa tsoron mutane take ji,daga nace wa zata yiwa kwalliya da safe shine taji tsoro na ta fasa fita,Yanzu kuma tana ganinka shine ta buya kasan Nan wai tsoronka take ji,Aljanun tsoro ne suka shigeta,Dariya Ameer yayi tare da tsugunuwa kasa ya leka sai ko Meenat ta kara yin kasa tare da boye fuskarta,yace yau sai naga me kike boyewa yayi kamar zai kamota ta fito da rarrafe ta Mike da sauri ta koma Bedroom,Meenat ta saba da kwalliya idan bata yi ba bata Jin dadin rayuwarta,wanka tayi ta shirya cikin Doguwar rigar Lace tayi kyau matuka,sai lokacin ta fito suna ta cin abincin su ma sannan itama tazo ta zuba nata ta fara ci,Ameer ya kalleta ya kara kallonta sannan yace baki gaisheni ba yau,Ina kwana?ka tashi lfy? Yace lfy lau, u?tace lfy yace good kin kyautawa kanki da badan haka ba yau da sai kin fadawa yan garinku,dariya suka yi gaba daya.

    Meenat yau ta fita zuwa Islamiyya schl dinsu ta kai wani kudi tana kan hanyarta ta dawowa  gida da yamma wani Saurayin matashi wanda bashi da makusa ta ko ina cikin dalleliyar motarsa ya dinga bin Meenat ta saurareshi amma taki sai da suka zo har gida,Matashin ya firgita da ganin irin wannan katafaren gida,A ransa yace da gani dama kalar masu kudi ce, haka yake ta kallon gidan da Meenat ta shiga da yake Islamiyyar ba nisa da nan gidan,Me mota dai haka yayi shahada ya tura daya daga cikin ma'aikatan gidan cewar dan Allah ya kira masa waccen yarinyar,Me gadi yace Meenat sunanta ai bari a fada mata,Ina Palo muna tare da Ma'eesha dake chat sai Ameer,Me gadi yayi Sallama tare da cewa Meenat kinyi bako yana waje wani me jar mota,Nasan wannan me nacin ne,Ameer yace kina ji fa Kije maybe yayan Tsito ne,wani haushin Ameer Meenat taji da ta rasa gane na mene kawai tace kace ina zuwa, Meenat ta Mike ta shiga daki Don ta kara dan gyarawa ta fita,Kafin ta fito Ameer ya fita wajen Saurayin kawai yace yayi hakuri an kawo kudin auren Meenat shi Yayanta ne, saurayi yace ba komai Allah tabbatar da alkhairi ya shiga motarsa ya tafi yana cike da jin haushin Ameer ko karya ma yakeyi oho a ransa yace suje da yarsu dan Ubansu an fasa aura wannan abu na rufawa juna asiri.

    Ameer ya koma inda ya fito ya zauna yayi mursisi,Sai ga Meenat ta fito anci uban gayu kamar zata je Dinner Ameer yana boye dariyarsa Meenat ta wuceshi da yanga tare da Galla masa harara dan ta ganeshi dariya yake mata,ta fita tana kunkuni tace Sa'idini kawai,Sai da taje taga wayam ba kowa,har waje ta leka,Me gadi yace ranki ya dade ya tafi yarsa ina daki naji karar motarsa ya figeta a fusace,ko dan kin dade ne yayi fushi,su kansu Masu aikin basu ga sanda Ameer ya kori bakon ba,Meenat a ranta tace yayiwa kansa, gaba ta kaini tuntuben me choge.

    Tana shiga Palo ta zauna gefen Ameer, har ya tafi? Meenat tace ae mun danyi magana sama sama,Ameer yace da Alama kina sonsa? Meenat tayi banza dashi tana latsa waya,sai daga baya tace ya Ameer dan Allah ka kaini gidan kawata da yamma mana kaji? Driver dinku me yakeyi? Sis Mufee tace yaje ya duba Iyalinsa can kauye sai mun koma hutun schl zai dawo,Ya Aayan ya hanamu fita sai nan da wani lokaci ki Bari idan mun tambayeshi ko zai yarda sai na kaiki.
   Ok to kana gani tun safe sunki fitowa abincin ma Shi yazo ya daukar musu na kasa gane meke damun Mufee, Aayan kuma sai nishadi yake kullum cikin farin ciki sai wani kiba da kyau ma yake karawa,Ameer baka fahimci komai ba? Ameer shi yasan dalilin komai Aayan warkewa yayi shi yasa yanzu angwanci yake yi su Meenat basu gane ba. Kallon Meenat Ameer yayi tare da cewa ki Bari kije ki tambayeta da kanki kiji tunda ke bakya gani ki kyale sai kinji dalili.

    Aayan ne da Misalin 5pm ya shirya tsab ya fito zaije wurin Daddy ni kuma na danji sauki haka na gyara toilet kal kal tare da Bedroom din yana kamshi ta ko ina,nayi wanka da ruwa me Zafi na shirya cikin kaya marasa nauyi,Meenat ce da Ma'eesha suka shigo da Sallama,Lokacin ina Jikin Mirror ina fesa turaruka,Maeesha tace kinyi kyau Mufeeda,Tnx ya kuke? Lfy sis bakya fitowa kamar baki da lfy muke ganinki Meenat ta furta,Wani kuka ne ya taho min sabo da Aayan kullum baya daga min kafa ko kadan na damu gaba daya yaki bari na dan warke ma,Meenat tace subhanallah me akayi miki kuma kuka? a jikin mirror na kifa kaina ina ta kuka da shesheka suna kallona duk sun shiga damuwa.

   Dan Allah ki fada mana mene ne?meke damun ki?me ya faru? Ina hawaye nace Ina so na fada muku amma Allah ya haramta ba kyau dole bazan fada ba wai sai dai nayi shuru, Meenat tace to wai tafiyarki ce duk ta canja mu bamu gane ba,nace Aayan ne yake ta abu daya ni wlh bazan iya ba gwara ayi asarar kudin gyaran jikin,ni da nasan hakane bazan yi gyaran ba,Sai yanzu Su Meenat suka gane me yake damuna,Dariya sukayi tare da cewa uhm wannan kuma tsakaninku ne wannan fadan ba ruwanmu babu me iya miki maganin abun sai dai muce aci gaba da hakuri kafin ki saba muji kinfi ma Aayan din maita suna ta dariya,nace
    Dan uwarku Ku fitar min a daki tunda dariya kuka zo yi min,Ficewa sukayi suna kuskus.

    Hajja ce take rera wakarta tana gaguda kwalli a idonta tana Yareye iyee nanaye...Ayyeee riyalle duniya.....Haneefa dake kusa da ita tayi lamo a gefe sai yanzu take tunanin aure,da can me yasa bata samu cikin samarin ta masu kudi ta fitar da miji an mata aure ba ta zauna tace ita karatu sai tayi Masters, yanzu ko mijin ma ta fito dashi wa zai mata kayan daki? Mikewa tayi ta bar wajen Hajja ta koma dakinsu inda ta tarar da Su Meenal tare dasu Sajeeda sunyi jugum suna tunani,Kallonsu tayi tace ya akayi ne yan mata? Meenal tace hmm ke dai bari Wai yanzu Abbi yazo duk mu cire layin wayar mu mu basu harda masu computer kowa ya kawo tasa wai za a siyar a siya mana kana na Irin su Dagani Gara, harda wata waya Dagani Gara kuma? Ae mana tana nan wata me uban nauyi yar China ko Camera babu,Yanzu dan danna wayar ma da muke tana ebe mana kewa karbesu za ayi kwarai kuwa dan har an kwace ta yan mazan gidan nan tare da Sauran yara kaf za a siyo kayan abinci me yawa wanda zai dan Dade ana ci,Abbi kullum suna fita neman aiki duk tsufansu amma ba a dacewa.

    Khaleel ne ya fito daga wanka ko Vaseline babu a dakinsu dakin su Haneefa ya shigo da gajeren wandonsa kai Ku miko min Vaseline na labta a jikina,Sajeeda tace kamarka da shafa Vaseline,to ya zanyi kawai a bani na labta haka,kune ance Ku samu aiki kunki ai da mun huta,Khaleel yace baki da hankali in mutum yayi aikin ma ai sai abinda Hajja tace wlh akan nayi wannan tsohuwar ta Dameni gwara na bar gidan nan na koma gidan frnd dina. Haneefa suna dariya tace nayi mamaki da yanzu kowa baya ragawa Hajja to ko dama wai tsafin nata can gidan ta binne su ne? Ita ta sani ai gashi tun ba a je ko ina ba sun jawo mana muna gane kurenmu gaba daya me yafi zaman lfy dadi Ameer tun wuri ya shiryu gashi ya huta Allah sai ya zareshi a cikin mu suka koreshi Ashe gata suka yi masa aikin banza ni dama ni suka kora wlh da wannan wahalar,Khaleel sai masifa yakeyi yana shafa mansa a dakin ya gama sannan yace to Ku ban aron Cumb,Meenal tace Cumb daya tal a gidan nan na Umma da ta zo dashi a jakarta shi yake yawo a gidan nan kowa dashi yake taje kansa mata da maza bari na karbo ma, yanzu wannan Sumar dana tara ta common Cumb ba bu bare man gashi da sauran kayan gyaranta ai kamar mahaukaci ma zan dawo soon zanje wajen me aski dole na sauketa, Sajeeda tana dariya tace haba gayu tana ma kyau, gyara ne yasa yanzu da babu zaki gani very soon dole ina ji ina gani na sauke ta, gaskiya Aayan baida mutunci Allah wadaran sa daya kore mu akan shegiyar Mufeedan nan,

Khaleel yace ah lallai baku fara nadama ba me tayi muku yanda haka kawai muke biyewa su Abbi da Hajja muka sasu a gaba musamman Ku,Aayan ko wacce shara shi ake turawa,tun bai San kasar nan ba Hajja ke tura masa asiri tun muna yara har muka girma,ki tuna takura da akayi masa shi da Ubansa,kalli matayen da aka sa ya aura kuma aka sa ya sakesu,kalli irin yanda ake nuna masa shi da Ubansa ko makiyinka ai baka yiwa haka ba bare dan Uwa na jini,Allah wadaran halin Hajja me zuciya kamar ta fir'auna danka da jikanka ka jefa su a wani Hali duk sabo da son kudi.

    To mu ba irinku bane Sajeeda shekaran jiya dukkanmu Maza muka zauna muka tace tare da tankada mukayi rairayi munyi lissafi ya bulle dai dai dan haka mu Maza duk mun tuba wlh Allah ya ganar damu gaskiya kuma Aayan bashi da laifi yama yi kokari yayi biyayya,yana da damar da zai tattara su koma kasarsu amma ya zauna damu yana Shan bakin ciki,to mu dai yanzu ma Istingifari mukeyi ko mu nan ance miki Hajja haka zata barmu ba tare da ta asirce kowa ba, tunda tayiwa danta da ta haifa wa zata kyale kuma Uwa fa guda, yanzu kalli inda su Mommy suke mata rashin kunya kin San kuwa asirinta ne yake ta karyewa zai tonu,gamu dan muma mun gano gaskiya,da ai bamu gane ba musamman Ku mata masu karamar kwakwalwa,mu dai sai Aayan da Mufeeda,Allah ya bar mana Anty Mufee sai Mufee.

    Sajeeda tace kato da kai kana kiran wata yarinya karama da Anty anji kunya,ai ke bakin cikin naki harda Hassada cewar Khaleel kinga tafi ki kyau,ta auri Aayan sannan Ameer ma maybe Kanwarta zai aura,Me yasa yanzu samarin naki yan iska basa zuwa? Duk sun gujeki wlh tun wuri ki gane gaskiya,Haneefa tana ji da sauran mata duk sunyi shuru Khaleel ya gogesu tas ya kara gaba abinsa.

    Gaba daya sun hallara a Palo ana cin shinkafa dafa duka tasha manja tana tiri tiri sun saba da cin girkin yan gayu duk sai suka ji wannan ba dadi kowa turawa yake da hakuri,Abbi mamakinsa daya shine dare daya suka koma talakawa me yasa basu yi planning sun mallaki kadarori ba,a ransa ya tuna da fa talakawa ne su sai rufin asiri kuma aka samu Daddy ya basu aiki suka koma gidansa da zama,da sun San haka ne gwara a ginawa kowa gidansa daban da yanzu ba ruwansu,duk kudin kuma da suke samu a wajen bokaye suke karewa aikinsu kenan,kawai kudi suke kwasa a Companies suna abinda suke so basa tunanin su tattala sabo da gaba sai burin kawai su kwace Dukiyar Aayan data Daddy,Hajja kuwa ko a jikinta bata da niyyar tuba sai ma kwantar da hankalinta da tayi tasan dole Daddy zai nemeta ta dawo dasu dole su dora daga inda suka tsaya.
    Meenal ce a palon tace duniya budurwar wawa,Abbi ya harareta tayi shuru,Abbi sani kuwa kallon Khaleel yayi tare da cewa dan ubanka baza ku aske Sumar nan ba ko sai kace kan mahaukata,Khaleel yace haba Abbi yawa kuke ba kudi ba komai me kuke so yan mata su gani a kanmu mu birgesu dashi yar wayar duk kun kwace kuma ya kuke so muyi shike nan mu baza muyi nishadi ba kenan, Mujaheed yace ni wlh aka sake barin gidan nan zanyi me ake min sai fada safe da rana da dare.
   Hajja ta Galla musu Harara ba wanda ya kulata wanda ta tabbata da ace da ne da tuni sun bata hakuri,Hawaye Hajja ta fara tare da cewa an rainani bani da iko da kowa,shuru ba wanda yace mata kala,ta mike tsaye tare da cewa ai bani na dora muku talaucin ba da zaku tsaneni me nayi muku? Wlh in na gaji bar muku gidan zanyi,sai nayi magana ayi Banza dani wata tsiyar nayi muku da za a dauki karan tsana a dora min,to duk Wanda ya fasa baya kaunar uwarsa da ubansa,Abbi yace me akayi miki kuma wai? Gasu nan bani da iko nayi magana sai cin mutunci to wlh zan bar muku gidan nan, Hajja ta fashe da kuka, yaran gaba daya tsaki suka ja tare da mikewa daya bayan daya suka bar palon su Abbi ne ke bata hakuri.

    Zaune nake a palon Sama na Aayan,naci uban kwalliya cikin English Gown iya cinya nayi kyau,Yau na samu Salama Da kyar Aayan ya fita zuwa wajen Yarima yana nemansa yace bazai je ba da kyar na lallabashi sabo da ya Dameni da fitina ko kasa bana sauka sai dai su Meenat ke yin komai kullum sai ya sani kuka yace zan saba ni dai yau 1wk kenan ban saba ba.
  Abin mamaki 40mnt sai gashi naji sallamarsa har ya dawo, duk da damuna da Aayan yakeyi bana ganin laifinsa kuma bana jin ya isheni ko naji haushinsa Sam bana jin hakan sabo da sonsa da yayi min yawa bana jin akwai abinda zai nema na hanashi a duniya,Da ya fita ma duk sai naji ba dadi gidan amma jin sallamarsa wani Sanyi da dadi ya ratsani har na kasa boye farin cikina,. Tsayawa yayi yana kare min kallo yanda yaga na wani yi mugun kyau kamar a sace ni,murmushin da nasan yana kara min kyau na sakar masa tare da walwali da Idona cike da jan hankali ina daga zaune na bude masa Hannu ya kuwa karaso a hankali tare da shigewa jikina a hankali na mayar da hannuna tare da rungumeshi gwiwoyinsa suna kasa,Hannayena nasa tare da tallafo fuskarsa muka hada Ido nace sannu da zuwa kana na shiga tsotsar bakinsa kamar na samu Alawa me dadin gaske.
    Hannu na daya na sa a cikinsa nace muji ko kana jin yunwa dariya yayi sabo da yanda nayi kamar irin dana din nan, ina Sonki My Queen ya furta yana dariya sabo da yanda nake masa cakulkuli a cikinsa, mikewa yayi tare da kwanciya saman doguwar kujera ya daura kansa a saman lumtsumemiyar cinyata wacce ke sheki da santsi ga tsoka da girma sai kamshi takeyi ta ko ina,Yar rigar dama guntuwa ce,Hannu yasa ya wara cinyata wai bude min Kingdom din taki na gani ya warke jiya fa sau daya kika bani tal, shagwaba na fara

 nace Allah a'a amma ai ya dace ka dinga danne maitarka kullum ba fashi ka bari na warke sai na baka amma kullum kace Dan Dis,gobe kace dan Mitsili,gata kace kadan,nasan yau kuma cewa zakayi....kafin na karasa yace Dan Kucili, dariya mukeyi gaba daya yace tunda nake koyan hausa in baki labari wannan words din ne suke bani Wahala da dariya,abin dariya,wai Dan Kucili,dan mitsili,dan dis,dan kadan,dan Kis,Dariya mukeyi nace ai har dan Kucilili ana cewa,yana dariya yace to na yau Dan Kucili zanyi,nace naki sai na warke 1wk sai next wk,Ido ya zaro waje tare da cewa kawai mutuwa kike so nayi ni bazan iya ba,Ina wasa da gashinsa nace gidanmu na gado wai ya za ayi dashi ne? Aayan yace ki Bari kawai a gyarashi a sake sabon Gini sai a sa yan haya mu jira muji nan gaba ko Abbanku yana da rai ko ya rasu dole bincike za ayi first,nace to Allah ya kaimu,Ameen yace sai me kuma?nace uhm...uhm.. da dai zan fada kar kace ina da son kudi ne,fadi mana idan ma kina so waye baya son kudi kuma ai kudin mijinki kije so ko? Kai na daga ae,Lefe ni fa ba ayi min ba,dariya yayi tare da cewa duk kayanki? Ai wannan kawai siya mana kayi kuma ma ai har su Meenat lefe kuwa iya Amarya akewa, Ki kwantar da hankalinki idan ma har biki kike so sai ayi miki,nace a'a ni bana son biki ko wata Dinner kawai lefe nake so sannan ayi min Kamu, mene kamu kuma? Kamu da akewa Amarya idan ana gobe za a daura mata aure a sata a lalle,to ai gwara Dinner dashi,nace a'a ni duk wannan basa birgeni kawai Kamu za ayi min nima shine yake birgeni a duniya bazai yuwu ace ni har abada baza ayi min ba,kullum burina naga anyi min Kamu a biki sai kuma haka ta faru to duk da haka ban makara ba shi yasa nake jin tsoro kar na samu ciki ba ayi min Kamu ba,idan na haihu ai magana ta kare kuma na haifi dan dakan Kuka,Dariya Aayan yake tayi tare da cewa lallai har yau Kuruciya na nan,Dan dakan kuka kuma shege fa kenan,Dariya nayi nace ae ayi min Kamu ni dai ko idan na haihu nace dan dakan Kuka na haifo.

   Jibi Birthday na sai a hada da kamuna,Waye zaiyi Kamun to? Zakiyi Birthday party ne? Nace a'a ba wanda zan gayyata Meenat da Ma'eesha sun isa su sani a lalle,ga Ameer da kai kuma Ango kun isa shike nan,Aayan yau dariyar Mufee kamar ta kasheshi da shirmena,yace to sai na gayyato Yarima ma yazo ayi dashi ko,nace to Allah ya kaimu,Aayan ya kalleni yace Amarya an kusa saki a lalle,nace haka yake next wk zamu koma schl ma,Nan Aayan ya hade rai yana jin haushin schl shike nan bazai dinga gani na ba sai yamma,yace a bari sai nan da 2wks ki koma kinga kin kara 1wk kenan ko? Nace ae Allah ya kaimu,Bazan iya yini ban ganki kusa dani ba, schl ta wani dawo ya furta tare da sauke ajiyar zuciya .

    Na kalleshi nima nayi shuru sabo da bana so mu rabu ko na 1mnt,hannunsa naji ya tura cikin rigata yana Murza kirjina, sakon dai dai yake shigata babu gargada ban san sanda na shiga Maida masa da martani ba,daukana yayi cak yana rada min dan Kucili za a bani,banyi musu ba sabo da bana son na bata masa kuma kar ma yace na fiye Complain ba dama miji yace zaiyi wani abu sai mace ta fara Complain sai ki ga yana jin tsoron neman hakkinsa yana danne sha'awarsa sabo da yawan Complain,ko miji ya dinga zargin kansa Shi ba namiji bane ko bai iya komai ba baya sa matarsa taji dadi dashi sai kiga duk ya shiga damuwa da tunani baya birge matarsa shi.
 
    Meenat ce zaune Saman sofa tana Shan ice cream dinta tana kallon American film a Tv,Ameer ya shigo ya zauna gefenta shima sanye da riga me gajeren hannu da 3qtr sai kamshi yake yi,yace San min na Sha Ice cream din,Dazu ya Aayan ya kawo mana da yawa yana fridge,bana iya Sha da daya ni kawai in zaki bani a naki ki bani,Meenat ta turo baki haka ta ebo a spoon tace duk zaka rage min quantity ni ungo ni karbi ya bude baki kuwa Meenat ta zuba masa ya shanye tana Sha tana bashi sai da suka shanye robar guda sannan Meenat tace kaji dadi hankalinka ya kwanta mun shanye da kai,karo wani mu shanye again ,au dama kana iya Sha da yawa dan kar nasha nayi kiba kazo ka raba ni dashi, Ma'eesha ce ta cakare ta fito kamar zata je Dinner,Meenat kawai sai ta hade rai tam, Ma'eesha tace Sis zanje wurin Yarima yana palon baki,Meenat sai lokacin ta saki ranta tace to maza ayi sauri a dawo lfy ki gaisheshi..me Meenat ke nufi da fushinta da farko? oho.

    Kallon film dinsu suke yi sai katsam budurwa da saurayi suka fara kissing din juna a haukace,Americans ba kunya sai gashi ana tube kaya za a fara Sex,Meenat duk kunya ta rufe ta da sauri ta dauki remote zata canja Chanel,Ameer yace mene haka sai da kallo ya dauko dadi ai nan shine ainihin film din Horror movie ne ki tsaya ki gani abinda zai faru mana,Meenat tace ni ba yar Iska bace tana Satar kallon Tv kuma,tace haka kawai mu dan Allah ka kawo remote a canja ka wani kwace basai mutum zai kalla ba, Meenat taji ana shidewa a Tv Ameer ya ba da Amanna yana kallo ta dan kallo ta dauke kai tace yan iska kawai sai taga Masoya sun koma abin tsoro dama Horror film ne sai suka koma fada da zako zako hakora,mace ta bude bakinta wommm...Sai da Meenat ta buga kara tare da fadawa jikin Ameer, Ameer yana Jinta dan munafuncin Sa sai yace ai film din nan abin tsoronsa yayi yawa yanzu zaki ga ma sun koma kamar Dujal ance har mafarkinsu akeyi, na gani a BBC wani Horror rannan ana kallo a wani gida ya fito daga TV ya shiga jikin matar kin San Aljanune, Meenat ta kara kankameshi ta boye fuskarta a jikinsa taki dagowa,Ameer yana jin dadi a ransa a fili yaci gaba da cewa ai ba a barin irinku su kalli wannan sabo da idan suka ganku sukan iya Faso TV suzo wajenku,ni tsoro nake jiye miki dan yanzu zan fita sai ke daya bari na Canja Chanel,ya canja Chanel ya fara kamar zai Mike Meenat ta rikeshi kam ta makale a jikinsa tana roko Karya tafi,yace to sai dai ki dakko Ice cream ki dinga bani a baki sai na zauna idan ba haka ba tafiya zanyi.
   Da sauri Meenat ta dakko tace bari na baka idan Ma'eesha ta dawo sai ka tafi kawai,nan ta zauna damfamfam tana bawa Ameer Ice cream a baki yana sha yana latsa wayarsa ya Zama dan gata,a ransa yace wlh aure zance Aayan ya min kwana nan na huta nima.






AsmaBaffa
[2/2, 12:41 AM] Asmabaffa: 🌖🌖🌖🌖
🌖🌖🌖🌖

    KASUWANCI NA







         107-108









Official







By
AsmaBaffa








HOUSE OF HAUSA NOVEL,TASKAR SURAYYARHMS,TASKAR FIDDAUSI SODANGI,UWARGIDA,ASMABAFFA FANS CLUB gaba dayanku gps na gode da Sharhi da kuke yawan yi kunfi kowa shi yasa wannan page naku ne.

    Tnx etc da ake yawan fada basu damu Writers ba anfi son Sharhi Readers Ku daure kuci gaba munfi jin dadin typing da posting.Gp dina naga ana sanya da Sharhi ko an fara gajiya ne da Novel din a tafi Hutu?😍😍😍 Love u all fans.













     Ameer yana tunani ya zaiyi ma shima yayi auren nan ya huta,kwanciya yayi saman 3seater tare da Jan eriyar tunaninsa ya shiga nazari,Meenat na gefensa ta gama bashi Ice cream tana waya da kawarta ta schl,yawancin yan makaranta musamman yan Boarding schl idan suka hadu da kawayensu zage zage zaka ji yana tashi kawai ana shegiyar ya gari etc,yanzu Meenat ita da tayi Day schl ma wannan tsabiyar ta zauna mata Ameer na gefe ta daga waya kawarta tana dagawa Ameer yaji kawar ta duro ashar, Meenat tana dariya tace amma dai Allah ya tsine miki,Shegiya ai baki da mutunci,Kawar tace dan ubanki ke Hafsat Salisu ciki ne da ita daga biki, Meenat tace ke Dan Allah? ke Amai take yi,Meenat tace ai Hafsat Salisu matsiyaciya ce,ai Allah yayi yar iska a nan wajen,Kawar Meenat tace hmm ke dan uwarki Aisha Balarabe wai aure zatayi shegiya, Meenat tace ai tsinanniya ce Aisha ta kirki zamu je gidansu ai soon, duk wayar tasu a zage zage ta kare har suka gama wai nan hira aka Sha kuma sai gulmar frnds,Abinda yan mata keyi kenan ai bin diddigin kawaye ana munafunci wance taci gaba ko baya taci,taci gaba da karatu ko a'a,anyi mata aure dadi take Sha ko wahala,ya ta koma ya gidansu yake aikin kenan sa ido,haka ma'aikata ma burinsu suga a ina abokiyar aikinsu take kwana ya gidansu ko gidan mijinta ayi ta gulmarta,duk iyayinta Ashe kaza kaza, frnds cikin su idan ba wata a kusa sai ayi ta gulmarta kema kina tashi ayi taki gulmar aikin kenan ya kamata ayi gyara mutum yaji da kansa ma matsalarsa ta ishe shi,amma sai abinda ba ruwanka zaka damu kanka.

    Ameer ya kalli Meenat yace yanzu wannan wayar taku mene sunanta mene amfaninta? Gulma ko zage zage? Shuru Meenat tayi,abinda kika koyo kenan a schl din taki zagi da gulma,ki daina ba kyau kawai kuyi ta zagin juna sannan da hirar wasu kuna zagi wannan bai kamata ba babu tarbiyya a ciki,Last warning na miki wannan idan na kara Jin wannan zage zagen am serious sai na Zaneki a gidan nan,Meenat baki bude take kallonsa da mamaki yanda ya zage yake ta mata masifa ba ji ba gani,kuma ba alamar wasa a idonsa ita dai tayi shuru.

   Lokacin munzo sakkowa ni da Aayan muka ji wayar da Meenat ke yi har ta gama,haka muna tsaye Ameer ya fara mata fada,naji dadi kuma ya birgeni,yau na tabbatar Ameer yana da hankali sosai kuma yasan me yake,kuma na kara yarda da zancen Aayan cewar Ameer ya tuba ya canja halayensa sabo da ace da ne ba ruwansa.
   Karasa sakkowa mukayi nace Weldon Ameer na gode haka ake so idan Zama ya hada ka tare da mutum yayi ba daidai ba ka gaya masa gaskiya na gode,Ke kuma Meenat haka Ammah ta bamu tarbiyya?Ni ban sanki da haka ba wlh,Meenat zatayi magana nace dalla rufe min baki Banza ko kunya bakya ji,Aayan yace to fadan ai ya isa haka taji ta daina ko Kanwata? Meenat tace ae.

     Zama Aayan yayi tare da cewa Meenat ku shirya gobe akwai Kamun Amarya a gidan nan,Meenat tace wace Haneefa ce ko Sajeeda ko a cikin su Meenal ne? Aayan yace My wife Mufeeda,tace Kamu take so ayi mata kamar ko wacce Amarya, Meenat tace tabara ce kawai da samun waje kaine ma kake biye mata,ni kuwa nace ae anji din ina ruwanki,Meenat tace wlh ba wani Kamu da za ayi miki ya wuceki sai kallo,Ameer yace ina ruwanki? Ma'eesha ta shigo itama dariya tayi tare da cewa bata lokaci ki Bari a hada da sunan Baby idan kin haihu a kama ki,Haka duka suka ki yarda dole Mufee sai hakura nayi nace Birthday din ma na fasa shiryawa a gidan,Aayan yace to gobe Ku shirya akwai surprise a gidan nan kuma gift ne na wife dina, amma kar wacce tace zata ji tsoro,muka ce to Allah ya kaimu.

    Washe gari mun gama shiri muna jiran Surprise na Aayan,Ameer ma yace baza a barshi a baya ba,5pm dai dai sai ga Aayan ya shigo tare da securities dauke da akwatuna ana shigowa dasu sunfi guda Ashirin,baki muka bude muna kallo aka gama jere su kaf suka fita, sallamar Yarima Bobo muka ji tare da Mace dattijuwa a bayansa amma ta rufe fuskarta da Mayafi sai dai da ganinta Hutu da jin dadi ya ratsata, gashi kafafunta da hannayenta da muke gani fara ce amma ba kar ba sai sheki takeyi,wani lace ne a jikinta na alfarma da gani yar gayu ce,sai kamshi takeyi, Doctor din dake Kula da Ammah kafin ta rasu muka gani, Uwata zauna ga kujera cewar Aayan,mamaki ya rufeni wai uwarsa,to wai wace ne haka,dattijuwar ce muka ji tana kuka amma kamar mun San muryarta,a hankali ta bude mayafinta tare da Cewa Mufeeda ta,zo nan Mufee ta,Meenat Ma'eesha nice fa Ammanku,Ammah ce,nan take muka kalleta sosai ba Shakka Ammah ce ta Sha Hutu,to ita bata rasu ba,nan tsoro ya kama mu na tashi da gudu ina fatalwa...fatalwa....Meenat ma suka Mike tare da rufa min baya muka fada Bedroom tare da boyewa,daga su Yarima har Ammah dariya sukeyi,Haka ma Ameer duk da bai Santa ba,Qur'ani na dauka,Meenat ta dauki carbi,Maeesha ta fara Rabbana atina muna ta yi kamar makarantar allo,tafiya muka ji za a bude kofar muka kara Volume din muryarmu ina Yaseen....Meenat na Lahaula Wala quwwata illabillah,
   Aayan ne ya shigo aiko muka manne kanmu waje daya,yace baku da hankali wai Ammah taku ce bafa mutuwa tayi ba,idan fatalwa ce taya zaku ganmu da ita,dama ba mutuwa tayi ba turai muka kaita akayi mata magani,shine abinda nake ta cewa zan baki wanda yafi miki ko mene a rayuwa,ita ce gift din tawa,surprise dina kenan,Mufee tace kuji haka kawai munga gawarta kiri kiri kuce waye waye, wlh Allah bata mutu ba Ammah ce kuzo muje Yarima zai muku bayani.
   Da kyar Aayan ya lallaba mu muka fito,amma sai buya mukeyi a bayansa na manne fuskata a jikinsa Meenat kuma taja rigata ta rikeni,Maeesha kuwa da tafin hannu ta rufe idonta.

     Har Palo muka zauna can nesa inda ba ruwanmu da Ammah,Ammah mamaki takeyi Ashe duk son da kakewa mutum ya mutu kana ihun Kuka da ace zai dawo kowa gudunka zaiyi bazai Zauna da kai ba,Allah me iko,Muryar Yarima muka ji yace a bude taro da Addua Ameer,Ameer  Ashe Malam ne yanda ya dinga zazzaga addua ba a magana.
    Yarima yace Mufeeda kece Babba ya dace Ku bamu hankalinku,Alhmdllh kamar yanda kuka gani Ammah ce taku ba mutuwa tayi ba kuna mamaki sabo da kunga gawarta a kwance,to wannan ba shirin kowa bane face nawa,idan baza ki manta ba lokacin da akayi aurenki da Aayan ya tafi bai kara waiwayonki ba,ko gaisuwa bai miki ba,kuma zaki tuna da kika ce masa Ammah ta rasu ko damuwa baiyi ba,sannan nace nan gaba idan kika ji rawar dana taka a aurenki da Aayan har kyauta sai kin min,nace ae anyi haka duka.
   Zakituna me Daddyn Aayan ya fada miki cewar labarinki da Aayan ya bashi shine yasa yace dole sai ya aureki ko? Nace ae haka ne.

    To lokacin da Aayan ya sameni da Zancen ni na kara cewa kin dace kuwa ya aureki yace shi bai yarda da tarbiyarki ba kuma da alama kina da son kudi,baki sani ba sai da muka dinga bibiyar rayuwarki sabo da ba auren mutum haka kawai shi yasa ake so har kullum ace mutum ya Zama na gari sabo da irin wannan kuma alhmdllh bamu samu wani mummunan Hali naki ba sai wanda ba a rasa ba wanda kowanne dan Adam yana da aibu ko yaya ne bazai yuwu ace 100% kake ba,nace ae, idan munzo miki da zancen ba lallai ki yarda ba a wancen lokacin,kuma lokacin kin kawo bukatar taimako na aikin Ammah idan muka ce gashi gashi zaki ce ba dan Allah muka zo ba,kuma lokacin Aayan baya son wani aure umarni kawai yabi,shine nace mu bari sai mun kai Mahaifiyarku asibiti tunda ba ranga ranga take ba sai mu fada mata muji,bayan an kaita likitan yace Ku fita za a duba ta lokacin muna Office din a can ciki,a nan muka sameta da maganar,Tayi farin ciki kuma tayi Naam,amma tace mana ko da ta rasu ga Amanar yaranta nan Aayan ya rikesu,kuma mun karba,sai tace kina da wani Hali daya wanda bata Sonki dashi Aayan yayi kokari ya canja ki,nan tace mana ke akwai son kudi bata so abin yayi nisa ya kaiki ga halaka duk da cewa tasan talauci da nauyin dake kanki yasa wannan halin ya shige ki.

    Tace amma baza ki canja ba sai in kinsan bata raye sannan Zama ki yarda ayi auren,nan ta shirya mana dabara,Ammah ce tayi magana tace kwarai Mufeeda nice na shirya musu komai sabo da ki fara koyon Darasi a duniya ki san cewa Kudi ba shine komai ba,duk abinda Allah ya tsara shi zai faru,sai karfin addua kan sawa Allah ya canja,ina Sonki fiye da komai a duniya shi yasa Nace suce miki an farkeni baza a dinke ni ba sai kin yarda anyi aure nasan wannan zai sa ki yarda ayi miki auren sabo da Yarima ya bani Labarin Aayan kaf a asibitin,kuma naji tausayinsa,na yarda yaron kirki ne zai iya rike min ke da Amana,kuma naji kina jin tsoronsa shine ya dakeki kika min karya kika ce kwalabati kika fada,shine ya daukeki ya hukunta ki kika ce min kina gidan kawarki neman taimako sabo da kar hankalina ya tashi,to Mufee kin yarda kuma kinyi abinda nake zatonki wato dangina da dangin Mahaifinki sun daura miki aure,sun sani kuma makwafta sun sani,Alhmdllh an baki sadaki kin taho da burin Ammah dinki dole ta tashi sabo da tuna ninki kudi da aikin asibiti shi zai sa na rayu ba Allah ba,ya kika ji da kika ga basuyi tasiri ba na rasu a lokacin kinga hukuncin Allah,Meenat baki manta ba nace muku naji a jikina ta hadu da Alkhairi kuma na bar muku wasiyya Ku bata ko? Meenat tace ae kuma mun fada mata ashe dama kin San komai duk abinda kika fada kuma ya faru,Murmushi Ammah tayi tace to lokacin da kuke kuka kuna suma lokacin aka canja gawata wacce a asibitin idan baku manta ba Doctor ne ya daukeni tare da canja min daki lokacin aka daukeni aka kawo wata baiwar Allah wacce tayi hatsari da dadewa an rasa danginta tana motuary aka yi mata wanka tare da hada ta za a sa Alummar musulmai su sallaceta akaita makwanci ,Dangina dana Babanku duk sun San ban mutu ba,kawai kallonku sukeyi,a boye Yarima ya sanar musu amma basu San dalili ba,shi yasa kuka ga basu wani damu ba suna ta harkarsu ko? Nace kwarai kuwa ko a jikinsu a lokacin.

   Shi yasa aka hanaku Ku bude gawar lokacin da za a kaita kuna ihu da kuka lokacin ni kuwa tuni anyi min Visa ina Kukan rabuwa daku cike da tsoro kar na mutu da gaske,Aayan da Yarima ne suka kaini U.s acan aka yi min aiki da komai na warke,naso nazo na ganku Amma Aayan yace min baki shiryu ba kina nan da son kudinki na jira tukkunna.

    Aayan ne ya karbe zancen da cewa shine dalilin da yasa kika ga na Dade ban zo wajenku ba kina Amarya,ina U.s sai da Ammah ta samu sauki muka dawo ni da Yarima lokacin baki ga dana zo ba bana baki ko kwandala ba ban kuma siya miki komai ba,lokacin kuma tunanin ki zaki samu kudin Kasuwanci,ni kuma na nuna na fiki wayo,na hanaki sisi,sannan dana kaiki gidana na baku abinci garau garau Ammah ce tace nayi miki haka zaki kara hankali,tun kina tunanin zan saki kudi kuji dadi sai kika ji shuru,abinda kika ce na baki shi nake baki bana kari,sai da naga kin fara gane gaskiya,sannan na fara sakar miki sai naga ma kawai ma baki San wani kudi ba,sabo da Dubu biyu a wajenki kudi ce,nayi ta miki gwaje gwaje da dama baki gane ba,yanzu Ma Ammah ce tace ta gaji tasan yarta ta fara hankali ta girma ta hakura gwara ta dawo ta ganku,kuma da baki hankali kin canja ba da baza ki ganta yanzu ba,Yarima ne karfin shirya komai kuma shi ke yawan zuwa ganin Ammah a Us,shi yasa rannan muka je tare har kika yi fushi dani dole na dawo ba shiri, gata nan Ammah taga ina sonta da yawa sai garani takeyi na Zama mijin tace,Dariya Ammah tayi tare da cewa Allah kyauta Aayan,Yarima na dariya,Ameer kuwa sai yanzu ya fahimci komai,yace Ammah sannu da zuwa ni Cousin din Aayan ne ga Meenat nan ta rainani gaba daya kullum sai ta zageni a gidan nan,Dariya akayi gaba daya amma banda ni wacce nake hawayen bakin ciki,sam ni abinda Ammah tayi naji haushi gaskiya kuma bata kyauta ba,akan wannan ta iya sawa aka shirya ta rasu jibi irin kukan da mukayi da halin da muka shiga na rashinta, yanzu baza ta iya yi min fada na Canja ba kawai sai tayi mana haka yau gashi har Meenat tayi Candy anfi 1yr, kuma tasan Aayan a lokacin ba sona yake ba dan tana tunanin na gari ne kawai sai ta yarda nayi wannan auren da wuri gashi ni har ma nafi sonsa,kuma har Aayan ya rufeni shi da Yarima, gaskiya Ammah bata kyauta mana ba ni banga amfanin hakan ba amma wata zuciyar a raina tana sanar min fa ai na shiryu kuma nayi hankali sau nawa Ammah na min fada na daina abinda nake amma naki ji,to kuma idan ma naso kudin ai duk akansu ne tunda su nakewa komai,dan su nayi,sai kuma aga laifi na ai kowa da halinsa, ya Ammah za tayi da mutanen unguwa fa wanda suka Santa lallai za a dinga fyalla gudu kuwa.

    Meenat kuwa da Ma'eesha duk sun tafi sun makale a jikin Ammah suna ta murna da hira tana shafa Kansu,Ameer ma yace shima Allah sai ta sa masa albarka,haka ta shafa kansa daya tura mata,amma kuma Ammah hankalinta baya jikinta ya tashi matuka,hankalinta na kaina wacce tafi so a duniya ganin ina kuka naki kulata,kamata yayi ace ni ta fara shafawa ba wasu ba,Aayan ma hankalinsa ya koma kaina yar gwal dinsa na kuka kyautarsa bata birgeni ba kenan,Ammah ce       tace Zo Mufee ta kinji? Ta Mike zata zo wajena da sauri na Mike tsaye tare bin hanyar wani Bedroom wanda nake so na dauka cewar nawa ne ni kadai a sama kusa dana Aayan da muke kwana,nan na shiga kawai nayi kwanciyata a saman Bed,da sauri Aayan ya biyo bayana amma na sawa kofar Key,ko waye gaskiya zai iya jin ba dadi idan akayi masa haka Mufee tana da gaskiya cewar Aayan a ransa.
 
   Magiya da lallashi ba wanda bai min ba naki ki magana,Haka Ammah tazo da kanta tayi tayi naki,su Meenat ma,Yarima da Ameer duk sunyi sun hakura,Aayan yace suje kawai zan huce ne.

    Suna Palo suna ta hira har Ammah ina jiyo hayaniyarsu,Suka ci suka Sha,Ammah kuwa Aayan cewa yayi ta hau sama ta zabi daki ko a bata part guda tace a'a a dakin su Meenat zasu dinga kwana suna hira da yaranta kafin ta koma gidan can tsohuwar unguwarmu.
    Yarima yace Ammah Aayan ya miki magani kin warke ni kuma ai na siya miki gida hadadde ciki zaki koma,Ammah harda kuka su Meenat sai godiya suke masa,Ameer yace to ni kuma Mota zan sai mata insha'allah,Mamaki Ammah takeyi har ni kaina da nake labe ina jin hirarsu Allah haka yake ikonsa ka gama Shan wahalar duniya ba sai ya yanka ba wasu ma sai kaji dadinsu,suji kanka lallai ba a san wanda zaiji kanka ba a duniya ba sai lallai danka daka haifa ba.

    Ammah duk wannan baya gabanta hankalinta yana kaina dana ki kulata,Haka har suka tafi tare dasu Meenat tayi wanka tare da shirin baccinta suma haka sai suka ci gaba da hirarsu suna ta bata labarina da abubuwan da suka faru bayan bata nan,da halayen yan gidan su Aayan etc da kyar Ammah ta iya bacci sabo da tuna nin naki saurarta na kasa yi mata Uzuri,kuma Danni tayi hakan dan rayuwata ta inganta amma na kasa Fahimtar me take nufi,Kuka nake tayi a daki ni an tozartani a gaban kowa ance ina da son kudi har Uwata tayi karyar mutuwa sabo dani, kuka nake sosai Aayan yana jikin kofar yayi yayi na fito mu kwanta naki yarda,shi kuma bazai iya bacci  babu ni ba ya riga da ya saba,kukan nan nawa yana kona masa rai,tun yana rokona na fito mu kwanta har ya hakura yaje ya kwanta amma kasa bacci yayi gaba daya ya shiga damuwa sai tsaki da juye juye yakeyi ya rasa ya zaiyi ya iya bacci ba tare da ina jikinsa a kwance ba,Bai kara Sanin lallai Ashe yana sona kamar ransa ba sai yau,ko baiyi komai ba ace yana ganina a kusa dashi.

   Cikin dare wurin 1am ya kara zuwa ya rokeni na bude masa ko bazan je wajensa ba naci gaba da bacci na ina jinsa,har ya gaji ya tafi,2am ya dawo wai dan Allah to na bude ya bani abinci naci tun rana banci komai ba, nan ma naki kulashi Sai ma baccina da nakeyi.
   Haka ya kusan kwana a hanyar dakina da dakinsa sai da yayi sallar Asuba sannan bacci ya daukeshi cike da bacin rai.
   Washe gari Har Ammah suka shiga kitchen suka shirya abinci ana ta Harka ba Aayan ba ni,shi yana baccin gajiya,ni kuma naki fitowa nayi wanka na da komai yunwa na kwakulata amma naki fitowa ko kadan,Sai haka suka hakura sukayi breakfast har Ameer, misalin 12pm Aayan ya Sha wanka direct dakin da nake ya nufo cike da hasala yace bude kofar nan ko na bude da kaina yanzu kafin na irga 3 tsoro da tausayinsa naji tun jiya yake abu daya na tabbata ko kansa bazai wa haka ba,ina fushi kamar zan fashe na turo baki na bude kofar, shigowa yayi da sauri ya rungumeni a jikinsa yana why? Babyna me yasa haka? Zaki kasa Fahimtar mu,idan laifi ne hakan kiyi hakuri baza a sake yi miki ba amma dan Allah ki Kula Ammah ko zata ji sanyi baki ga yanda ta damu ba sai zancenki take min kullum bata da burin da ya wuce Mufeedanta ranar nan ma fa da kika Dameni ko da budurwa nake waya nace miki watace yar Us Ammah ce fa kuma lafiyarki ta tambaya a lokacin,dan Allah kiyi hakuri ko abinci kici kalli duk har kin rame,ina jikinsa yana ta lallashina ina sheshekar kuka harda na shagwaba,yace ni Allah bazan je wajenta ba tunda tayi min haka ta tafi ta barmu Ashe tana raye kuma ka boye min bazan je wajenta ba,Ok to naji ya isa haka kukan Zauna bari na kawo miki abinci kici kinji mufeen Ammah? Nace Allah ni ba tata bace ka daina fada min,a raina mamaki nakeyi wai Aayan ke nuna min so haka,ashe yana sona haka ai har tsalle nayi da birgima a saman Bed sabo da murna Aayan na so na da yawa.
  Ammah ya fara gaisarwa cike da girmamawa,su Meenat suka gaishe shi yana tsokanarsu sun samu Ammah sun manta da kowa,Ammah tace ina mutuniyar? Yace  hmm da kyar ta yarda zata ci abinci sai yanzu ta bude kofar da kyar sai da na Sha fama tun jiya nake abu daya,Farin ciki Ammah tayi lallai Aayan yana son yarta sosai kuma yana kula da ita taga zahiri a jikin mu kuma su Meenat sun bata lbr,Abinci Meenat ta hada masa a tire ta abawa Aayan,Ammah tace nasan Halin abata akwai zuciya ka bita a hankali zata sameni ne,Aayan yace to ya nufo dakina, sai da yasha fama kafin ma naci abincin sai da kansa ya shiga bani a baki shima yana ci,da kyar nake karba,sai yace dan Allah ki hadiye pls sannan zan hadiye,idan ya takura min na fashe da kuka,bayan mun koshi nace to sai ya fitar min a daki,yace kai Sweetheart ki Bari ko hira muyi mana naji dadi kinga jiya ko bacci ban iya ba bakya kusa,nace ni ba ruwana ka tafi ko na barma dakin kawai,Haka ya hakura badan yaso ba ya fita,naji tausayinsa sai nace dawo to ka kwanta amma 2hrs kawai zaka tafi,ba musu ya dawo na nuna masa bed tare da cewa kwanta to zan tayaka baccin,Dadi ya lullubeshi nima haka sabo da nayi missing dinsa so nake naji duminsa,key na sawa kofar sannan na kwanta a gefensa ina kunkuni,jikinsa ya jawo ni yana aikin lallashina yana so ya danyi Romancing dina amma yasan bazan yarda ba fushi nake dasu gwara ya lallabani haka kan kace me bacci ya kwashe mu muna makale da juna dama baccin bai ishe mu ba,Ammah duk ta matsu ta bar gidan sabo da kunya take ji Zama gidan yarta jira take Yarima yazo a canja mata gida.
   Ameer har sun saba da Ammah kamar ummansa haka yake ji da ita.

   Kwanan Ammah uku a gidan nan ban kulata ba ko ganina bata kara yi ba tun zuwan farko,Aayan ma bana sakar masa fuska bana bari ma ya rabeni tun rannan da nace zan tayashi bacci ban kara bari ko yatsa ya rike min ba,ya shiga damuwa har ramewa yake yi,Ammah kuwa har da na sani takeyi da bata shirya hakan ba ta barni da halina,Yarima yace suyi hakuri zan sakko ne,Ammah tace tunda ta huta a kaita gidanta tare dasu Meenat gaba daya,Aayan yace ai shi bai yarda ba baza a dauke masa su Meenat ba,Ameer ma yace gaskiya basu yarda ba,Ammah da kyar ta lallabasu tare da ganar dasu har suka hakura,Aayan yace Mufee fa ai dole a tambayeta,Ammah tace kyaleta ba komai itama zata zo da kanta ne ta neme mu,Yarima suna zaune su Meenat murna kawai sukeyi da zumudi ko ta kaina basa bi suka tattara nasu ya nasu kaf suka shirge a mota,sannan Aayan ya rakasu wajena wai zasu bi Ammah su wani bakin ciki ya kara dirar min,mun saba da rayuwa tare da yan uwana kullum muna tare ina ganinsu ina jin dadi muna abubuwanmu sabo da tare dasu Meenat nazo gidan miji ban san zafin rabuwa da yan Uwa ba sai yanzu gashi mun kara shakuwa,tare muke kashewa mu rufe,su bani shawara na basu,su suke tayani ayyuka da komai ba ruwana da wasu masu aiki sai masu wanki da gyara Compound,nan take na kallesu kawai na fashe da kuka,suma suka rushe da kukan suna bani hakuri,nace Meenat kuma yanzu shike nan kun tafi ni kadai zaku bari?ai sai ku bari sai nan da kwanaki sai ku bi bayan Ammah amma ba komai kuje rayuwa ce, ita Ammah ai ta saba da zama ba mu,ta saba da rayuwa ita kadai shine yanzu daga zuwanta zaku manta dani Ku bi bayanta ko? Meenat tace gani mukayi idan mun barta baza taji dadi ita daya ba,ae Amma ni kuma fa kunyi tuna nin haka? Ita da tayi tafiyar muke tunanin bata raye fa mun hakura ma da ita shine zaku bita tun yanzu? Shike nan mun fasa Binta bari sanda kika yarda shike nan,Da sauri su Meenat suka fita suka sanarwa da Ammah,dariya tayi tace da gaskiyarta lallai Mufeeda na yarda ta Zama Babba ta kara hankali kuje Ku dawo da kayanku ni zan tafi Ku bata hakuri daga baya sai kuzo ku yini kwa dinga yi min.
  Haka suka dawo da komai nasu inda yake,Ameer yafi kowa murna,Aayan ma yaji dadi da basu tafi ba sabo da yasan an bar baya da Kura shi zai sha wahala dani kafin na huce.
   Ma'eesha ta dawo tace Ammah sun tafi da Yarima sis gamu mun dawo,Good for u nace kawai sannan na juya nayi kwanciyata.

     Bayan sati daya da dawowar Ammah Yarima ne ke dawainiya da ita tare da Ameer su suka kaita danginta can kawai tare da Maiduguri duk sunyi murna tayi musu bajinta ta dawo katon gidan da Yarima ya siya mata na alfarma,ga yan aiki mata dattijai masu kwari har biyu,da me gadi namiji daya, gidan ba abinda babu na kayan alatu da ci da Sha.
   Haka ta zauna a dan gidanta,Yarima ya kai Ma'eesha da Meenat sau biyu sun mata yini guda,ni kuwa ba ruwana fushi nake da kowa bana kula kowa sai Ameer,Haka Aayan ma kullum da sha'awarsa yake kwana yana tashi,bana kulashi babu yanda baiyi dani ba amma naki lallashi ba adadi,har Ameer yasa ya bani hakuri naki ji ,Yarima yace ba ruwansa sai dariya yakewa Aayan yanda duk ya fita daga hayyacinsa ya rame kullum tunani  da damuwa yakeyi,har kasa jurewa yayi ya Sanarwa Daddy wai idan nazo gaisheshi ya bani hakuri ya lallaba ni,Daddy yace ba ruwansa ya kula da matarsa kowa haka yake hakuri.
   Ni kaina tausayin Aayan nake ji sosai ganin halin damuwar da yake ciki,kuma shi yake kula da ganin naci na koshi,amma ba ruwana da shi kuma ba wai dan bana sonsa ba sai ma tausayinsa da nakeji.
  Sati gudan da mukayi bana kula Aayan kullum gyaran jikina nakeyi tare da Shan tsumi na masu Inganci,ina gyara jikina wanda Maman Sayyah kawata ta koya min hadawa da kaina,maza irin su Aayan sai da gyara sosai kwai kwarzaba,nayi mamakin da naga yana iya daurewa amma nasan a wahala yake kawai na rashina,Meenat ma duk sun fahimci yanda yanzu bana kula Aayan yana cikin damuwa, zuwa wajena suka yi tare da min nasiha sosai ba laifi kuma ta shageni sun tunatar  dani ina cikin fushin Allah da Mala'iku, bayan sun tafi na tafi Dakin Aayan amma baya nan,gyara dakin nayi sosai tare da toilet,haka gaba daya part din mu sai dana gyarashi Neat sannan na sauka kasa,Ameer dasu Meenat sai murna sukeyi da alama na daina fushin,da kaina na shirya girki na me shegen dadi,Pounded yam da egusi soup sai farfesun Kaji nayi tare da shirya lemuka kala biyu na gama komai na kwashi na Aayan a flasks na Alfarma na kai tare da shiryawa a bedroom dinsa, lemuka ne kawai na barsu a fridge sai ya dawo zan kai masa.

     Ina yin Sallar Isha na shirya cikin kayan bacci na ala tsine ba abinda ba a gani a jikina sunmin kyau,ko ina kamshi nake fitarwa abina nasa Hijab kato da niyyar sauka kasa naci abinci tare dasu Meenat,ina fitowa Aayan kuma ya hauro saman muka ci karo,yana ta kallona ganin haka yasa na juya zan koma Bedroom da sauri,hijab dina ya jawo na dawo baya,ido muka hada ina shirin fara kuka yace me nayi miki wai kike min haka? Shuru nayi yace fine jeki Allah ya gani kuma yana kallonki yayi gaba abinsa ya barni a tsaye,fasa sauka nayi nabi bayansa zuwa Bedroom dinsa yana kallona yayi banza dani ya fada toilet tare da yin wanka ya fito ina kallo ya gama shirinsa ina zaune Saman Bed,na fita na kawo masa lemuka tare da Fruits salat na ajiye,ya kalla tare da cewa kwashe abincin bana ci ni alhalin yunwa yake ji, shuru nayi ban kwashe ba,tsawa ya buga min ba dake nake ba,sai da na tsorata matuka,zuwa yayi tare da hayewa Bed dinsa yace kwashe ki bar min room bana son ganinki pls,Karfa ko ya daina so na haka nake tunani,kuka na fara masa ba tare da nace masa komai ba, idan na tashi sai na ballaki a room din nan bana ra'ayinki fice min da gani, Kukana naci gaba da yi nace an cuceni ace bazan yi fushi ba,kuka boye min Ammah ta bata raye kuma shine aka zo ake ce min ina da son kudi a gaban kowa duk an rainani,bayan ni ba haka nake ba maimakon a lallasheshi shine za a balla ni,barin gidan ma zanyi gaba daya tunda haka ne.
   Wanne hakuri ne ba a baki ba? Ya kike so ayi miki? Yarinya ce ke? ai dai na hakura har girki nayi ma kace wani baka ci kai,kuma ka tsaneni baka kaunata baka son ganina ai shike nan bari na tafi.
   
   Shuru yayi a ransa yana me jin dadi wani Sanyi tare da Hamdala ga Allah,muryarsa naji yace zo ki zauna akwai maganar da zamuyi kuma in dai baki karba ba kawai na daina kulaki ba ruwana dake,a raina nima sai murna nake,cike da shagwaba na zauna a gefensa nace gani to ai ko ina turo masa dan lips dina me kyau da birgewa,kallona ya tsaya yi na gama birgeshi.






   Wannan page na yan gps ne gaba daya sabo da wannan babban page ne babu wanda yayi zaton Ammah na raye abin mamaki,sai nan gaba za a kara Jin yanda akayi corner dasu Mufeeda ha Ammah ta barsu a zuwan ta mutu dole ba wannan ne kadai dalilin ba akwai wani.


  Tnx fans! ayi hakuri da typing errors.










AsmaBaffa
[2/3, 8:36 PM] Asmabaffa: 🌖🌖🌖🌖
🌖🌖🌖🌖

    KASUWANCI NA








          109-110









Official







By
AsmaBaffa









      MAMAN 2 KIDS and MOM INTEESAR wannan page nakU ne sabo da jajircewarki a Sharhi.

  HUMAIRA sarkin Sharhi ina gaisuwa me tarin yawa.


  AUTA ina kika boye tare da ASYCOOL shuru Allah yasa lfy.

Manya manya maganin kanana Jinjina nake muku
FLOWER
MARCYCOOL
ZAINAB ATIKU SALAMA
SAMEERAN GAYA
HAFSAT KHAIRAN
MAMAN MEENAT
MOM SUHAIL
MRS HAMZA
MRS UMAR
MRA FAROUQ
JANNAT
MAMAN WALEEDA
QUEEN MERMU.






 
           Ido ya lumshe tare da budesu tar a kaina,kallonsa nakeyi cike da so tare da kewa shima hakan,wani kallon so muke aikawa da juna dadi na ratsa mu, magana ya fara yi min cikin nutsuwa,Mufeeda ya furta cikin muryar tausayi da lallashi,Kallonsa nayi sunan da ya furta har kwakwalwata haka naji kamar wata na'ura ce ta ambaci sunan haka nake jin dadinsa.
   Magana yaci gaba da cewa tunanina kinyi hankali Ashe ba haka bane,an miki bayani sai ki fassara abu bai bai,kin kasa Fahimtar me ake nufi,yanzu abinda kikayi kin kyautawa Ammah kenan,mahaifiyarki guda,ta miki komai a rayuwa ance ta rasu kin damu kina kewarta ance bata rasu ba ta dawo akwai dalilin da yasa ta shirya hakan,ba wacce take so sama dake,bata da magana sai Mufeedanta,tazo har gidan mijinki da kike aure amma kika ki Kula ta ko kallo bata isheki ba,mutumin da yayiwa Mahaifiyarsa haka waye bazai masa ba,iyaye fa basa laifi wurin yaransu,Meenat su fiki hankali,mahaifiya guda kika ki kulawa,kika wulakanta,tana can da bacin ranki Allah ma na fushi dake,sannan ni ban miki komai ba ina mijinki kalli abinda kika dinga yi min kan abu kalilan kin bani kunya,yanzu gobe zamu je ki bawa Ammah hakuri ki shirya idan kin yarda idan baki yarda ba to,Da sauri nace ni bazan je ba na daina kulata tunda tayi min haka, cike da bacin rai yace to tashi kije nima ba ruwana dake.

    Kin tashi nayi tare da yin shuru sai da aka kwashe 15mnt sannan ina kunkuni nace to shike nan ai zanje amma Allah bazan gaishe ta ba tunda tace ina da son Kudi,Hararar wasa ya jefo min yasan na hakura ma tunda na yarda zanje,abincin fa baza Kaci ba? Kince baza ki gaisar da Ammah ba ta ya zan ci abincinki,baki na turo ai dai nace idan Naje kawai zance Sannu da zuwa Ammah amma Allah bazan gaisheta ba,to ruwa kawai zan sha nima,kai dan Allah Nafa sha wahala wurin girkin nan na bata lokaci nayi maka da kaina,baka ji dadinsa ba pls Kaci ko kadan ne? Bazan ci girkin wacce bata gaida Mum dinta ba,da ace kina gaisheta sai naci,shuru nayi sai da naga lallai bazai ci ba nace to zance mata Sannu Ammah ni dai bazan ce ina yini ko ina kwana ba Allah sai in kar Kaci abincin kuma ai nayi kokari ma.
  Shi kanshi yasan ma na huce gaba daya sai yace to zanci badan halinki ba,ina murna na cire Hijab dina na ajiye gefe,ya kalleni sama da kasa yaga kayan Harka iya kaya,Nayi kyau ga kayan baccin matsiyata dasu komai ana gani, ina sane nake kara girgiza jikina ko ina rawa yakeyi na zuba masa komai kawai na dauki Hijab dina zan mayar jikina yace noooo pls ki barshi haka zo ki tsaya a gabana,haka ya tsayar dani kamar wata soja yana cin abinci yana kallona na kasa tsayawa waje daya sabo da na tafi da Imaninsa ina sani nake girgiza jikina wai irin na gaji da tsaiwa sai kukan shagwaba nake masa ina dire diren kafafu shi kuwa karfin Hali kawai yake yi tuni hankalinsa baya jikinsa idonsa ya canja da kyar ma yake kokarin cin abincin hankalinsa yana kaina.

    Bai ma gama ci ba naga yace kwashe na koshi,na kwashe komai na mayar kitchen sannan na koma dakina na kwanta a bed tare da yin dai dai wai irin Jan aji nasan dole zai biyo ni,Brush da shiri ya sake ya fito yaga bana Bedroom din,Wayata ya kira yaga ban daga ba,ya kara kira shuru ina kallo kuma,Da kansa ya Mike ya nufi inda yasan zai ganni,hango ni yayi na baje ina baccin karya amma tunaninsa baccin gaske ne,wani juyi nayi me Jan hankali,light ya kashe tare da haurowa Saman Bed din,yanda naga yana abu a rude shi ya bani dariya har na kasa rikewa na saki abata,cakulkuli ya fara min muna dariya yace dama kina kallona ko? Nace Oya let's go,ai Bazan iya matsawa nan da can ba kawai mu kwanta a nan, yau ban bari ya fara min komai ba,ni na fara Sabo da nayi Missing din mijina da yawa,kamar zan cinye masa lips tare da tongue haka nake tsotsesu da zafi zafi, dadi ya gama rufe shi kawai wani nishi mukeyi,Bana iya cewa komai sai dai nace Miss u Baby,Shima haka can kasa naji yace yau Dan Ficici za a bani,Lokacin ina jin dadina ya min yawa bana hayyacina nace a'a yau kamfatowa zakayi,yace Allah? Nace ai Kwaso kawai, yace an gama,ba karya kuwa ya kamfanta dan yau nafi ko yaushe jin jiki a hannunsa,ba karamar wahala nasha ba,tun ina kuka dadi sai da na koma na wahala,sabo da ban wani saba ba,kadan na saba Bazan iya dauke yanda yake so ba ba tare da na dan sha wahala ba yanzu sai nan gaba,har yau sabon nawa ba wani me yawa bane sai kuri idan anzo kuma na fara kuka ido ya raina fata,shi kanshi Aayan ya san iya limit din da nake kaiwa ban gajiba,shine yake so dole na saba sai yazo wanda lokacin na gaji sai ya dinga Dragging dina,Kuma ko yaushe yana ganin ci gaba tunda kullum ina kara samun ci gaba.

    Sai da ya samu nutsuwa muka yi wanka na gasa kaina sosai mun kwanta again yana Sa min Albarka yana jin dadi yace lallai yan matana yanzu ana ta girma kullum, tnx alot My Queen,jikinsa na shige nace ni ba wani sabawa karka kala min ina yar yarinyata.dariya yayi tare da kara kankameni yana shafa min gashina zuwa gadon baya na yace muyi bacci sai gobe kuma zanga wanne salon za a nuna min naji na yau ya hadu kin ba da style,dukan wasa na masa ina jin kunya na kara boye fuskata a kirjinsa ina dariya kasa kasa,wata Kalma na rada masa a kunne wacce saura kadan ayi second round da kyar na lallasheshi yace to ki daina kunna ni,nace kyis na kasheka to,Dariya mukayi gaba daya hannayensa suna saman Mazaunai na yana shafasu cikin Salo iri iri wanda ni kaina hakan yana min dadi.

     Abbi ne kwance saman gadonsa  yana nazarin duniya tare da mamakin canjawar komai da ya samesu a rayuwa,gashi har sun lalace suna ramewa sunyi duhu sosai kamar basu ba,dama ance duk wanda ya saba da rike kudi yana shan wahala idan karayar arziki ta sameshi,kuma dama can taimakon su akayi talakawane gaba da baya, duk gashi har sun zama abin tausayi duniya ta juya musu baya,wai sune a wannan matsayi, Hajja ce ta shigo dakin Abbi tana fada mene amfanin kwanciyarka a gida da tsakar rana haka baza ku fita neman na kanku ba,kudin hannuna sun kare saura Naira dari kamata yayi ko yar dubu biyu ina rikewa a hannuna ni bana iya rayuwa ba kudi,Abbi shuru yayi bai ce mata komai ba Sabo da bakin ciki da me zasu ji, Hajja tace au dan Iskanci kana jina ina magana kamar kaga Kashi eyee,ni na daura muku talaucin idan kudin banza ne me yasa baku yi zuciya kunyi ba, Haba Hajja me nace miki kuma,ya kike so muyi kina gani karatun su Sabeer ma nema yake ya tsaya,ba komai bamu da komai sai bashi ma da muke ci ki dinga tausayinmu mana,idan ba sata kike so muyi ba me zamuyi miki? Hajja Hawaye ta share wai an ci mata mutunci,ta fice fuuuu ta bar Abbi yana bakin ciki.
    Haneefa ce ta fito ta cikin yan uwanta Maza da mata tace to Jama'a ku kalli atamfar jikina ta gaji da wanki har ta kode tana neman jemewa,dama kayan namu kadan muka ebo,Meenal ce ta fado da gudu tace Bazan ji kunya ba bayin Allah nasan masu hankali ne gaba daya dan Allah me Pad always ta san min ko a min karo karo na kudi na siyo,Sajeeda tace ai duk dan kwalayen Ka kayana sun kare a kunzugu rannan,sai dai kiyi amfani da dankwali, Mujaheed da Khaleel suna dariya suka ce kadan kuka gani Yara tun yaushe muke cewa kuyi aure tun da gatanku samari na rubibinku kuka ki gashi na pad ma ya gagareku.

Meenal ta kalli Khaleel tace dan Allah bani gajeren wandon nan naka da naji zaka jefar naga cotton ne sosai zai sha ruwa a jikinsa,Khaleel yace ko kunya bakwa ji wai a gabanmu kuke irin wannan kalamai ba tarbiya ba komai sai kije yana cikin bakar jakar nan ki dauka,Meenal da Sauri taje ta dauki gajeren wandon Khaleel wani me nauyi cotton tasa reza tare da yankashi kashi Kashi ta linka kamar dai Pad haka ta dinga sawa tana kunzugu dashi.
  
   Matayen su Abbi talauci ne ya ishesu gaba daya suka ga gwara su tafi gida tunda yanzu ko sabulun wanka da wanki Rasawa akeyi a gidan,Nan suka tayar da rigima sai an sakesu,Umman Ameer tace ita dama tana jin Haushi an rabata da Danta Ameer ta gaji,Hajja tace ba shegiyar da za a saki kamar yanda akaci daula dasu dole Asha wahala dasu dama in sun koma dangin nasu ma dai talaucin zasu tarar Sabo da duk kanwar ja ce.

   Yaji sukayi wai sun tafi gida sai sun huta zasu dawo,Yaran gida suka ce sama dawo idan sunji Wahala kar wanda ya hanasu,suna shiryawa suka ce mu munyi gaba,Su Mujaheed suka ce a dawo lfy Allah ya kiyaye Hanya,tuna ninsu yaran zasu damu sai suka ga kowa harkar gabansa yake,Sabeer yace mu ai Aayan da Daddy kadai ne zasu ce zasu yi yaji zuwa turai mu damu Amma kawai ba abinda ake tsinana mana ace za a damemu,common toothpaste mu muke siya,sabulun wanka da wanki ba a san a bamu ba,Abbi yace Kai rufe mana baki marasa kunya,Sajeeda tace ai wlh sai daí a godewa Allah Amma ya dace ace a cikinmu akwai Karuwai,akwai yan shaye shaye tare da kasurguman barayi sabo da Halin da muke ciki a gidan nan,kowa kansa ya sani kowa ta kansa yakeyi,Hajja tace ai duniya ce yanzu ma kofa a bude take zaku iya komawa Karuwanci da shaye shaye,sace sace kuwa na wanda kuka gani shi zaku dauka dan ni nawa yafi karfinku😅, Abbi Sani yace Haba Hajja addua ai zaki yi musu ba kice suje suyi ba ai yarane yanzu idan  mune zaki so yaranki su dawo haka?.
     Kai Sani ka rufe min baki shegen kunne kamar malafar Kwadi,Dariya aka dauka gaba daya har yaran Sabo da kunnen Abbi Sani kamar Malafa haka suke kuwa,Abbi Mustapha ne ya buga musu tsawa,shima Abbi babba yace zaku bar palon nan yan Bantan uban Yara.

     Khaleel ne yake ta masifa a tsakar gida an sace masa sabulun wanki wanda da kyar ya hada kudin ya siyo na wanki dan Naira Hamsim wani kato zai dinga cancanawa yana wanka dashi,daga ajiyewa ya juya baya zai dauko bokiti kafin ya dawo har an dauke sabulun yan mintuna kadan,Nan ya fara fakon wanda ya dauka duk wanda ya shiga wanka ko me wanki sai ya duba sabulunsa mata da Maza,Meenal tana fitowa daga wanka ya ganshi a hannunta ashe ita ta sace ta wanke panties dinta tunda period take dole sai da wanka da wanki,Kamar zai cinyeta haka ya kwace abinsa,dan ya bar mata tace kazanta ta na wanke dashi fa period ne duk na shafa masa na wanke da kyar ake gane kalar sabulun dazu wlh dan baka gani ba yanda ya rine kamar jar color aka Sa,abin kyankyami har wari yakeyi, Khaleel ya gano so take ya bar mata shi du, yace ai ko a Abbatuwa mayankan dabbobi aka jefa shi cikin kogin jini bani abina dan Uwarki mayya wlh idan na kara ajiye abina kika dauka sai kin gane kurenki,Meenal tace jaraba akan sabulun wankin?Yace ae din,to yi hakuri dan Allah ka bani na karasa wanke daya pant din nawa yanzu na tuna ban gama ba kaima kasan sanda muna daula bakwa sanin ma time din da muke period yanzun ma babu ce tasa ba yanda zamuyi dole muke yage yar kunyar.
    Khaleel yace ungo badan halinki ba dan dai kawai kina san min Vaseline dinki ne Allah gashi nan saura ki karar dashi,Na gode cewar Meenal ta koma toilet ta gama ta fito ta bashi sabulunsa,Mujaheed ma da shi yayi wanka haka mata da mazan kaf ba yanda Khaleel ya iya haka kowa ke zuwa yana rokarsa dashi sukayi wanka,Abbi ma yace kai Khaleel bani sabulun sodar nan naka zan cude jikina dashi ina so na fita neman Ameer ruwa a jallo dan ubansa ya zai manta da iyayensa,Khaleel yace kune fa kuka koreshi ai ni ya birgeni wlh,gashi sabulun dan Allah nasan wankanka dadewa kakeyi karka silleshi Abbi.

Harara Abbi ya zuba masa ya wuce yayi wanka sannan ya kwalawa Meenal kira tana zuwa yace Bani Toothpaste naji ance kece me shi a gidan nan,Meenal tace Vaseline gareni  ni Katon gaske wlh ko wanka zaka yi dashi ina dashi kamar tulu yake Sabo da girma saurayina nasa ya kawo min shi maganin gidan yawa,Meenal Me Vaseline kenan,Abbi yace dauko min shi na shafa,wace to me abin goge baki?Haneefa ce me su manya manya ita take matsowa kowa da kanta duk yanda kuke da ita sai daí ta Matsa ma da kanta kar ya kare da wuri,Abbi yace kirawota ta bani,Tunanin Abbi ai shi Babbane Haneefa zata bashi ya matsa da kansa yanda yake so sai kuwa yaga tace kawo Brush din,da mamaki ya kalleta ta kuwa bude ta dan difara masa kadan tare da cewa kar ka raina Abbi rayuwar sai da tattali,Hajja ma tazo tace Haneefa ashe kece me makilin matso min a nan na goge bakina,Haneefa tace  rayuwa sai Imani Hajja ku tsofaffi har wani goge hakora kukeyi idan ba iyayi ba da ganin arahar Sa me zaki goge hakora kamar Tsinken tsire duk sun zube saura dai daiku kici goronki shima yana wanke muku baki tayi tafiyarta,Hajja tace ni me na tare musu da aka rainani,ta fara kiran Khaleel sai da yazo jikinsa ba riga, tace wai kai kullum baza ka Sa riga ba kai kenan daga dogon wando sai gajere,Khaleel yace Am too sexy ne Hajja wlh shi yasa nake nuna muku baiwa ya fada yana dariya,Hajja tace ina wata baiwa a nan Da Ameer dina ne ya fada sai na yarda dalla bani sabulu na wanke jikina, Khaleel yace Rayuwa sai Imani Hajja wa zaki wa wanka ke ba miji ba,yo ko miji gareki me zai ci da ke ki sha zamanki haka da Allah wannan Asarar sabulu zaki mana,Hajja ta balbale shi da masifa ko wanne dan iska bani da iko nayi magana sai yace wani Rayuwa sai Imani wata sara kuka samo kuma ko kuwa ni kuka raina.

    Khaleel dai yayi tafiyarsa,Mujaheed ne yazo ya wuce Hajja shima ba Riga sai 3qtr ya tattaro hantsar Wando ya rike gaba daya yana tattalewa yana tafiyar yan gayun samari ga uwar suma duk ta cukurkude,Hajja tace haka dai aka iya yan iskan Yara ayi aure tun tuni kuka ki yi sai aikin rike hantsar Wando Sabo da jarabarbu ne ku mayun mata,Hajja bata san gayu bane ta dauka sha'awa ce ko Iskanci ne ke damunsu,Mujaheed yana Jinta yace Hajja sai Imani ai ko Ya kika ce,Tsaki ta ja tare da tauna
Goronta,Sabeer da Aliyu ne wanda sun kai 24yrs yanzu su kuma boxers ne dan karami suka Sa da yar Singlet ga abar tasu nan a Wando ana gani duk ta mike da wata yar kwarababbiyar waya karama a hannusu suna dannawa suna kallon pics din yan matan turawa kusan tsirara suke,Hajja nan ma ta rasa uwar da suke sai kus kus suke suna dariya suna kallon waya,ta kalli wandonsu a ranta tace na shigesu ni Hajja kar fa a fara cikin shege a gidan nan ayi yar gida tunda ga yan mata nan kuma ba muhararram juna bane wasu to matan ma ya suke bare Maza,Ganin Hajja na Sa musu Ido Sabeer yace Allah wadaran karamin gida sanda muna gidanmu babba wa yasan me wani yakeyi Amma yanzu komai kayi akan idon wani,Aliyu yace muyi maganinta suka samu Hajja tare da cewa Hajja kinga wasu dan Allah sun hadu? Nan Hajja ta kalli waya ai sai taga Mata kusan tsirara,Sabeer yace wannan zan aura Hajja tayi? Duka Hajja ta rufeshi dashi tare da cewa wlh in dai ina raye baka Isa ka auri wannan ba,Aliyu yace musulma ce sunanta Rasheeda,Hajja ta dauka da gaske ne ta dinga tsine tsine ba a Isa ba,kuma tace sai ta fadawa su Abbi,Sabeer yace Hajja masu kudi ne fa yar gidan shugaban kasar Ethiopia ce fa kinga mun washe,sabo da son kudi Hajja sai tace ya sunanta kace? Yace Rasheeda,Hajja tace ayyo yanzu naji zance ai tun daga sunan ma kasan musulma ce,a ina kuka hadu a Internet din naku?Sabeer yace ae tace kwanan zata zo ma kuma zata Aiko min da yar million goma na sha ruwa,kirji Hajja ta dafe tare da cewa kace ina gaisheta kakarka Hajja sunana,yaro kayi dabara wlh kafi su Khaleel hankali ina kallonku yara ashe kune manyan,Aliyu yace Hajja kinji tana kira ma a waya kash Amma bamu da kudin Sa kati kuma dole sai da kati so muke mu tura mata accnt Number tace Sauri take zata turo kudin gashi bamu da sisi,Hajja da Sauri tace zan baku rance ina jin kamar Ina da dubu biyu a hannuna nawa ne Katin da zai isa? Sabeer yace tab ai sai dubu biyar yanzu kuma babu sai daí ayi asarar milliyan goma kenan Hajja ki taimaka idan ta turo zamu baki milliyan Uku a ciki kyauta,Hajja dadi ya rufeta tsohuwa da son kudi nan tace to  dama dubu shida ce ta ragemin a duniya ga biyar sai na rike daya ni kuma,Nan Hajja ta zaro dubu shida a jikinta wanda da haka kawai ne sai daí a mutu a gidan baza ta iya siyan ko sabulu ba.

   Sabeer suka karbe dubu biyar da Sauri suka dauki dubu daya daya,dubu Uku kuma suka siyowa kowa na gidan sabulun wanka da wanki,suka bawa matan kudin kitso,mazan kuma na aski,har pad aka siyawa matan kowacce biyu biyu Sabeer yace gashi naga Alama boxers dinmu an fara sace mana ana kunzugu dasu, har da Sauran dan abinda ba a rasa ba duk sun dan siya me araha,karshe dai Sabeer dari biyu biyu ce ta rage musu,Duk yaran gidan sunji wayon dasu Sabeer suka hadawa Hajja sai dariya akeyi a boye kowa ya washe yau a gidan har kifi soyayye suka Dora a saman shinkafa da wake kowa daya,su Abbi da Hajja basu san me akeyi ba,dama matayen su Abbi sunyi yaji su Haneefa ke girki duk da basu wani iya ba wahala tasa har sun saba.
    Kwana biyu Hajja taga su Aliyu shuru ba 5k dinta ba milliyan Uku sai nemansu take Amma sunki yarda ma su hadu wasan buya sukeyi.Idan taje dakinsu sai su Khaleel su boyesu kowa yace basa nan sun fita,Hajja ta koma me gadin dole a Palo take kwana wai zata ga wucewar Aliyu ko Sabeer amma sai su wuce ma bata ganesu ba.

   Washe gari da Safe ma sai da Aayan ya kwashi Harka ba daga kafa kamar ma baya tausayina, kamar yanda su Meenat suka saba haka sukayi komai girki da gyaran gidan su ma yan aiki suna nasu,sai 11am muka fito bayan Aayan ya shirya ni yayi min komai,ba su Meenat gidan shuru sai guntuwar paper na gani sun ajiye min,.......wai mun tafi gidan Ammah tare da Ameer sai dare.
     Aayan yace ina suka je? Gidan Ammah na bashi amsa a takaice, da kansa yayi Feeding dina muna hira sama sama yana tsokanata wai jiya naji dadi na fara sabawa,na fara Kukan shagwaba ina Ni ba wani dadi,yana mun dariya har muka gama,yace je ki shirya muje gidan Ammah sauri ya furta ba alamar wasa,da Sauri na tashi na je sama nasha wata dakakkiyar shadda yar Senegal tasha aiki Dark purple aikin kuma da light blue and pink na fito kamar wata Hajiya,Shi kuma shadda Light blue kamar munyi ango sosai muka yi kyau.

    Jerawa mukayi wow yau abin kallo ne mu, nace muje wajen Daddy mu gaisa,Daddy ba karamin farin ciki yayi ba da ya ganmu haka sai albarka yake sa mana sannan yace mu gaishe da Ammah, yau ba Driver bane zai tuka mu kuma ba escourt mu biyu kawai,da kansa ya zagaya tare da bude min gaban motar yace ranki ya dade Allah ya taimakeki shiga,Kafadarsa na dan buga kadan ina dariya na shiga ya rufe sannan shima ya zaga ya shiga yaja motar cike da nutsuwa muka bar gidan,Ba wani nisa me yawa bane sai gamu a wani gida dan babba me kyau sosai yayi kyau gaskiya,me gadi ne ya bude mana gate ya Cinna hancin motar Sa cikin gidan,gidan yasha tiles da flowers yayi kyau sosai,jikin wata katuwar Bishiya muka hango su Meenat tare da Ammah zaune a katuwar tabarma suna hutawa,Ameer da Yarima suna gefe suma,Hajja da Katon tire a gabanta tana kwada musu zogale da Kuli yaji hadi sai nishadi sukeyi abinsu.

    Aayan ya kalleni yaga ina murmushi ni kadai ina ta kallon Ammah muryarsa naji yace muje ko? Da sauri na dawo hayyacina na daure fuska irin ba dadi naji ba,murmushi yayi yace kinfi kyau a haka muje dama naji jiya Ammah tace duk tafi so taga kina fushi dariya kike bata,da Sauri na washe bakina nace na fasa fushin tunda tana so,na fito ina ta fara'a ina murmushi wai Ammah ta gani kar taji dadi ma,Aayan yana ta dariya a ransa,a hanya yace Ammah tace tana so taga kina fushi kinki gaisheta,nace aiko sai na gaisheta din,Aayan yace ke duk abinda bata so shi zakiyi ko? To ki daure dan Allah ki nutsu tana son ta ganki a nutse cib dake,Nace haka tace?Yace ae,na girgiza kai nace za a gani wlh Bazan nutsu ba sai na koma kamar bera wasa zan tayi ba nutsuwa.Aayan yana ta dariya mugunta yake hada min.
    Muna karasawa mukayi sallama kowa Murna yake yi nazo na huce,a kunne ya rada min tace ita bata son a durkusa mata da Sauri na durkusa nace ina yini Ammah kuna lfy ya gida ya aiki?irin na bata haushi bata so a gaisheta,sai naga tana ta murna ta Amsa da fara'a harda Sa min Albarka,ni kuma sai yashe baki nake ina fara'a wai ance tana son nayi fushi shine bazanyi ba ni fara'a zanyi,har hannu nake sawa ina kara bude bakina sosai,Aayan yana ta dariya a boye,shima cike da ladabi ya gaishe da Ammah ta amsa da sakin fuska suna hira sama sama,tunowa nayi ance tana son ta ganni a nutse to Bazan nutsu ba,Sai mutsu mutsu nakeyi muna hira da Ameer tare dasu Ma'eesha duk nafi kowa surutu,dan karma ace na nutsu nace Ma'eesha jibi akwai schl kema kin sani ki tabbatar kin mana wanki da guga na furta da masifa kuma da sauri irin ba nutsuwa,Ammah hirarsu sukeyi tare da Aayan da Yarima,Na dauko wayata ina dannawa,na mike na dauko wata kujera fara naki Zama waje daya naki yin shuru kar wai ace ma ina da nutsuwa, ita kuwa Ammah dadi take ta ta ji tana kallona irin na saki jikina a gidanta sai harkata nake yi,Meenat ma da sauran haka suna ta kin dadi.
   Aayan ya zo gefena ya rada min Ammah fa bata so a shigar mata Palo da Bedroom shi yasa tunda taji na mata waya zamu zo sai ta zauna a nan wajen sabo da kar ki je mata dakinta.
   Da gaske kake?yace ina miki karya ne ki kiyaye abinda zai bata mata rai zamu fita da Yarima zan dawo anjima mu tafi, Yarima tashi muje,Yarima yace Madam yau an manta damu? Sai lokacin na tuna bamu gaisa ba da sauri na gaishe shi ina bashi hakuri suka fice daga gidan a motar Yarima.

   Na tuna Ammah bata so a shigar mata Palo da dakinta kawai na tafi na shige can ciki ina ganin haduwar gidan da furniture din gaba daya,Ina haka naji Muryar Ammah a bayana tace Mufeeda ta wai kamar ba ke ba? Tausayi ta bani kawai naje na rungumeta harda hawayen farin ciki,nace kiyi hakuri Ammah kece nan kika yi mana haka me yasa haka? Kin samu kuka da damuwa,kuyi hakuri haka Allah ya tsara da ace banyi hakan ba baza ki taba yarda da auren nan ba,yanzu gashi kina zamanki da mijinki,nasan halinki Mufeeda kamar yunwar cikina,ko kin yarda anyi auren baza ki zauna ba matukar kin San inda zaki ganni,kuma cewa zakiyi sai kin kula dani,zaki dinga dorawa mijinki nauyi yayi tunanin baki da tarbiya,kuma ai gaskiya ce har fa auren kasuwanci kikayi da ina raye yana hanaki kudin zaki barshi,haka kuma akan kudi nasanki ba mutunci,har auren Kasuwanci kika yarda kika yi,shi yasa yana fada min kin yarda da auren kasuwanci nasan kawai son kudin naki yayi yawa shi yasa kawai nace ace miki na rasu naga yanda kudin zasu amfaneki,nayi tunanin tun daga Ranar zakiyi nadama Ashe sai kika ci gaba da son kudin ki dole sai kin ci kudinsa,yanzu ba gashi Mufeeda na ta Zama Babba ba,ta girma,tayi hankali,da mijinta,tana zamanta lfy,tana karatu,ba ruwanta da harkar son kudi rayuwarki ta gyaru Alhmdllh.

   Tafiyar da nayi nace ace muku na rasu nan ma ba iya akan kanki bane akwai wani abu a kasa amma zan fada muku sai lokaci yayi zaku sani insha'allah,Yanzu Aayan ya sanar dani rashin lafiyar babansa akwai wani me maganin gargajiya can kauyenmu Insha'allah wani satin zamuje a kaishi ko za a dace,Allah ya kaimu nace Ammah wai Allah yanzu kece? Na furta ina shafa jikin Ammah,tana dariya tace nice ko kin tuna sanda kike kaini toilet ki dauko ni? Sannu Ammah kinji kinga yanda kika kara kyau da haske Ashe kema fara ce Ammah amma da kinyi duhu, bedroom muka kule da Ammah ta bani labari kaf tun daga yanda Aayan da Yarima sukayi ta dawainiya da ita a turai,Aayan ya kashe mata kudi,yanda ya dauketa kamar Uwarsa yake kula da ita kullum sai sunyi waya ba fashi,gashi komai akan lokaci,abinda Aayan yayiwa Ammah ko uwarsa ce abinda zai mata kenan,Ammah ta fada min irin jin dadin rayuwar da ta shiga a turai,tunda naji haka Aayan ya kara shiga raina,na kara bashi wani matsayi na daban,sonsa da kaunarsa ya kara mamayeni,nan take na fara kukan dadi nace Ammah Allah ya taimakeni ban taba wulakanta mijina ba,shi yasa ake son ko yaushe kayi me kyau,da yanzu kunyarsa zanji,Murmushi Ammah tayi na manya tace abinda naji irin son da kike masa har muna waya ina jiyo muryarki wai wace? Macece?kyakyawa ce? Dariya nayi tare da rufe Idona da tafukan hannuna,Mufeeda an girma,nima na zauna na bata labarin kaf bayan rabuwarmu wanda su Meenat basu bata ba na sanar mata,tace Allah ne yake tsare min Ku Allah yaga halin da muke ciki kuma yaga zuciyar kowa,sai mu kara dagewa da addua,yini mukayi muna ta hira da Ammah ba ji ba gani ina kwance a cinyarta muna labari,tana kara koya min yanda zan kula da mijina da gyaran jiki,Wasu magungunan tsumi data hada min ta bani katuwar leda guda da yanda zanyi amfani dasu,tace ga akwatunan lefanki can ki tambayi Meenat suna dakinsu guda goma sha biyar mijinki yayi miki a wajena ya hadasu can turai ni na hana a baki wancan lokacin sabo da baki hankali ba,yanzu kuma ya hada komai ya barsu wajena,akwati biyu kuma tsarabarki ce ni na siyo miki,Sauran kuma guda hudu nasu Meenat ne nayi musu baya min komai na nuna musu,Ammah to kayanki na gani cikin Sip na sawa ga wasu a akwatuna yaushe kika dinka? Aikin Mijinki ne gaba daya tare da Yarima.
   Ammah Yarima fa Ma'eesha yake so,ae na sani ai ya fada min rannan ma babarshi tazo wajena mun dade da ita mutanen kirki ne ai,yanzu Ammah Meenat ce kadai ta rage,dariya tayi tace tun yaushe Mijinki yace min yayi mata miji wai shi ya samo mata ban san dai waye ba,Nace ni gaskiya a'a wlh Ameer zan bawa ita sun dace kuma baki ga taimakon da yake mana ba,to Aayan ya rigaki zabin Aayan zata aura Insha'allah cewar Ammah,kamata yayi ma su dawo gida wajena Mufeeda kinga an takurawa mijinki bazai sake ba,kai Ammah ni ki bar min su dan Allah,Bakya gane me nake nufi Mufeeda sabo dake fa nake komai da bakya min musu duk abinda nace shi kike yi me yasa kike haka yanzu?kiyi hakuri su dawo zaki gane me nake nufi,to shike nan Yaushe kike so? Yanzu suje su kwaso kayansu idan nace gobe kuka zakiyi in zasuyi miki Sallama gwara kina nan gidan,Nan take kuwa suka tafi da Ameer suka kwaso nasu ya nasu tas har akwatunan da Ammah ta ciko musu da kaya,na gani kaya masu kyau da tsada duk gasu nan iri iri,nawa kuma an bar min su a gidana.

    Aayan ne ya basu Driver guda da mota dalleliya ta gaske za a dinga kai su Meenat schl da kuma unguwa har Ammah.
   Su Meenat ne sukayi Dinner Ameer yace dama shima a barshi a gidan Ammah da yafiye masa,nace ai kuwa baka isa ba sai dai ka dinga zuwa kullum,Bayan munyi sallar Isha Ammah tace bana son shaye shayen maganin matan nan barkatai,wanda na baki sun isa ni na hada da kaina da yayan itatuwa,zan koya miki wasu ki kiyaye kinji,nace to,Dauko ki fara shan wasu yanzu ko period kikeyi cike da kunya nace a'a,ta bani wasu nasha tace nayi matsi da wasu duk nayi ina zaune muka ci abinci da komai,ba na so ma na koma gida nafi so na kwana wurin Ammah muyi ta hira ina jin dadi,nace Ammah Abbanmu fa?, Nan take Ammah ta bata rai karki kara yi min zancensa,gidan nan kuma da kike gani na sa an siyar dashi na kai kudin wajen danginsa dama shike nan abinda ya mallaka tare da yan uwansa mukayi shawara,Ammah idan ya mutu fa ya Zama gado fa? Nan gaba zan muku baya ni karku damu,nace to ba damuwa.

    8:30pm sai ga Aayan ya shigo da Sallama idonsa na kaina, yace Ammah Yarima yace bazai samu Damar shigowa ba sai gobe zai zo,ba damuwa ai yana kokari ma kullum sai yazo,Aayan ya kalleni yaga ina jikin  Ammah a kwance nayi rashe rashe ina danna waya,tashi mu tafi gida,Baki na turo gaba ina shagwaba nace anan zan kwana ni sai nayi kwana uku zan dawo,Su Ma'eesha duk sakin baki sukayi suna kallon irin yanda nake kashe murya,Ammah tace tashi ke ku tafi bana son shashanci shi yasa nasan da ina kasar nan zaman auren ma gagararki zaiyi gashi daga dawo wata zaki fara,Ameer kuwa shima tuni ya tafi gida yace sai gobe.

   Aayan na kalla nace dan Allah fa nace sai gobe to ka dawo mu tafi,Har gida Ammah tazo yanda zaki ganta kika ki yarda sai yanzu zaki ce wani kaza kaza,tashi mu tafi kin ma san bazan iya kyaleki ba,Ammah tace ka daina bata bakinka tasar min a cinya ku tafi, gani Ammah tayi ina bata lokaci tace Meenat kuje Ku kwanta suka tashi suka wuce tare da ce min sis sai da safe zamu zo,Na Galla musu Harara nace dalla...dalla..dalla kuje can ku rufe min baki,ance muku bazan iya zama ni kadai ba ko aikin nawa bazan iya ba na gida,Dariya sukayi suka wuce suna yiwa Aayan sai da safe.
    Ammah ma tureni tayi daga jikinta ta shige dakinta sukayi Sallama da Aayan tace ka rufe mana kofar,Daukan kayan da Ammah ta bani yayi tare da mayafina ,jakata da takalmina har dankwalina,cikin mota ya kaisu ya dawo ya daukeni cancak tare da cewa zaki san kin min musu yau Allah ya kaimu gida,ina magana kina min musu ko,nace wayyo na tuba Allah ni na isa,wlh wasa nakeyi na tuba pls My Man bazan kara ba,yace ai kin jawowa kanki yau.
  Kin san dai Bana son ina magana ana min musu dan kinga Ammah na wajen ko? Da sauri nace a'a am so sorry bazan kara ba.


2 comments:

  1. Wannan shaidena ne game da kyakkyawan aikin Chief Eli Dodoru wanda ya taimake ni .... Ni ne Ann Earnis daga arewacin Carolina Amurka. tare da taimakon wannan sihiri, maigidana wanda ya bar ni tsawon shekaru 3 da suka gabata ya dawo, daga ƙarshe na sadu da wannan mutumin a shafin yanar gizon da aka buga shi ta hanyar abokin ciniki don taimako, na bayyana masa komai kuma ya gaya mini game da ya rubuta min leda da ya sani game da shi kuma ya ba ni whatsapp na rubuta wa mai rubutun sihiri don in sanar da shi matsalolin na. A cikin sati 2 kacal, sai maigidana ya dawo wurina. Ina so kawai in ce na gode wa wannan mai magana da gaskiya na gaskiya da gaske, sir duk abin da kuka fada min ya wuce kuma na gode sir. Don Allah ina so in fadawa duk wanda yake neman wata mafita ga matsalar su, don a tuntuɓi mai wannan sihiri, shi mai gaskiya ne, yana da iko kuma duk abin da maginan ya faɗi ya faɗi abin da zai faru, domin duk abin da mai sihiri ya faɗa mini ya zo. wucewa. Zaku iya yi masa nasiha ta alheri akan: whatsapp +2349015088017

    ReplyDelete
  2. Wannan shaidena ne game da kyakkyawan aikin Chief Eli Dodoru wanda ya taimake ni .... Ni ne Ann Earnis daga arewacin Carolina Amurka. tare da taimakon wannan sihiri, maigidana wanda ya bar ni tsawon shekaru 3 da suka gabata ya dawo, daga ƙarshe na sadu da wannan mutumin a shafin yanar gizon da aka buga shi ta hanyar abokin ciniki don taimako, na bayyana masa komai kuma ya gaya mini game da ya rubuta min leda da ya sani game da shi kuma ya ba ni whatsapp na rubuta wa mai rubutun sihiri don in sanar da shi matsalolin na. A cikin sati 2 kacal, sai maigidana ya dawo wurina. Ina so kawai in ce na gode wa wannan mai magana da gaskiya na gaskiya da gaske, sir duk abin da kuka fada min ya wuce kuma na gode sir. Don Allah ina so in fadawa duk wanda yake neman wata mafita ga matsalar su, don a tuntuɓi mai wannan sihiri, shi mai gaskiya ne, yana da iko kuma duk abin da maginan ya faɗi ya faɗi abin da zai faru, domin duk abin da mai sihiri ya faɗa mini ya zo. wucewa. Zaku iya yi masa nasiha ta alheri akan: whatsapp +2349015088017

    ReplyDelete